Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-18 08:50:46    
Ana yin kokarin shigar da wasan damben mata cikin gasar wasannin Olympic

cri

A halin da ake ciki yanzu, wasan damben mata bai samu shiga gasar wasannin Olympic ba tukuna, amma a cikin 'yan shekarun da suka shige, wasan damben mata na duniya ya sami ci gaba cikin sauri kuma yadda ya kamata, a kullum 'yan wasa mata na wasan dambe suna fatan za su sami iznin shiga gasar wasannin Olympic, wato shiga gasar wasannin Olympic burinsu ne. Ko yaushe za su cimma burinsu? A cikin shirinmu na yau, bari mu yi muku bayani kan wannan.

Daga ran 21 zuwa ran 29 ga watan Nuwamba na shekarar 2008, an yi gasar cin kofin duniya ta karo na 5 ta wasan damben mata na duniya a birnin Ningbo na gabashin kasar Sin. 'Yan wasa sama da 200 da suka zo daga kasashe da shiyyoyi 43 sun yi kara cikin gasannin aji 13. A yayin gasar, shugaban hadaddiyar kungiyar wasan damben duniya kuma mamban kwamitin wasannin Olympic na duniya da ya zo daga birnin Taipei na Taiwan Wu Jingguo ya gaya mana cewa, wannan gasa ta sami babban sakamako, matsayin wasan damben matan duniya ya dinga dagawa cikin sauri, haka zai taimaka wa wasan damben mata da ya shiga gasar wasannin Olympic. Wu Jingguo ya ce,  "Tun bayan da aka shirya karo na farko na gasar cin kofin duniya ta wasan damben mata na duniya a shekarar 2001, kawo yanzu, shekaru 7 sun wuce, yanzu dai, ana shirya karo na 5, kuma ana yin kokarin neman samun goyon baya daga wajen kwamitin wasannin Olympic na duniya. Bayan gasar, za mu gabatar da rokon shigar da wasan damben mata a cikin gasar wasannin Olympic ga kwamitin wasannin Olympic na duniya, muna fatan sakamakon da muka samu a yayin wannan gasa zai zama mai amfani."

Yanzu dai, an kawo karshen gasar wasannin Olympic ta Beijing ba da dadewa ba, shi ya sa hadaddiyar kungiyar wasan damben duniya ta kyautata tunani cewa, wannan gasar cin kofin duniya ta wasan damben mata na duniya ta nuna wa kwamitin wasannin Olympic na duniya matsayi da sakamako na wasan damben mata na duniya, wato za ta ba da babban amfani kan batu game da shigar da wasan damben mata a cikin gasar wasannin Olympic ta London a shekarar 2012. To, idan ana son shigar da wasan damben mata a cikin gasar wasannin Olympic, wadanne ayyuka za su fi muhimmanci? Game da wannan, shugaban hadaddiyar kungiyar wasan damben Asiya daga kasar Sin Chang Jianping ya yi mana bayani cewa,  "Abu mafi muhimmanci shi ne matsayin wasa, in matsayin wasa ya kai koli, to, zai kara jawo hankalin 'yan kallo; na biyu shi ne aikin lafiyar jiki wato ba za a kawo hadari ga jikin 'yan wasa, musamman ga 'yan wasa mata ba; na uku, aikin alkalan wasa da aikin masu shirya gasa da sauransu su ma suna da mihimmanci."

Bayan da aka shirya gasanni na kwanaki 9 a yayin gasar, gaba daya kwararrun mutane kan wasan dambe sun amince da ci gaban da 'yan wasan damben mata na duniya suka samu sosai da sosai. Ban da wannan kuma, abu mafi faranta ran mutane shi ne ba wadda ta ji rauni a yayin gasar.

