Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-09 22:17:35    
An kafa yankin kiyaye muhallin halittu da al'adu na kabilar Qiang

cri
Kabilar Qiang mai mutane sama da dubu 300, wata karamar kabila ce dake da tsawon tarihin shekaru dubbai a kasar Sin. Akasarin 'yan kabilar Qiang suna zaune a lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin.

A matsugunar kabilar Qiang, a kan ga mutane sun taru suna yin raye-raye a yayin da suke busa sarewa. Amma mummunan bala'in girgizar kasa da ya fadawa gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan a ranar 12 ga watan Mayu na shekarar 2008 ya lalata zaman lafiya da kwanciyar hankalin da 'yan kabilar Qiang suke ciki.

Mummunan bala'in girgizar kasa ya kawo babban lahani ga cibiyar al'adun gargajiyar kabilar Qiang. Gunduma mai zaman kanta ta kabilar Qiang daya kadai a nan kasar Sin, wato gundumar Beichuan ta lardin Sichuan, ta zama wata gundumar da bala'in girgizar kasa ya yi kaca-kaca da ita, kusan rabin mazauna gundumar suka rasa rayukansu ko jikkata. A waje daya kuma, wasu kauyuka da gidaje masu sigar musamman ta kabilar Qiang sun ruguje. Har wa yau kuma, bala'in girgizar kasa ya kawo babbar illa ga muhallin halittu da 'yan kabilar Qiang suke zaune zuriya bayan zuriya, an binne kayayyakin tarihi, da tufafin gargajiya, da kayayyakin kida masu tarin yawa a karkashin baraguzan gine-gine.

Kamar yadda mataimakin darektan kwamitin kwararru kan harkokin kiyaye al'adun tarihi da ba na kayayyaki ba da aka gada daga kaka da kakanni na ma'aikatar al'adu ta kasar Sin Mista Liu Kuili ya ce, ya zama tilas a kare al'adun gargajiyar kabilar Qiang ba tare da wani jinkiri ba, inda ya bayyana cewa:"Cibiyar al'adun gargajiyar kabilar Qiang mai mutane masu dimbin yawa ta yi asara sosai sakamakon bala'in girgizar kasa. Idan an yi kokarin kiyaye su, za'a sake farfado da al'adun gargajiyar kabilar Qiang. Amma idan ba a iya daukar matakin da ya dace ba, mai yiwuwa ne yaren kabilar zai bace."

Bayan da aka aukuwar bala'in girgizar kasa, hukumomin kiyaye kayayyakin tarihi da sassan nazarin al'adun tarihi da dama na kasar Sin sun dauki matakai cikin gaggawa, da tura mutane zuwa yankunan da bala'in girgizar kasa ya ritsa da su, domin bada shawarwari kan yadda za'a kiyaye kayayyakin tarihi.

A cikin rabin shekara bayan aukuwar bala'in girgizar kasa, hukumomi da dama ciki har da ma'aikatar al'adun kasar Sin sun sanar da kafa yankin gwaje-gwaje na kiyaye al'adu da muhallin halittu na kabilar Qiang, domin kara kulawa da matsugunar kabilar Qiang dake lardunan Sichuan da Shanxi. Bisa shirin da aka tsara, an ce, zuwa shekarar 2015, ya kamata a sake farfado da zaman lafiyar 'yan kabilar Qiang, da kyautata tsarin gado na al'adun gargajiya na kabilar Qiang.

Mataimakin ministan kula da harkokin al'adu na kasar Sin Mista Zhou Heping ya ce, 'yan kabilar Qiang ba su da rubutattun kalmomin yarensu, shi ya sa su kan gaji al'adun gargajiya daga kakannin-kakanninsu ta baka, inda ya bayyana cewa:'Yan kabilar Qiang sun gaji kyawawan al'adun gargajiya daga kakannin-kakanninsu, shi ya sa abun da ya kamata a ba fifiko shi ne kare 'yan kabilar Qiang, ta yadda wadanda suka gaji al'adun gargajiya za su gudanar da harkokinsu yadda ya kamata."

