Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-11 17:05:35    
Rahoton aiki na majalisar NPC ya shaida amfanin majalisar sosai

cri

Madam Li Zhimin

A ran 10 ga wata da safe, 'yan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na jihar Xinjiang mai cin gashin kai sun ci gaba da tattaunawa kan rahoton aiki da shugaban majalisar Wu Bangguo ya yi jiya, inda Li Zhimin, mataimakin shugaban kungiyar 'yan kwadago ta jihar Xinjiang ta bayyana cewa, a shekarar da ta gabata, an gabatar da shirye-shiryen tattaunawa fiye da 400 da kuma shawarwari fiye da 6000, kuma an mayar da martani a kansu cikin lokaci domin bukatar hukumomin da abin ya shafa da su daidaita su yadda ya kamata. Ko da yake wasu batutuwa sun gamu da matsaloli, amma irin wannan ra'ayin da ake dauka wajen daidaita batutuwa ya yi daidai sosai.

Ban da wannna kuma Li Zhimin ta nuna yabo sosai da muhimman ayyukan da zaunannen kwamitin kula da harkokin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin za su gudanar a shekarar da muke ciki, inda ta bayyana cewa, "zaunannen kwamiti na majalisar za su gudanar da muhimman ayyuka uku a shekarar bana, wato kara kafa tsarin dokoki da ke dacewa da halin musamman da kasar Sin ke ciki, da kara sanya ido kan manyan ayyukan da gwamnatin kasar Sin ke cikin shirin gudanarwa, da kuma kara yin cudanya da kuma raya majalisar kanta. Ko da yake wadannan ayyuka ba yawa, amma su shaida halin musamman na majalisar da kuma amfanin da majalisar ke bayarwa."(Kande Gao)