Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-18 10:51:53    
Me ya sa ake ta da zaune tsaye a kasar Madagascar

cri

Cikin shirin yau za mu mai da hankali a kasar Madagascar da ke gabashin Afirka, inda a rana 17 ga watan Maris Marc Ravalomanana, shugaban kasar,ya ba da umarnin rushe gwamnati da kafa kwamitin zartaswa na soja don aiwatar da ikon shugaban kasa. Amma shugaban kwamitin soja ya ce an riga an mika ikon shugaba ga Andry Rajoelina, shugaban 'yan Adawa, yayin da Mista Rajoelina ya yi ikirarin cewa ya riga ya zama shugaban kasar, kuma zai shirya babban zabe cikin shekaru 2.

Manazarta na ganin cewa, dalilan da suka sa ake samun fadi-tashi kan harkokin siyasar kasar Madagascar, su ne, da farko, manufar kasar kan tattalin arziki ba ta ba jama'a gamsuwa ba. Bayan da Ravalomanana ya kama mulki a shekarar 2002, ya taba gabatar da taken manufar raya tattalin arziki na "mai dorewa kuma cikin sauri", ta yadda ya samu yabo. Sai dai lokacin da ya yi tazarce a shekarar 2007, ya fito da matakan tattalin arziki wadanda ba su dace da halin da ake ciki ba, sa'an nan ya kasa kyautata halin zaman rayuwar jama'a kamar yadda ya alkawarta. Talaucin da kasar ke fama da shi ya haddasa rashin gamsuwa a cikin jama'ar kasar.

1 2 3