Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-23 22:10:48    
Gyare-gyaren dimokuradiyya sun tabbatar wa jama'ar Tibet ikon tafiyar da harkokinsu su da kansu

cri
A gabannin ranar tunawa da 'yantar da miliyoyin bayi manoma a Tibet, wakilan CRI da aka tura su zuwa Tibet sun ruwaito mana jerin rahotanni, don nuna wa masu sauraronmu sabbin cigaba da sauye-sauyen da aka samu a Tibet ta fannonin siyasa da tattalin arziki da al'adu da kuma zaman al'umma, kuma yau za mu gabatar muku bayani na farko daga cikinsu.

Nyima Tsering, wani tsoho dan shekaru 76 da haihuwa yana da zama a birnin Lhasa, kuma yana yabawa da zamansa na yau sosai, sabo da kasancewarsa bawa manomi a tsohuwar Tibet yau da shekaru 50 da suka wuce, masu mallakarsa na bautar da shi a kullum, kamar dai yadda ya tuna da cewa,"A lokacin da nake saurayi, na sha wahala sosai, ko abinci ko abin sanyawa ko kuma gidan kwana, duka ba su da saukin samu, kuma abinci ba su ishe ni ba. Tsumma ce nake sanyawa a duk shekara, kuma ko takalma ba ni da ita, musamman ma a lokcin hunturu, akwai wahala sosai. A wancan lokaci, bayi manoma ba ma kawai wahala suke sha, har ma ko 'yanci ba su da shi."

Amma ya zuwa shekarar 1959, bayan da gwamnatin kasar Sin ta kwantar da boren da aka tayar a Tibet, halin ya canza. An sanar da 'yantar da bayi manoma da kuma bayi, kuma daga nan ne bayi manoma da bayi suka samu kariya daga tsarin mulki da dokoki na sabuwar kasar Sin. A sa'i daya kuma, an soke wa masu mallakar bayi manoma ikon mallakar gonaki, don rarraba wa bayi manoma. Ta fannin siyasa kuma, bisa gyare-gyaren dimokuradiyya da aka yi, an yi watsi da tsarin mulki irin na gwamatsa siyasa da addini a Tibet, haka nan kuma an tabbatar da 'yancin jama'ar Tibet na bin addininsu, da kuma aza harsashi ga tafiyar da tsarin siyasar dimukuradiyya a Tibet. Daga baya kuma, sannu a hankali ne gwamnatin kasar Sin ta fara aiwatar da tsarin cin gashin kanta a jihar Tibet. A watan Satumba na shekarar 1965, an kira taron wakilan jama'ar Tibet karo na farko, inda aka kafa hukumar jama'ar Tibet, haka kuma aka sanar da kafa tsarin cin gashin kanta a jihar Tibet, wanda ya tabbatar da ikon jama'ar Tibet na sa hannu cikin harkokin kasa da kuma tafiyar da harkokinsu su da kansu. A Teng, mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar jihar Tibet, ya ce,"Taron wakilan jama'ar jihar Tibet da aka kira a watan Satumba na shekarar 1965 alama ce da Tibet ta fara tafiyar da tsarin cin gashin kanta. A gun taron, an zabi kwamitin jama'ar jihar Tibet, kuma daga nan, aka sami hukumar Tibet mai cin gashin kanta, wato majalisar wakilan jama'a da kuma kwamitin jama'a."

Tsarin cin gashin kai ya tabbatar da ikon 'yan kananan kabilu na sa hannu cikin harkokin siyasa da kuma tafiyar da harkokinsu su da kansu. A halin yanzu, 'yan kabilar Tibet da na sauran kananan kabilu sun kai sama da kashi 94% na wakilan jama'ar jihar Tibet su 34,000, kuma 'yan kabilar Tibet da na sauran kananan kabilu suna rike da muhimman mukamai a cikin hukumomin Tibet da majalisar wakilan jama'ar Tibet. A lokacin taron wakilan jihar Tibet da a kan kira kowace shekara, wakilan jama'ar Tibet su kan gabatar da shawarwari da ra'ayoyi sama da dubu 10 ta fannonin siyasa da tattalin arziki da al'adu da zaman al'umma, wadanda kuma ke taka muhimmiyar rawa ga cigaban tattalin arziki da zaman al'umma a Tibet.

Kelzang Teshe, wani manazarci a cibiyar nazarin zaman al'ummar Tibet ya ce, gyare-gyaren dimokuradiyya ne suka kawo wa Tibet manyan sauye-sauye, ya ce,"rabin karni ne kawai bayan da aka yi gyare-gyaren dimokuradiyya a Tibet, aka samu manyan sauye-sauye a Tibet. Idan babu gyare-gyaren dimokuradiyya da sauyin tsarin siyasa da zaman al'umma, lalle, ba za a iya samun irin manyan sauye-sauye ba." (Lubabatu)