Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-26 16:32:35    
Makarantun firamare da taimakon mutumin Malasiya

cri
Mutumin Malasiya dan asalin kasar Sin da ake kiransa Chen Chengfa ya ba da taimakon kudin kafa makarantun firamare guda uku a birnin Shihezi na jihar Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar Sin inda ake koyarwa yara da harsuna biyu.Ina dalilin da ya sa wannan malami ya zo daga nesa zuwa jihar Xinjiang ta kasar Sin domin kafa makarantun firamare? To, a cikin shirinmu za mu ba ku cikakken bayani.

A farkon watan Satumba,makarantun kasar Sin sun shiga sabon lokacin karatu. Haka ma makarantar firamare ta farko ta gandun noma na Shihezi na jihar Xinjiang dake arewa maso yammacin kasar Sin ta shiga nata.malaman koyarwa da 'yan makarantar firamare na kabilu daban daban su fiye da dubu uku suna farin ciki kwarai da gaske sabo da suka sami sabin ginin karatu mai fadin muraba'in mita sama da dubu bakwai. Airken,dan makarantar firamare na kabilar Uighur da ya cika shekaru 11 da haihuwa a wannan shekara ya yi farin ciki da cewa:

"Wannan ginin da aka kafa yana da kyaun gani sosai. Ina so in yi karatu a ciki. Kaka Chen Chengfa ya kafa wannan makaranta tare da kudin taimakon da ya bayar.Mun yi masa godiya. Kamata ya yi in yi kokari wajen karatu kuma in samu ci gaba kowace rana."

Kaka Chen Chengfa da Airken ya ambata,mutumin Malasiya dan kasar kasar Sin ne,shi mai kishin kasar Sin ne ya ba da taimakon kudi na kudin Sin Reminbi Yuan dubu dari tara ya kafa makarantun firamare guda uku masu amfani da harsuna biyu a birnin Shihezi na jihar Xinjiang.

Da ya ke Mr Chen Chengfa bai taba ganin 'yan makarantun nan ba ya bayar da taimakon kudi ya kafa makarantun,me ya sa ya zabi wannan wuri? Dalili kuwa shi ne sakatarer kungiyar samari 'yan kwaminis ta birnin Shihezi na jiar Xinjiang Gu Jinhua ta sami wannan labari cewa wani mutumin Malasiya dan asalin kasar Sin yana so ya kafa makarantun firamare a bangaren iyakar kasa da kanana kabilu ke zaunne yayin da take halartar wani taron musayar ra'ayi a birnin Fuzhou,babban birnin lardin Fujiang dake kudu maso gabacin kasar Sin a watan Nuwamba na shekara ta 2005. Madam Gu Jinhua ta waiwayo yadda ta samo wannan labari ta furta cewa:

"sakataren kungiyar samari 'yan kwaminis ta birnin Fuzhou ya sanar da mu nufin da wani danginsa da Mr Chen Chengfa ke da shi na kafa makarantu a kasar Sin,ya kuma gaya mini cewa Mr Chen Chengfa ya yi kome cikin nitsuwa ya kan cika alkawarin da ya dauka,mutum ne mai nitsuwa.Bayan da Madam Gu Jinhua ta koma birnin Shihezi daga birnin Fuzhou,ba tare da bata lokaci ba sai ta sanar da sassan da abin ya shafa na ba da ilimi na birnin Shihezi,ta bukaci su yi mu'amalla da Mr Chen Chengfa. Cikin hanzari hukumar kula da ilimi ta birnin Shihezi ta jihar xinjiang ya samar da cikakken bayani kan ci gaban da aka samu wajen samun ilimi a wuraren da kanana kabilu ke zaune da kuma makarantun da ake fatan a gina su a cikin wasikar da ta aika zuwa ga Mr Chen Chengfa.

Bayan da ya samu wasika,Mr Chen Chengfa ya sane da akwai kabilu 47 da suke zaune a yankin Shihezi na jihar Xinjiang. Mutanen kabilun suna zaune a warwatse bisa yanayin da suke ciki da kuma dalilin tarihi,kuma ba su samu ci gaba sosai wajen samo ilimi,musamman a wasu gandunan noma,gidajen da suka gina domin 'yan makarantu a saukakke suke, an gina su ne a shekarun 1960 zuwa 1970. da ganin haka Mr Chen Chengfa ya kuduri aniyar kafa makarantu masu amfani da harsuna biyu.Nan ba da dadewa ba Mr Chen Chengfa ya yi hira da wakilin gidan rediyonmu daga kasar Malasiya ta wayar talifo,inda ya yi alfahari da cewa(??3) "da ya ke an haife ni ne a kasar Malasiya,amma na dauke kaina basine,ni basine na kwarai. A lokacin da nake cikin yarantaka,kasar Sin tana fama da talauci. An dauke ni saniyar ware yayin da nake kasuwanci a kasashen waje. A ganina mai da kasar Sin kasa mai karfi nauyina ne."

