Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-11 17:24:14    
Li Changchun ya bayyana cewa, ya kamata a sa kaimi ga aikin yada al'adu a kauyuka don amfana wa jama'a

cri

A ran 7 ga wata, wakilin zaunannen kwamiti na hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS Li Changchun ya bayyana cewa, ya kamata a sa kaimi ga aikin yada al'adu a kauyuka domin amfanawa jama'a.

Li Changchun ya fadi haka ne lokacin da ke halartar taron tattaunawar rahoton aiki na gwamnati da wakilan jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kai suka yi a ran nan da safe. Kuma ya kara da cewa, "Ya kamata mu raya ayyuka biyar a fannin al'adu don amfana wa 'yan kauyuka. Na farko shi ne ya kamata ko wane kauyen da yawan mutanensa ya zarce 20 ya iya samun shirye-shiryen rediyo da kuma talibijin. Na biyu shi ne ya kamata a raya aikin more labarun al'adu na zamani a duk fadin kasar Sin, wato za a tattara littattafai da wake-waken gargajiya na Sin da ilmin kimiyya da fasaha a fannin ayyukan gona tare, daga baya kuma za a canja su zuwa bayanai na digital na zamani domin a same su ta hanyar sadarwa ta zamani wato Internet. Haka kuma za a raya dakunan littattafai a kauyuka da kuma gina cibiyoyin al'adu na kauyuka da gundumomi domin warware matsalolin da jama'a ke fuskanta wajen karancin harkokin al'adu. Bugu da kari kuma za a samar da film daya ga manoma domin jin dadin jama'a." (Kande Gao)