Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-16 21:55:47    
Daga "likitoci manoma" zuwa asibitocin kauyuka

cri
Sakamakon kyautatuwar sabon tsarin bada hidimar jiyya ga manoma cikin hadin-gwiwa a kauyuka, aikin kiwon lafiya da na jiyya a kauyukan kasar Sin yana bunkasuwa yadda ya kamata. A cikin 'yan shekarun nan, an kara kafa asibitoci a kauyukan kasar Sin, ta yadda za'a sassauta matsalar da manoma suke fuskanta a fannin samun jinya.

Masu saurare, a cikin tarihin kiwon lafiya na kasar Sin, musamman ma daga shekarun 1960 zuwa 1980 na karnin da ya gabata, akwai wasu likitoci na musamman, wadanda suka gudanar da aikin jinya a kauyuka amma ba su yi rajista da gwamnati ba. A wancan lokaci, a kan zabi wasu mutane daga iyali wanda ya yi suna a fannin aikin jiyya daga zuriya zuwa zuriya, da dalibai wadanda ke da ilimi a likitanci daga makarantun midil da sakandare, sa'annan aka horas da su a fannin likita, don su zama irin wadannan "likitoci manoma".

Membar majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa a karo na 11, kana babbar malama mai kula da masu karatun digiri na uku, Madam Adaleti Ahmatjan ta siffanta likitoci manoma kamar haka:"Kafin a aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, akwai wasu likitoci manoma, wadanda suka fito daga kauyuka, inda aka horas da su har na tsawon 'yan watanni, daga baya suka yiwa mutane jiyya ta hanyar yin amfani da allura da magungunan gargajiya."

Tare da taimakon kayayyakin aikin jiyya na tsohon zamani, da aiki tukuru da suka yi, likitoci manoma suka bayar da kyawawan hidimomin jiyya ga manoma masu dimbin yawa a kasar Sin, da bayar da babbar gudummawa a fannin warware matsalar karanci ko rashin likitoci da magunguna a wancan lokaci.

Amma, yiwa mutum jiyya, ba wani abu ne mai sauki ba, rashin cigaba a harkar aikin jiyya, da karancin kyawawan na'urorin jiyya a wancan lokaci, sun jawo tsaiko ga aikin ceto mutane cikin gaggawa. Wani dan kabilar Tatar, kana shi ma memban majalisar bada shawarwari ne kan harkokin siyasa ta kasar Sin Mista Elidos Ahtemof ya tuna zahirin musabbabin rasuwar kakansa, inda ya ce:"A wancan lokaci, sakamakon rashin kyautatuwar sharadin aikin jiyya, har wata karamar tiyata ba'a iya yi ba, kamar cutar tsiro a uwar hanji. Kakana ya kamu da wannan cuta a yayin da yake shekaru 55 da haihuwa, amma saboda babu wanda ya iya warkar da shi, ya riga mu gidan gaskiya. Amma gaskiya, wannan tiyata na da sauki."

Masu saurare, a cikin 'yan shekarun nan, gwamnatin kasar Sin na kara maida hankali kan kyautata sharadin aikin jiyya, da inganta aikin bada hidimar jiyya a kauyukan kasar, adadin asibitocin kauyuka ya yi ta karuwa ainun, wadanda suke kawo sauki ga zaman rayuwar manoma.

Madam Adaleti Ahmatjan ta cigaba da cewa, a cikin 'yan shekarun nan, gwamnati ta sayowa asibitoci na kananan hukumomi na'urorin aikin jiyya na zamani. Yayin da musulma Guo Cunjun, wadda ta fito daga yankin Changji mai zaman kansa na jihar Xinjiang ta kasar Sin take hira da wakilinmu, ta yi bayani kan halin da ake ciki a asibitoci dake kauyenta, inda ta ce:"Yanzu a cikin asibitocin kauyenmu, akwai na'urorin aikin jiyya na zamani iri-iri, ciki har da na'urar CT, da na'urorin auna bugun zuciya da dai sauransu."

