Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-05 18:05:02    
Kasar Sin take da imani da karfi wajen tinkarar hada hadar kudi ta duniya, a cewar Wen Jiabao

cri

Yau, wato ran 5 ga wata, an bude taron shekara-shekara na majalisar dokokin kasar Sin a nan birnin Beijing. A gun bikin kaddamar da taron, a madadin gwamnatin kasar Sin ne Mr. Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin ya bayar da wani rahoto game da ayyukan da gwamnatin ta yi a shekarar da ta gabata, da ayyukan da za ta yi a shekarar da ake ciki ga wakilai mahalarta taron kusan dubu 3. Lokacin da matsalar hada hadar kudi ta duniya take ta yaduwa a duk duniya, kuma ba a san lokacin da za a kawo karshen wannan matsala, wannan rahoton da gwamnatin kasar Sin ta bayar ya yi amfani da dimbin hakikanin abubuwa da adadi domin bayyana yadda take cike da imani da karfi wajen tinkarar wannan matsala da kuma tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasar Sin cikin sauri ba tare da tangarda ba. A waje daya, wannan rahoto yana bayyana yadda gwamnatin kasar Sin take bin tunanin kokarin kyautata zaman rayuwar jama'a da raya zaman al'umma mai jituwa ko da yake yanzu take cikin mawuyacin hali.

A cikin wannan rahoton da ke kunshe da bakake dubu 20, an tabbatar da cewa, yin fama da matsalar hada hadar kudi ta duniya da kuma ci gaban tattalin arzikin kasar cikin sauri ba tare da tangarda ba shi ne aiki mafi muhimmanci ga gwamnatin kasar Sin da dole ne ta yi a shekarar da ake ciki. Mr. Wen Jiabao ya ce, "Ainihin halin da kasar Sin ke ciki a fannin tattalin arziki da zaman al'umma da kuma kyakkyawar makomarsu ba su samu canji ba. Sakamakon haka, muna cike da imani da sharadi da karfi wajen tinkarar matsalolin da muke fuskanta domin neman samun nasarar tinkararsu."

A hakika dai, dalilin da ya sa gwamnatin kasar Sin take da imani shi ne ci gaban da kasar Sin ta samu a shekarar da ta gabata a fannonin tattalin arziki da zaman al'umma. Ko da yake kasar Sin ta gamu da bala'u daga indallahi sau da yawa, amma jimillar GDP ta kasar Sin ta kai fiye da kudin Sin yuan biliyan dubu 30, wato ta karu da kashi 9 cikin kashi dari bisa ta shekara ta 2007.

Bugu da kari kuma, kasar Sin ta samu imani ne domin ta samu nasarar tinkarar illar da matsalar hada hadar kudi ta duniya ke kawo mata a zagaye na farko. Game da ci gaban da gwamnatin kasar Sin ta samu bayan da ta dauki matakan tinkarar matsalar hada hadar kudi, Mr. Wen ya ce, "Wadannan matakai sun taka muhimmiyar rawa wajen sassauta sabane sabane masu tsanani da suke yin mummunan tasiri ga ci gaban tattalin arziki da kara imani da tabbatar da cimma buri da kuma karuwar tattalin arziki cikin sauri ba tare da tangarda ba."

Lokacin da gwamnatin kasar Sin take mai da hankali wajen tinkarar hada hadar kudi domin tabbatar da habaka bukatu a cikin gida da karuwar tattalin arziki, ba ta sake jikinta ba wajen kokarin kyautata zaman rayuwar jama'a. Ana ci gaba da bin tunanin sanya dan Adam a gaban kome da mai da hankali kan zaman rayuwar jama'a. Sabo da haka, a cikin rahoton gwamnati da Mr. Wen Jiabao ya bayar, an ce, gwamnatin za ta sanya batutuwan samar da karin guraban aikin yi da kara saurin kyautata tsarin ba da tabbaci ga jama'a a matsayi mafi muhimmanci da gwamnatin kasar Sin za ta yi namijin kokarin warware su. Mr. Wen ya nuna cewa, "kara mai da hankali kan zaman rayuwar jama'a da raya zaman al'umma mai jituwa" na daya daga cikin muhimman ka'idojin da gwamnatin kasar Sin take bi lokacin da take yin ayyukanta a shekarar da ake ciki. Mr. Wen ya ce, "A lokacin da ake cikin mawuyacin hali, dole ne a kara mai da hankali kan zaman rayuwar jama'a da raya zaman al'umma mai jituwa. Dole ne a tsaya sanya batutuwan ba da tabbaci ga jama'a da kyautata ingancin zaman rayuwar jama'a su zama mafari da burin da ake son cimmawa lokacin da ake raya tattalin arziki." (Sanusi Chen)