Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-11 17:14:34    
Horar da ma'aikatan kotu da hukumar gabatar da kararraki na da muhimmanci sosai

cri

Mr.Chen Jianguo

A ran 11 ga wata, 'yan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kai ta kasar Sin sun tattauna kan rahotannin aiki na kotun koli ta kasar Sin da kuma hukumar koli ta gabatar da kararraki ta kasar a jiya da yamma, inda suka bayyana ra'ayin cewa, kotun koli da kuma hukumar koli ta gabatar da kararraki sun gudanar da dimbin ayyuka wajen horar da ma'aikatansu ko a fannin kwarewarsu ta aiki ko a fannin dabi'a, da kuma kara sanya ido a kansu, ta yadda aka kyautata hazakar ma'aikatansu sosai, amma a waje daya kuma rahotannin ba su boye abubuwa marasa kyau a wannan fanni ba. Don haka bayan da 'yan majalisar suka saurari rahotannin, sun bayyana cewa, an karfafa zukatansu sosai wajen raya tsarin dokoki na gurguzu da ke da halin musamman na kasar Sin da kuma yanke hukunci cikin adalci.

Haka kuma a cikin dukkan rahotannin biyu, an sa muhimmanci sosai kan kafuwar kotuna da hukumomin gabatar da kararraki a kananan wurare da ke tsakiya da kuma yammacin kasar Sin. Game da wannan, sakataren sashen Ningxia na JKS Chen Jianguo ya bayyana cewa, "Idan kotuna da hukumomin gabatar da kararraki na jiharmu ba su iya samun isassun ma'aikata ba, to ya kamata mu dauki ma'aikata daga birane da gundumomi bisa kwarewarsu ta aiki. Kuma bayan da muka dauke su, to ya kamata a aika su zuwa kananan wurare domin samun horaswa, wannan wani muhimmin mataki ne wajen kyautata hazakar ma'aikata da kuma fahimtar halin da kasar Sin ke ciki."