Mataimakin darektan kwamitin kwararru kan harkokin kiyaye al'adun tarihi da ba na kayayyaki ba da aka gada daga kaka da kakanni na ma'aikatar al'adu ta kasar Sin Mista Liu Kuili ya shiga aikin tsara shirye-shiryen kiyaye al'adu da muhallin halittu na kabilar Qiang. Ya nuna cewa, matakan da ake dauka daga dukkan fannoni a halin yanzu suna dacewa da hakikanin halin da ake ciki, kuma za'a iya cimma burin gadar al'adun gargajiyar kabilar Qiang yadda ya kamata, inda ya ce:"Kusan lokacin da bala'in girgizar kasa ya faru, mun yi la'akari da makomar bunkasuwar al'adun gargajiyar kabilar Qiang, haka kuma mun samar da kyakkyawan sharadi ga aikin kiyaye su. Matukar mun cigaba da daukar duk wani mataki da ya wajaba kamar yadda muke yi a halin yanzu, za'a sake farfado da al'adun gargajiya na kabilar Qiang."

Mun dai kawo muku wani bayani dangane da yadda ake kokarin kiyaye muhallin halittu da al'adun gargajiya na kabilar Qiang. Yanzu sai ku dan shakata kadan, daga bisani za mu dawo domin kawo muku wasu labarai dangane da kananan kabilun kasar Sin.

A shekarar 2008, akwai karin manoma da makiyaya da yawansu ya kai dubu 312 a jihar Tiebt wadanda suka kaura zuwa sabbin gidajen kwana, matsakaicin kudin shiga da manoma da makiyaya suka samu ya yi ta karuwa cikin jerin shekaru 6.

Zuwa yanzu, gaba daya akwai manoma da makiyaya da adadin su ya kai dubu 860 wadanda suke jin dadin zama a sabbin gidajensu.

Baya ga gidajen kwana, a shekarar 2008, an gina sabbin dakunan biyan bukatun jama'a na yau da kullum da yawansu ya tasam ma 700 a kauyukan Tibet, da shimfida hanya a kauyuka guda 423. Yayin da zaman rayuwar manoma da makiyaya ke samun kyautatuwa, yawan kudin shiga da suka samu ya karu kwarai da gaske. A shekarar 2008, matsakaicin kudin shiga da manoma da makiyaya na Tibet suka samu ya kai kudin Sin Yuan 3170.

A ranar 5 ga wata, hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta jihar Tibet mai cin gashin kanta ta sanar da cewa, za'a shirya gasar kera tsarabobin yawon shakatawa a karo na farko nan ba da jimawa ba.

Masu saurare, sha'anin yawon shakatawa ya kasance babban jigo wajen bunkasa jihar Tibet, an yi hasashen cewa, a shekarar bara, yawan mutane masu yawon shakatawa daga cikin gida da waje da jihar Tibet ta karba ya kai miliyan 2.2, jimillar kudin shiga da aka samu daga wajen sha'anin yawon shakatawa ta zarce Yuan biliyan 2.2.

Bisa labarin da muka samu, an ce, a halin yanzu, yawan kudin da ake kashewa ta fannin sayayya ya dauki kashi 25 bisa dari na dukkan kudaden da ake kashewa ta fannin yawon shakatawa a Tibet. Sana'ar kera tsarabobin yawon shakatawa ta jihar ba ta samun bunkasuwa sosai. Ta hanyar shirya gasar kera tsarabobin yawon shakatawa a karo na farko, za'a nuna da tallata dimbin albarkatun yawon shakatawa da Allah ya horewa jihar Tibet, ta yadda za'a cigaba da bunkasa sha'anin yawon shakatawa na jihar.

An ce, jihar Tibet za ta kara tallafawa aikin raya tsarabobin yawon shakatawa, da kera tsarabobin yawon shakatawa masu sigar musamman ta jihar, da kafa cibiyar sayen tsarabobin yawon shakatawa.