Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-11 19:28:15    
Manyan sauye-sauyen da gyare-gyaren dimokuradiyya suka kawo wa Tibet cikin shekaru 50 da suka wuce

cri

Ran 28 ga wannan wata rana ce ta tunawa da cika shekaru 50 da yin gyare-gyaren dimokuradiyya a jihar Tibet ta kasar Sin. Mahalartan taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar da ake yi yanzu a nan birnin Beijing, suna ganin cewa, a cikin shekaru 50 da suka wuce, manyan sauye-sauye sun auku ta fannonin siyasa da tattalin arziki a Tibet, kuma gyare-gyaren dimokuradiyya sun kawo wa jama'ar Tibet zaman alheri cikin 'yanci da zaman daidaici.

Karma Rinchen, wani wakilin jama'a dan kabilar Tibet yana da zama a filin ciyayi da ke arewacin jihar Tibet, wato muhimmiyar makiyaya ta wurin. Yau da shekaru 50 da suka wuce, garinsa na bin tsarin mallakar bayi manoma, kuma iyayensa duk sun kasance bayi manoma, ba su da 'yanci. Amma yanzu, yana iya halartar taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a madadin 'yan garinsa, don yin shawarwari tare da wakilan da suka zo daga sauran wuraren kasar kan harkokin kasa. A game da sauye-sauyen da suka auku a garinsa, cike yake da murna kuma ya ce,"Kasancewata zuriya ga bayi manoma a zamanin da, na taba shan wahala sosai a tsohuwar Tibet. Bayan da aka yi gyare-gyaren dimokuradiyya a Tibet, musamman ma bayan da Sin ta fara aiwatar da manufar gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, bisa taimakon gwamnati, na sayi motar sufuri, kuma na gudanar da hidimomin yawon shakatawa, zaman rayuwata ya yi ta samun kyautatuwa. Bisa taimakon gwamnati, a shekarar bara, na sami sabon gida. Yanzu yarana biyu suna cikin makarantar midil, kuma gwamnati na ba su abinci da gidan kwana da kuma kudin karatu."

1 2 3