Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-24 16:16:17    
Kasar Sin tana cikin shirin kafa tashar bincike ta uku a nahiyar iyakacin duniya na kudu

cri
Ya zuwa yanzu, ko da yake ana iya samun kasashe 28 da suka kafa tashoshin binciken kimiyya 53 a nahiyar iyakacin duniya na kudu, amma yawancinsu sun kasance kamar a wajen nahiyar, sai dai kasashe 6 ciki har da Amurka da Rasha da kuma Japan sun kafa tashoshin bincike a yankunan da ke cikin nahiyar. Li Haiqing, kakakin hukumar kula da harkokin teku ta kasar Sin ta bayyana cewa, tashar bincike da kasar Sin za ta kafa ba da jimawa ba tana wuri mafi tsayi da ake kirar "A" a yankin karkara na nahiyar iyakacin duniya na kudu, wanda za ta kasance tashar binciken kimiyya da ke layin latitude na koli a duniya. Kuma ya kara da cewa,

"Tashar bincike da kasarmu za ta kafa a yankin da ke cikin nahiyar iyakacin duniya na kudu yana kan digiri 80 bisa layin latitude na kudu da kuma digiri 77 bisa layin longitude na gabas. Tsayinta daga leburin teku zai kai mita 4087. Kuma wurin da take ciki ya kai kilomita 7.3 da ke kudu maso yammacin wuri mafi tsayi da ake kirar 'A' a yankin kankara na nahiyar."

Kuma an labarta cewa, fadin wannan tashar bincike da ake kira Kunlun ya zarce murabba'in mita 500, kuma za a samar da kayayyakin samar da wutar lantarki da daidaita ruwa da zirga-zirga da kuma sadarwa bayan da aka kammala aikin kafa tashar domin biyan bukatun masu gudanar da binciken kimiyya 24 a fannin zaman rayuwa da kuma aiki.

Li Yuansheng, shugaban ofishin kula da kogin kankara na cibiyar nazarin iyakacin duniya ta kasar Sin shi ne shugaba mai kula da kankara na kungiyar binciken iyakacin duniya na kudu a wannan karo. Kuma ya gaya wa wakilinmu cewa, domin dace da yanayi mai matukar sanyi a yankin da ke cikin iyakacin duniya na kudu, za a yi amfani da bakin karfe na musamman wajen gina tashar Kunlun. Kuma ya ce,

"Ana iya samun kankara mai kauri mita 100 a kan nahiyar iyakacin duniya na kudu, kuma bisa bayanin da tashar binciken yanayi ta ruwaito mana, an ce, yawan sanyi na wurin yana iya kaiwa digiri 82 kasa da sifiri, shi ya sa dole ne a tabbatar da cewa, za a iya yin amfani da kayayyakin gine-gine a digiri 90 kasa da sifiri."

A hakika dai, kafin wannan, kasar Sin ta riga ta kafa tashar Babbar Ganuwa da tashar Zhongshan a wajen nahiyar iyakacin duniya na kudu a shekara ta 1985 da shekara ta 1989 bi da bi. Kuma bayan kafuwar tashar Babbar Ganuwa, kasar Sin ta kan gudanar da harkokin binciken nahiyar a ko wace shekara. Ta haka, kasar Sin ta samu manyan nasarori a fannonin binciken yanayin nahiyar da kankara da halittun da ke iya rayuwa a cikin yanayi mai matukar sanyi da harkokin teku, musamman ma a fannin nazarin duwatsu daga sararin samaniya a nahiyar, kasar Sin ta riga ta kama kasashen Amurka da Japan da ke nuna gwaninta wajen binciken iyakacin duniya da kuma kai matsayin gaba a duniya.

Qu Tanzhou, mataimakin shugaban ofishin binciken iyakacin duniya na hukumar kula da harkokin teku ta kasar Sin ya bayyana cewa, bisa shirin da aka tsara, za a kammala aikin gina tashar Kunlun a karshen watan Janairu na shekara mai zuwa, wanda zai shaida cewa, kasar Sin ta samu babban ci gaba a fannin shiga cikin muhimmin yankin da ke cikin nahiyar iyakacin duniya na kudu daga wajen nahiyar. Kuma ya kara da cewa,

"Wannan tasha da za a kafa tasha ce da ke iya gudanar da aiki a lokacin zafi kawai a maimakon a ko yaushe. Shi ya sa ake bukatar inganta ayyukan ajiyar makamashi da kayayyaki da ba da tabbaci da agaji da kuma sufuri. Muna sa ran alheri kan cewa, tashar za ta iya aiki a lokacin hunturu cikin dogon lokaci bayan shekaru 5 zuwa 10."