Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-23 15:37:27    
Ra'ayoyin da wasu masu sauraronmu suka aiko mana

cri

Dangane da batutuwan da suka shafi ballewar jihar Tibet daga kasar Sin, a yadda abubuwan suka nuna, a ra'ayina zancen ma bai taso ba. A nawa tunanin ba wai bawa Jihar Tibet 'yancin ballewa ne matsala ba, a'a, a da zarar ta samu irin abinda take kira "'yanci" ya tabbatar, to fa farkon gutsuri-tsoma kenan, ba sauran zaman lafiya a wannan yanki. Domin kasar America (watau U.S.= Uwar Shaidanu) ta samu damar shigowa cikin kasar Tibet din domin yin angizon da zai hana zaman lafiya da ci gaban zamani da tattalin arziki, da yanzu suke wanzuwa a wannan yankin mai albarka. Kuma ko ma dai da yake yanzu an sami canjin gwabnati a Amerika kuma canjin jam'iyya mai mulki, a tsarin Amurka ba lallai yayi wata canzawar a-zo-a-gani ba dangane da harkar tafiyar harkokin kasashen waje ba. Bayan nan kuma tun dai ita Tibet ai ba ita kadai bace yankin kasar Sin, ba don menene ita za ta damu da sai ta balle idan dai ba wata boyayyar manufa ko wata kinaya da ake so a kitsa tsakaninta ta da wasu kasashen da ba sa so a zauna lafiya a kasar Sin ba? .Kuma a yanzu a yau din nan me yankin Tibet ya rasa na abin ya shafi ci gaban zamani, ko kuma akwai hakki da aka hana ta na tafitar da harkokin more rayuwa ko na bin addininta na 'yan yankinsu? Ni dai a iya sani babu. Saboda haka, Tibet tayi ta zama a matsayinta na jiha a cikin kasar Sin har abadan abada!Bissalam.

Salihu Abdullahi Kiyawa