A halin da ake ciki yanzu, ya kasance da sabani tsakanin kasashen duniya kan wasan damben mata. Wasu suna nuna damuwar cewa, wasan zai kawo hadari ga jikin 'yan wasa mata. Kan wannan batu, shugabar kwamitin 'yan wasa mata na hadaddiyar kungiyar wasan damben duniya Joe Bowen ta bayyana cewa, kwamitin kula da lafiya na hadaddiyar kungiyar wasan damben duniya ya riga ya ba da muhimmanci matuka kan aikin kare jikin 'yan wasa. Alal misali, ana yin kokarin gabatar da kayayyakin kare jiki kamarsu safar hannu da kwalkwali na 'yan wasan dambe, a waje daya kuma, yayin da ake tanada ka'idar gasa, ana mai da hankali kan lafiyar jikin 'yan wasa. Joe Bowen ta bayyana cewa,  "Wasan dambe ba wasa ne mai nuna karfi fiye da yadda ya kamata ba, kana iya samun amsa daga fuskokin 'yan wasan dambe mata, ba rauni ko kadan a kan fuskokinsu, wasan dambe ya yi daidai da sauran wasanni, shi ma ba zai kawo hadari ga jikin 'yan wasa ba."

Game da aikin alkalin wasan dambe, shi ma yana jawo hankulan mutane sosai a duniya. Bayan da Wu Jingguo ya hau kan kujerar shugaban hadaddiyar kungiyar wasan damben duniya, ya yi manya gyare-gyare kan wannan, wanda ya fi muhimmanci a cikinsu shi ne hana aikin hukunci na rashin adalci a cikin gasar dambe. Ya ce, "Da, ana tsammani cewa, a cikin gasar dambe, alkalan wasa su kan yi hukunci kamar yadda suke so. Bayan na fara aiki, na yi gyare-gyare saboda na kyautata tunani cewa, adalci ya fi muhimmanci. Yanzu dai, mun kafa wani kwamitin yin gyare-gyare kuma mun gayyaci wasu kwararrun mutanen da abin ya shafa, mun yi tattaunawa sosai da sosai, muna fatan za mu kawar da dukkan kuskuren da muka yi fama da su a da."

Masu sauraro, kamar yadda kuka sani, yanzu ana kayyade yawan 'yan wasa da wasanni da lambobin zinariya na gasar wasannin Olympic, wato 'yan wasa ba za su zarce dubu 15 ba, wasanni ba za su zarce 28 ba, kuma lambobin zinariya ba za su zarce 302 ba. A sanadiyar haka, kwamitin 'yan wasa mata na hadaddiyar kungiyar wasan damben duniya ya tsai da cewa, za a rage yawan ajin wasan damben mata daga 13 zuwa 11, haka kuma za a rage yawan 'yan wasan damben mata da za su shiga gasar wasannin Olympic.

A watan Agusta na wannan shekara wato shekarar 2009, kwamitin wasannin Olympic na duniya zai yi taro a birnin Vopenhagen na kasar Denmark inda za a jefa kuri'a kan wani batu game da wasannin da za su shiga gasar wasannin Olympic ta London ta shekarar 2012. Wu Jingguo, mamban kwamitin wasannin Olympic na duniya yana ganin cewa, kila wasan damben mata zai shiga gasar wasannin Olympic ta London. Ko shakka babu, wannan shi ma fata ne na dukkan 'yan wasan dambe mata da malamai masu horaswa da sauran mutanen da abin ya shafa.

Malami mai horaswa dake jogorancin kungiyar 'yan wasan kasar Canada a yayin wannan gasar cin kofin duniya ta wasan damben matan duniya Hank Summer ya bayyana cewa,  "A kasarmu wato Canada, fitattun 'yan wasan damben mata suna da yawan gaske. Dukkanmu muna fatan cewa, za mu samu iznin shiga gasar wasannin Olympic ta London a shekarar 2012. Na san shugaba Wu Jingguo yana yin kokari domin wannan, mun hakkake cewa, za mu cimma burinmu, bari mu je London tare a shekarar 2012. Ya zuwa wancen lokaci, kasashe da shiyyoyi za su kara aika 'yan wasa domin shiga gasar damben mata. Bari mu sa ido mu gani"(Jamila Zhou)