Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-23 15:59:08    
Bayani kan yadda wani dan kabilar Mongoliya ke yaki da ciwon sankara

cri
A ranar 17 ga watan Yuni na shekarar 2006, an yi wani taron amsa tambayoyi kan takardar shaidar digiri na uku a jami'ar Mongoliya ta gida ta kasar Sin. A wajen taron, akwai wani kwararre maras dogo dan kabilar Mongoliya wanda ke karanta takardarsa da babbar murya. Wannan mutum shi ne Jin Hai, wanda ke fama da ciwon sankara mai tsanani. A gun taron, Jin Hai ya amsa tambayoyin da kwararru suka yi masa da kyau ba tare da wani kuskure ba. A matsayin wani mutum wanda ke fama da ciwon sankara, Jin Hai ya nuna karfin zuciya wajen kammala rubutun takardar shaidar digiri ta uku, wanda kuma ya sami babban yabo daga takwarorin aikinsa. Jin Hai ya bayyana cewa:

"Mahalarta taron sun yi mini ban tafi. A ganina, da wuya gare ni wajen yaki da ciwon sankara. A wajen taron, na mikawa malamina furanni, domin nuna masa godiyata."

Jin Hai, wani mutum wanda ke da karfin zuciya sosai. A cikin tsawon shekaru 10 da yake fama da ciwon sankara, an yiwa Jin Hai tiyata har sau 7, amma bai taba yin watsi da aikin nazari da na malanta ba, ya yi iyakacin kokarinsa wajen yaki da ciwon sankara mai tsanani, wanda ke sadaukar da ransa ga aikin malanta.

A watan Afrilu na shekarar 2008, an yiwa hantar Jin Hai tiyata, wadda ya kasance karo na 8 da aka yi masa tiyata, inda Jin Hai ya ce:

"Ita wata karamar tiyata ce gare ni idan aka kwatanta ta da sauran tiyata da aka yi mini. Na warke tun da wuri."

Masu saurare, bayan da aka yiwa Jin Hai tiyata har sau da dama, an cire kwayar idonsa ta dama, kuma ya yi amfani da wata na'urar dake taimaka masa wajen sauraro. Amma a cikin wadannan shekaru 10, ya rika koyar da dalibansa a cikin aji, ba sau daya ba ba sau biyu ba ya fita waje domin gudanar da bincike, haka kuma, ya kammala rubutun kasidu da littattafan da yawan kalamansu ya kai miliyan 4.2.

Ko da yake Jin Hai ke fama da ciwon sankara mai tsananin gaske, amma hankalinsa a kwance yake. Yana fatan zai kara bayar da gudummowarsa a cikin wani kankanin lokaci, inda ya ce:

"Ina so in bayar da gudummowa cikin zaman rayuwata mai kurewa."

A shekaru 10 ko fiye da suka gabata, Jin Hai ya riga ya zama wani matashi kwararre mai fada-a-ji a fannin nazarin tarihi a jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta. Yayin da yake gudanar da aikinsa yadda ya kamata, an shaida masa cewa ya kamu da wani irin mummunan ciwon sankara da ya shafi hanci. Lokacin da Jin Hai ya gamu da wannan labari, ya yi mamaki sosai. Jin Hai ya ce:

"Wannan lamari ya ba ni mamaki kwarai da gaske saboda akwai wata babbar masifa wadda ta afka mini. A lokacin, ina so in yi watsi da duk abin da nake yi, ciki har da neman samun digiri na uku, da aikin malanta."

A shekarar 1999, bayan da aka yiwa Jin Hai babbar tiyata a karo na farko, Jin Hai ya gano mummunar surarsa daga cikin madubi. Tiyatar da aka yi masa ba ma kawai ta sauya surarsa ba, har ma ta sauya tsarin halittar hancinsa da bakinsa. A wancan lokaci, ya kusan gaza wajen yin magana, amma abun da ya fi bakanta masa rai shi ne kada ya sake komawa dandalin koyar da dalibai. A lokacin da yake yaki da ciwon sankara, Jin Hai ya dinga inganta kwarewarsa har ya iya magana a karshe! Sa'annan kuma Jin Hai ya sake komawa aji domin cigaba dukufa ka'in da na'in kan aikin malanta, inda ya bayyana cewa:

"Ya kamata ka nuna hazaka wajen yaki da ciwo, kar ka ji tsoro! Dalili daban da ya sa na iya cimma galaba kan ciwon sankara shi ne, akwai mutane da dama a kewayena, wadanda suka ba ni kwarin-gwiwa, da kara mini kuzari wajen cigaba da aiki."

Sakamakon nazarin da ya gudana da dimbin nasarorin da ya samu, Jin Hai ya karo ilimi sosai har kullum ana kiranshi "Mai Sanin Kome". A lokacin da yake tabo magana kan yadda ya yi girma, Jin Hai ya ce, an haife shi a wani yankin karkara na kiwon dabbobi na birnin Erdos na jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta. Bayan da ya gama karatunsa a makarantar sakandare, ya taba kiwon awaki a garinsa, da zama malamin koyarwa a makaranta, inda ya bayyana cewa:

"Sharadin zaman rayuwarmu ba shi da kyau. Balaga a yankin kiwon dabbobi wata babbar dukiya ce gare ni wajen bunkasa zaman rayuwata da karo ilimi."

Jin Hai ya cigaba da cewa, gudanar da nazari kan tarihin Mongoliya ba ma kawai sha'awarsa ba ce, har ma ya kasance baban nauyin dake rataye a wuyan kwararru. Lokacin da yake karatu a jami'a, Jin Hai ya gano cewa, akasarin sanannun littattafan dake shafar tarihin Mongoliya, mutanen kasashen yammacin duniya suka wallafa su, musamman ma Japanawa suna kan gaba a duniya wajen nazarin tarihin Mongoliya, amma kiri da muzu ne hukumar kasar Japan ta yi sauye-sauye ga littattafan koyarwa kan tarihi, wannan lamari ya burge shi kwarai da gaske. Sabili da haka Jin Hai ya kuduri aniyar nazarin tarihin Mongoliya, ta yadda Sinawa za su iya taka muhimmiyar rawa a fannin nazarin tarihin duniya.