A shekara ta 2003 ne Mr Chen Chengfa ya fara kulla aminci da jihar Xinjiang ta kasar Sin.A wannan shekara Mr Chen Chengfa ya zo yankin Turfan na jihar Xinjiang domin yawon bude idanu. A cikin ziyararsa ya ankara wasu mutanen wurin ba su iya magana da sinanci ba sai yaren wurinsu kawai, da ya ke su ma sinawa,amma ba su iya sinanci,ba su iya yin mu'amala da mutane na sauran kabilu,idan suna so sun yi tattaunawa da mutane na sauran kabilu sai su nemi mai fassara. Da ganin haka wata dabara ta fado masa, yana so ya kafa makarantu masu amfani da harsuna biyu. A ganinsa ya kamata a horar da yara harshen sinanci da yarensu na Uighur da kara musu ilimi ta yadda za su iya bauta wa kasar mahaifa bayan da suka kammala karatunsu.

"yau shekaru hudu ke nan da na sa kafata a jihar Xinjiang.A wancan lokaci bai dora muhimmanci kan ilimi na kanana kabilu ba. Ina fatan mutanen kanana kabilu sun karo ilimi na dangane da al'adun kasar Sin, idan mutanen kanana kabilu sun gaza yin mu'amala da mu,ta yaya kasarmu ta zama kasa mai karfi."

A ranar 18 ga watan Afril na shekara ta 2006, gwamnatin birnin Shihezi ta jihar Xinjiang ta kasar Sin ta samui wasikar dake dauke da yarjejeniyar ba da taimakon kudi da Mr Chen Chengfa ya sa hannunsa a kai. Muhimmin abun da aka tanadi a cikin wasikar shi ne Mr Chen Chdengfa ya ba da kyautar kudi na kudin Sin Renminbi Yuan dubu dari tara wajen kafa makarantun firamare guda uku a birnin Shihezi na jihar Xinjiang.Bayan da makarantun uku suka sami taimakon kudi,sai su gaggauta kafa ko gyara dakunan karatu da na kwana na makarantu da kuma kyautata sharudan koyarwa.A cikin takardar ba da taimakon kudin, Mr Chen Chengfa ya kuma bayyana cewa zai kara kokarinsa wajen aiki,zai kuma ba da karin taimako gwargwadon iyawarsa a nan gaba.

Nan ba da dadewa ba sabbin gidaje da dakuna na makarantun firamare guda uku sun shimfidu daya bayan daya. Da samun labarin,Mr Chen Chengfa ya aika da sakon mika gaisuwa. Malaman koyarwa da 'yan makarantu da suka shiga sabbin gidaje da dakunan sun nuna godiyarsu ga Mr Chen Chengfa dake zama a kasar Malasiya ta wayar talifo ta duniya. Wani almajiri na kabilar Hui a aji na hudu na makarantar yana jin kunya kadan wajen yin magana ta wayar talifo ya ce : "zan kara rubanya kokarina wajen karatu in mayar da martani ga kaka Chen Cheng kan taimakon da ya ba mu. Zan yi kome kamar yadda kaka Chen ya yi a nan gaba,in je aiki a wuraren da ake fi samun matsaloli." Malaman koyarwa da 'yan makarantun sun kuma gayyaci Mr Chen Chengfa da ya zo jihar Xinjiang ta kasar Sin domin sake yin yawon bude ido idan ya samu dama.sun yi hira cikin yanayin arziki ta wayar talifo ta duniya:

Malami: Mista Chen, ina fatan za ka bakunci birnin Shihezi idan ka samu dama, za ka ga makarantun da aka gina da taimakonka da 'yan makarantun firamare da kanka.

Mr Chen: To,da kyau idan in samu dama.

Malamin: muna fatan harkokinka na ci gaba da habakawa.

Mr Chen: na gode. Ina so in sanar da kai cewa idan makarantun kanana kabilu suna bukatar taimako,sai ku aika da takardu zuwa gare ni,in yi kokarin ba da taimakona gwagwardon iyawata.

Kafin a kawo karshen hira,Mr Chen Chengfa ya sha bayyana fatansa na ba da karin taimako ga yankunan da kanana kabilu ke zaune,dalili kuwa shi ne yana da wata zuciya ta mai kishin kasa.