Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-05 09:41:11    
An bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin

cri

Ranar 5 ga watan Maris, an bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a birnin Beijing, hedikwatar kasar, da karfe 9 na safe,bisa agogon wurin. Taron majalisar wadda ke da ikon koli a kasar Sin ya sami halartar shugabannin kasar Sin da na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kamarsu Hu Jintao, da Wu Bangguo, da Wen Jiabao, da Jia Qinglin, da Li Changchun, da Xi Jinping, da Li Keqiang, da He Guoqiang, da Zhou Yongkang, da dai sauransu.

Wu Bangguo, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, shi ke jagorancin taron, inda Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin, ya gabatar wa wakilan jama'a kusan 3000 da rahoto kan aikin gwamnati a madadin gwamnatin tsakiyar kasar.

Cikin taron na kusan kwanaki 9, wakilan jama'ar kasar Sin za su dudduba rahotanni kan aiki na gwamnati, da zaunannen kwamitin majalisar, da kotun koli, da kyma na hukumar koli mai bin ba'asi da gabatar da kara, sa'an nan wakilan za su tattauna da zartas da shirin aikin gwamnati na shekara mai zuwa, da kasafin kudin kasar. (Bello Wang)