Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-27 15:37:48    
Yankin musamman na Macao na kasar Sin

cri
Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun Sa'idu Umar, wanda ya fito daga garin Akwanga, Nasarawa, tarayyar Nijeriya. A cikin wasikar da malamin ya aiko mana, ya ce, "ni mutum ne mai sha'awar yawon bude ido a wurare daban daban, kuma ina fatan wata rana Allah zai kawo ni kasar Sin in bude ido, yanzu ina fata za ku ba ni bayani a kan yankin Macao na kasar Sin a filin amsoshin takardunku".

To, malam Sa'idu, mun gode maka da aiko mana wannan tambaya, kuma muna fatan za ka gamsu da amsarmu. Macao yankin musamman ne na kasar Sin, wanda yake a mashigin teku na kudu maso yammacin kasar, kuma yana da nisan kilomita 60 daga yankin musamman na Hongkong na kasar. Fadin yankin Macao ya kai muraba'in kilomita 29.2, kuma yawan mutanensa ya kai dubu 557, wadanda daga cikinsu kashi 95% sun kasance Sinawa, a yayin da sauran 5% zuriyoyi ne na mutanen kasar Portugal da sauran al'ummomi. Sinanci da harshen Portugal harsuna biyu ne da hukumar Macao ke amfani da su wajen tafiyar da harkokinta. Akwai zafi da kuma damshi a yankin Macao, kuma yawan zafi ya kan sha bamban sosai a duk shekara.

Da a zamanin gargajiya, yankin Macao wani karamin kauye ne na kasar Sin. A shekarar 1535, mutanen Portugal sun dakatar da jiragen ruwansu a yankin Macao, domin yin ciniki da mutanen wurin. Daga baya, sun fara zuwa Macao da kuma zama a wurin. Tun bayan shekarar 1849, mutanen Portugal sun fara mallakar Macao. Sai kuma ya zuwa ran 20 ga watan Disamba na shekarar 1999 da aka maido da Macao a karkashin mulkin jamhuriyar jama'ar Sin.

A game da asalin sunan Macao, akwai labari. An ce, a zamanin da, wata rana, akwai rana sosai, ko gajimare babu, wani jirgin ruwan aikin su na tafiya yadda ya kamata a kan teku. Sai dai ba zato ba tsammani, guguwa ta yi awon gaba da shi. A cikin wannan mawuyacin hali, wata yarinya ta zo, kuma ta dakatar da guguwar tare kuma da maido da kwanciyar hankali a kan teku. Daga karshe, jirgin ruwan ya isa tashar jiragen ruwa lami lafiya. Daga nan ne, mazauna wurin suka gina wani dakin ibada a inda wannan yarinya ta sauka a gabar teku, don bauta mata, kuma suna kiran wannan dakin ibada "Ma Ge." A lokacin farkon zuwan mutanen Portugal a Macao a tsakiyar karni na 16, sun tambayi mazauna wurin sunan wurin da suka isa, amma mazauna wurin ba su gane ba, sun yi tsammanin ko dakin ibada ne bakin ke tambaya, shi ya sa suka amsa, "Ma Ge". Sabo da haka, mutanen Portugal suka fara kira wurin da sunan "Macao".

Bayan da Sin ta maido da Macao a karkashin mulkinta a shekarar 1999, sai aka kafa yankin musamman na Macao, inda aka aiwatar da manufar "kasa daya amma tsarin mulki iri biyu", kuma mutanen Macao suna cin gashin kansu wajen tafiyar da harkokinsu.

Macao tashar jiragen ruwa ce mai 'yanci, kuma tana aiwatar da manufar ciniki cikin 'yanci. Ban da wannan, hada-hadar cinikayya a fannin wasanni ta amfani da na'urorin zamani da yawon shakatawa da gine-gine da inshorar bankuna da kuma masana'antar gyaran kayayyaki sun kasance manyan ginshikai hudu na tattalin arzikin Macao. Bayan da aka maido da yankin Macao a karkashin mulkin kasar Sin, tattalin arzikinsa sai dinga bunkasa yake yi, yawan GDP nata ya yi ta karuwa cikin sauri shekaru 8 a jere. Har ma a shekarar 2007, yawan GDP da kowane mazaunin Macao ya samu ya kai dalar Amurka dubu 36, wanda ya zarce na Singapore da na Japan, har ma ya zama na farko a nahiyar Asiya. A shekarar 2008, duk da illoli a sanadiyyar matsalar kudi ta duniya, ba a lalata manyan fannoni na tattalin arzikin Macao ba. Ban da wannan, bayan da aka maido da Macao a karkashin mulkin gwamnatin kasar Sin, mu'amala da ke tsakanin Macao da babban yankin kasar Sin ta fannonin tattalin arziki da al'adu da zaman al'umma duk ta yi ta inganta.

Malam Sa'idu Umar, muna fatan Allah zai kawo ka Macao wata rana, ka yi yawon bude ido.(Lubabatu)