Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-13 21:31:52    
Kasar Sin na cike da imani kan fuskantar matsalar kudi ta duniya

cri
A ranar 13 ga wata, an rufe taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, wato hukumar koli ta kasar a nan birnin Beijing, inda aka zartas da rahoton ayyukan gwamnati da firayin minista Wen Jiabao ya yi, kuma an amince da kudurai da dama a jere da gwamnatin kasar ta yi don magance matsalar kudi da duniya ke fuskanta. A gun taron manema labaru da aka shirya bayan taron kuma, Mr. Wen Jiabao ya amsa tambayoyi na manema labaru na gida da waje dangane da yadda kasar Sin ke shirin magance matsalar kudi, da kuma sauran batutuwa, kazalika kuma ya jaddada cewa, kasar Sin na cike da imani kan fuskantar matsalar, kuma tana son hada kai tare da kasashen duniya, don warware matsalar.

A cikin wadannan tambayoyi guda 23, akwai kashi 70 cikin dari da suke shafar matakan da kasar Sin ta dauka kan harkokin gida da na waje don magance matsalar kudi. Mr. Wen Jiabao ya yi cikakken bayani kan kudurin zuba jari na kudin Sin RMB biliyan 4000 da kasar Sin ta gabatar,

'Wadannan kudurai a jere na kunshe da abubuwa a fannoni guda hudu, wato kara zuba jari bisa babban mataki da gwamnatin kasar za ta yi, da daidaita da farfado da sana'o'i bisa babban mataki, da kara nuna goyon baya a fannin kimiyya da fasaha, da kuma kara matsayin ba da tabbacin taimako ga jama'a.'
Mr. Wen Jiabao ya kara bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai da yawa a sauran fannoni, ciki har da rage kudin haraji, da inganta samun aikin yi, da kyautata tsarin ba da tabbacin taimako ga jama'a, da dai sauransu.

A wannan halin da ake ciki na fuskantar matsalar kudi ta duniya, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da tushe na tabbatar da samun karuwar jimlar kudin kayayyakin da za a iya samarwa a gida na kasar da cewar za ta kai kashi 8 cikin dari a shekarar bana, wannan ya jawo hankulan mutane sosai. A lokacin da yake amsa tambayoyin 'yan jarida, Mr. Wen Jiabao ya bayyana ba tare da rufa-rufa ba cewa, akwai yiwuwar tabbatar da kafa wannan tushe sakamakon kokarin da za a yi duk da kasancewar wahalhalu.

Kasar Sin da ke adane da kudaden musaya na dalar Amurka biliyan 2000 ta riga ta zama kasa mafi girma mai bin kasar Amurka basussuka. Mr. Wen Jiabao ya ce, kasar Sin na mayar da hankali sosai kan samun bunkasuwar tattalin arzikin Amurka. Sabuwar gwamnatin kasar Amurka ta dauki matakai a jere don magance matsalar kudi, kasar Sin na fatan samun nasarori sakamakon wadannan matakai.

'Mun ba da rancen kudi da yawa ga kasar Amurka, ko shakka babu muna kula da tsaron kudinmu. Gaskiya ce, ina damuwa kan wadannan kudade. Sabo da haka, na kara jaddada cewa, muna bukatar kasar Amurka da ta ba da lamuna, da cika alkawarinta, don tabbatar da tsaron harkokin kudi na kasar Sin.'

Game da taron koli game da harkokin kudi na kungiyar kasashe 20 da za a shirya a birnin London, Mr. Wen Jiabao ya bayyana cewa, lallai bai kamata a manta da kasashe masu tasowa a lokacin da ake magance matsalar kudi ta duniya ba.

'A yayin da ake fuskantar matsalar kudi, kasashe masu tasowa sun fi haduwa da wahalhalu, da kuma kasa samun kulawa. Tilas ne, taron koli na harkokin kudi na kungiyar kasashe 20 ya mayar da aikin ba da taimako da kula da kasashe masu tasowa, musamman ma kasashe mafiya karancin ci gaba a matsayin muhimmin batu.'
Ban da kokarin magance matsalar kudi da kasar Sin ke yi, kuma ko gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da yin shawarwari tare da Dalai Lama, ko a'a, wannan ya zama wani batu na daban da ke jawo hankulan 'yan jarida. Mr. Wen Jiabao ya bayyana cewa,

'Dalai Lama ba mai bin addini na gaskiya ba ne, wani 'dan siyasa ne mai gudun hijira. A hakika dai, gwamnatin gudun hijira da ya kafa wata haramtacciyar gwamnati ce da tayi shinkafa da waken siyasa da addini, wadda ke karkashin shugabancinsa kai tsaye. Dalai Lama yana yawo a kasashe daban daban, don rikita tunanin wasu 'yan siyasa, a waje guda kuma, wasu kasashen yamma suna yin amfani da shi.'

A gun taron manema labaru da aka shirya a wannan rana kuma, Mr. Wen Jiabao ya amsa tambayoyin da 'yan jarida suka yi a fannonin manufar farashin kudi ta kasar Sin, da dangantakar da ke tsakanin babban yankin kasar Sin da Taiwan wajen tattalin arziki da ciniki, da dai sauransu.