Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-10 16:21:09    
Zhou Yongkang ya bayyana cewa, ya kamata a mai da hankali kan zaman rayuwar jama'a domin tabbatar da samun kwanciyar hankali a kasar Sin

cri
A ran 6 ga wata, Zhou Yongkang, zaunannen dan hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS ya bayyana cewa, ya kamata a mai da hankali kan zaman rayuwar jama'a domin tabbatar da samun kwanciyar hankali a kasar Sin.

Zhou Yongkang ya fadi haka ne lokacin da ke halartar taron tattaunawar rahoton aiki na gwamnatin kasar Sin da firayim minista Wen Jiabao ya bayar a ran 5 ga wata. Kuma ya kara da cewa,"makasudinmu na samun bunkasuwa shi ne jama'a su iya jin dadin zaman rayuwarsu. Shi ya sa lokacin da muke raya kasarmu, ya kamata mu yi la'akari kan yadda ya kamata mu yi domin tabbatar da jama'a su ji dadin zamansu. Amma ya zuwa yanzu ana kasancewar matsalolin rashin samun daidaito da rashin samun dauwamammen ci gaba, shi ya sa ba yadda za a yi sai mu raya kasa bisa ilmin kimiyya. In ba a yi haka ba, to, jama'a ba za su iya jin dadin zaman rayuwarsu ba, har ma za su sha wahalhalu, balle ma samun ci gaba cikin dogon lokaci. A cikin rahoton aiki na gwamnati, an gabatar da batutuwan samun guraban aikin yi da samun ilmi da ishorar tsoffi da kuma kiwon lafiya, duk wadanda ke da nasaba da zaman rayuwar jama'a. In an iya warware matsaloli kan batun, to za a kafa wani tushe mai inganci wajen tabbatar da samun kwanciyar hankali a zaman al'umma."(Kande Gao)