Dangane da kyautatuwar sharadin aikin jiyya a matsugunan musulmi a jihar Xinjiang ta kasar Sin, Madam Adaleti Ahmatjan ta yi farin-ciki sosai, haka kuma ta bayar da wasu shawarwari game da yadda za'a yi don kara raya harkokin kiwon lafiya da aikin jiyya a jihar, inda ta bayyana cewa: "Ina fatan za'a kafa wani cikakken tsari na sa ido kan aikin jiyya, da inganta kwarewar mutane masu kula da kudaden da ake kashewa a fannin bada hidimar jiyya ga manoma cikin hadin-gwiwa a kauyuka, ta yadda za'a yi amfani da wadannan kudade da gwamnatin kasar ta ware yadda ya kamata."

A ranar 5 ga watan da muke ciki, a yayin bikin kaddamar da zaman taro na 2 na majalisar wakilan jama'ar duk kasar Sin a karo na 11, a madadin gwamnatin kasar Sin, firaminista Wen Jiabao ya gabatar da rahoto kan aikin gwamnatin, inda ya bayyana hakikanan matakai da za'a dauka don kyautata tsarin bada hidimar jiyya a kananan hukumomi:

"Ya kamata a yi kokari don kyautata tsarin bada hidimar jiyya a kananan hukumomin kasar Sin. Bisa shirin da aka tsara, a shekarar bana, za'a kammala aikin gina asibitoci da yawansu ya kai dubu 29 a garuruwa. A cikin nan da shekaru 3 masu kamawa, gwamnatin kasar za ta ware karin kudade don nuna goyon-baya ga aikin gina asibitoci da sassan kula da lafiyar jama'a a kananan hukumomin kasar."

To, masu saurare, muna da imanin cewa, musulmi manoma da makiyaya daga kabilu daban-daban a jihar Xinjiang za su cimma alfanu daga jerin matakan da gwamnatin kasar Sin ke dauka a fannin kiwon lafiya da aikin jiyya. To, jama'a, yanzu sai ku dan shakata kadan, daga bisani za mu dawo domin kawo muku wasu labarai dangane da kananan kabilun kasar Sin.

Jama'a masu saurare, muna muku lale marhabin da sauraren shirinmu na "Kananan Kabilun kasar Sin". Yanzu sai ku gyara zama ku saurari labarai biyu dangane da kananan kabilun kasar Sin.

------ Kwanan baya, dan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin Mista Qiangba Puncog ya nuna cewa, hanya mafi kyau da za'a bi domin yaki da tsirarun 'yan a-ware, da masu fafutukar neman 'yancin kan Tibet ita ce, a gaggauta raya jihar, da kyautata zaman rayuwar al'ummar jihar. Matukar aka inganta hadin-gwiwa tsakanin al'ummar jihar Tibet, duk wani yunkuri na kawo baraka da tsirarun 'yan a-ware suke yi zai ci tura!

Qiangba Puncog ya ce, ko a da, ko a yanzu, ko kuma a nan gaba, gungun mutane mabiya Dalai Lama, da sauran 'yan a-ware sun dade suna watsa rade-radi game da gwamnatin kasar Sin da hukumar jihar Tibet mai cin gashin kai. Dangane da irin wadannan danyun aiki, abu da ya kamata a ba fifiko shi ne raya harkokin jihar Tibet daga dukkan fannoni.

Kwanan baya, a yayin da dan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, kana manazarci daga cibiyar nazarin ilimin zaman al'umma ta kasar Mista Chao Ke ke zantawa da wakilin CRI, ya bayyana cewa, kamata ya yi gwamnatin kasar Sin ta fitar da wasu dokokin shari'a, da manufofi, da ka'idoji, a wani kokarin kare harsunan kananan kabilun kasar Sin.

Chao Ke ya ce, a cikin 'yan shekarun nan, an cimma dimbin nasarori a fannin habaka tattalin arzikin kasar Sin, ya kamata a kara kokari wajen kare harsunan kananan kabilu, wadanda mutane kalilan ne ke yin amfani da su. A halin da ake ciki yanzu, harsuna na kananan kabilu dake arewa maso gabashi da kuma kudancin kasar Sin suna dab da bacewa, inda Mista Chao Ke ya ce:"Harshe, da al'adu na duk wata kabila, abubuwa ne da aka shafe shekara da shekaru aka gada daga kaka da kakanni. A shekarar bana, ina dauke da shawarwari guda biyu, na farko shi ne, a kafa yankunan musamman don kare harsuna da al'adun gargajiya na kananan kabilu, na biyu kuwa shi ne, a zuba karin kudade a fannin kare harsuna da al'adun gargajiya na kananan kabilu."