Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-06 19:19:42    
Jama'ar Sin da gwamnatin Sin dukkansu na nuna karfin zuciya wajen tinkarar matsalar kudi tare

cri

A sakamakon mummunar matsalar hada-hadar kudi da ke addabar duk duniya, raguwar kudin shiga da wahalar samun aikin yi suna addabar fararen hula na kasar Sin a kusan rabin shekarar da ta gabata. Gwamnatin kasar Sin kuwa tana fuskanar kalubale da dama.

Domin tinkarar matsalar, tun daga karshen rabin shekarar bara, gwamnatin Sin ta fara mayar da habaka bukatu a gida da tattabar samun bunkasuwa a matsayin muhimmin aikinta, tare da aiwatar da jerin matakai. Wadannan matakai sun samu amincewa daga wakilai da mambobi da suke halartar tarurrukan shekara-shekara na majalisar NPC da ta CPPCC a nan Beijing.

Qi Xiaojin, wata wakiliyar jama'a da ke tafiyar da wata babbar masana'antar masaka. Ta yi karin bayanin cewa, shirin gwamantin na farfado da masana'antun masaka zai taka rawa wajen fitar da masana'antun masaka daga mawuyacin hali. Madam Qi ta ce,"Shirin farfado da masana'antun masaka ya tabbatar da cewa, masana'antun masaka shi ne kashin bayan tattalin arzikin jama'ar kasarmu, shi ne kuma muhimmin masana'antun da ke shafar zaman rayuwar jama'a, haka kuma, ya kan nuna fifiko sosai a kasuwannin duniya. Ya taka muhimmiyar rawa wajen raya kasuwa da kyautata aikin fici da samar da guraban aikin yi da kuma samar wa manoma karin kudin shiga. Ta haka mun gano cewa, ba za mu iya raya masana'antun masaka ba, sai dai muna iya tabbatar da matsayinsa a harkokin tattalin arzikin jama'a."

Ko da yake ba a aiwatar da wadannan matakai cikin dogon lokaci ba, amma matakan sun fara ba da taimako saboda gwamnatin Sin ta dauke su cikin lokaci kuma tana aiwatar da su da babban karfi. A gun taron manema labaru da aka yi a ran 6 ga wata, Zhang Ping, darektan kwamitin yin gyare-gyare da raya kasar Sin ya fayyace cewa, "A ganina, wadannan matakai na da amfani sosai. Wasu adadi na samun kyautatuwa. An hana raguwar farashin wasu kayayyakin da muke sayarwa zuwa ketare, wasu kuma an kara farashinsu kadan. Babu shakka ba za mu iya samun kwanciyar hankali ba tukuna, kuma ba a iya cewa, mun iya gudun illar da matsalar kudi ta kawo mana ba. Za mu ci gaba da mai da hankali kan sauye-sauyen da za a haifar. Amma muna da karfin zuciya wajen fita daga mawuyancin hali na yanzu da warware mastalar kudin."

A shekarar bana, gwamnatin Sin ta zuba makudan kudade kan harkokin al'umma domin habaka bukatu a gida da kuma tabbatar da samun bunkasuwar tattalin arziki. Haka kuma, ta zuba kudade masu yawa kan aikin gona. Wannan ya sanya Liu Yonghao, mamban majalisar CPPCC, manajan kamfanin aikin gona mai zaman kansa mafi girma a kasar Sin da sauran 'yan masana'antu na kauyuka sun inganta karfin zuciya. Mr. Liu ya ce,"Muna farin ciki sosai da ganin karuwar kudaden da za a zuba kan aikin gona. Gwamnatin Sin za ta kuma aiwatar da sabbin matakai a kan aikin gona da kauyuka da kuma manoma. Dukkansu sun kawo wa manoma kyakkyawan fata da kuma karfafa mana gwiwa."

Ga sauran fararen hula kuwa, samun aikin yi da kuma ci gaba da aikinsa na da muhimmanci sosai a halin yanzu. 'Yan ci rani kimanin miliyan 200 sun fi gamuwa da matsalar samun aikin yi. Hu Xiaoyan tana daya daga cikin 'yan ci rani, ita kuma wata wakiliyar jama'a ce da aka zaba. Tana ganin cewa, matakan gwamnatin na sa kaimi kan samun aikin yi sun sa 'yan ci rani su sami damar kyautata karfinsu. Inda ta ce,"Mu 'yan ci rani ya kamata mu yi kokari da kanmu tukuna domin tinkarar matsalar kudi ta duniya. Yanzu gwamnatinmu ta ba mu taimako, za mu iya koyon fasaha bisa abubuwan da muke so. Ina fatan 'yan ci rani da suka rasa aikin yi za su yi amfani da dama a bana domin kyautata karfinsu."

A bana, adadin karuwar tattalin arziki da gwamnatin Sin za ta nemi samu shi ne kashi 8 cikin dari. Ko da yake yana kasancewa wahalhalu da yawa, amma gwamnatin Sin da jama'arta suna nuna karfin zuciya ga tabbatar da samunsa.(Tasallah)