Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-13 18:48:46    
Kasar Sin na nuna hazaka a fannin tabbatar da ingancin kayayyakin abinci da magunguna

cri
A ranar 5 ga wata, firaministan kasar Sin Mista Wen Jiabao ya gabatar da rahoton aikin gwamnati, inda ya nuna cewa, a shekarar da muke ciki, Sin za ta rubanya kokari wajen sa ido kan ingancin kayayyakin abinci da na magungunan da ake sayarwa, da kyautata sa'annan da aiwatar da ma'aunin ingancin kayayyaki, ta yadda jama'a za su saya, kana su yi amfani da kayayyakin abinci ba tare da matsala ba.

A cikin shekaru 20 da suka gabata, sana'ar harhada kayan abinci ta kasar Sin ta samu bunkasuwa cikin sauri, amma don rage yawan kudaden suke kashewa a fannin samar da kayayyaki, akwai wasu kamfanoni wadanda suke sanya sinadarai a cikin kayan abinci yadda suka ga dama. Bisa ka'idojin da dokar da ta shafi ingancin abinci ta tanada, an ce, duk wani yunkuri na saka sinadarai a cikin kayan abinci ba bisa doka ko ka'ida ba, laifi ne wanda ke sabawa doka.

Mista Ye Jiannong, wani kwararre a fannin ilimin Chemistry, wanda a yanzu haka yake halartar taron shekara-shekara na majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin a nan birnin Bejing yana ganin cewa, sinadaran da ake sanyawa a cikin abinci, abubuwa ne da 'yan Adam suke harhadawa, wadanda akasarinsu har yanzu dai ba'a tabbatar da yawan gubar dake cikinsu ba, inda Mista Ye ya bayyana cewa:

"Matukar an dade ana yin amfani da wani irin sinadarin da aka saka a cikin kayan abinci, da tabbatar da cewa, sinadarin ba ya kunshe da guba, to, za'a iya saka sunansa cikin takardar jerin sunayen sinadaran da aka amince da sakawa a cikin kayan abinci."

Daidai kamar yadda ingancin kayayyakin abinci yake, haka ma ingancin magunguna yana shafar zaman lafiyar jama'a. Memban majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin, kana babban manazarci daga cibiyar nazarin likitancin gargajiyar kasar Sin Mista Shi Dazhuo ya nuna ra'ayinsa da cewa, kamata ya yi gwamnatin kasar ta kara karfin sa ido kan harkokin saye da sayar da magunguna, don bada cikakken tabbaci ga jama'a da su yi amfani da magunguna yadda ya kamata, inda Mista Shi ya ce:

"A halin da ake ciki yanzu, kasar Sin tana maida hankali da sa ido sosai kan ingancin magunguna a lokacin da ake harhada su a kamfanoni, amma a yayin da ake sayar da su a kasuwanni, har yanzu ba'a samu wani cikakken tsari ba na bincike da sa ido a kan hakikanin amfaninsu ga jama'a."

A nasa bangare kuma, yayin da mataimakin shugaban kamfanin harhada kayan abinci na Guangming na Shanghai, wanda kuma shi ma memban majalisar bada shawarwari ne kan harkokin siyasa ta kasar Sin Mista Ge Junjie ke zantawa da wakilin CRI, ya ce, kamfaninsa ya kafa wani kyakkyawan tsari na sa ido kan ingancin kayayyakin abinci, inda ya nuna cewa:

"Idan ingancin kayan abinci da muke samarwa ba shi da kyau, babu shakka kamfaninmu zai rushe. Duk kamfanoni kanana ko matsakaita, abun da ya kamata su ba fifiko shi ne daukar nauyin dake kansu na samar da kayan abinci mai inganci."(Murtala)