Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-16 22:17:08    
"Kwalliya ta biya kudin sabulu" wajen bunkasa jihar Tibet ta kasar Sin

cri

Bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, an samu muhimmin cigaba da manyan sauye-sauye a jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin. Aikin gona da harkokin kiwon dabbobi na jihar sun samu bunkasuwa kwarai da gaske, zaman rayuwar jama'a kuma ya rika samun kyautatuwa.

"Babban kamfanin "Da Re Wa" namu yana da rassa guda 8, zuwa shekarar 2007, yawan kadarorin da kamfaninmu ya samu ya zarce kudin Sin Yuan miliyan 500. Lallai wannan babbar dukiya ce gare mu wadda ba'a taba ganin irinta ba a tsohon zamani a Tibet."

Masu saurare, muryar da kuka saurara murya ce ta wani dan kabilar Tibet mai suna Qunpei Ciren, wanda ya fito daga wani iyalin bayi manoma mai fama da kangin talauci a gundumar Renbu ta jihar Tibet. Sakamakon gyare-gyare ta hanyar dimokuradiyya da aka fara aiwatarwa a shekarar 1959 a jihar Tibet, Qunpei Ciren wanda yake da kuruciyarsa ya dasa aya ga halin kaka-naka-yi da yake ciki na bautawa iyayen gijin bayi wajen kiwon dawaki. Daga baya a shekarar 1982, Qunpei Ciren ya kafa wata kungiyar magina mai suna "Da Re Wa". Ta nuna hazaka har na tsawon shekaru 20 ko fiye, "Da Re Wa" ta tashi daga wata karamar kungiya har zuwa wani hamshakin kamfanin da ba na gwamnati ba a Tibet, Qunpei Ciren shi kansa kuma ya zama shahararren manomi mai masana'antu.

Masu saurare, a jihar Tibet mai cin gashin kanta, akwai 'yan kabilar Tibet da dama wadanda zaman rayuwarsu ya kyautatu kwarai da gaske bayan da aka soma aiwatar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje. A wurin dake da tazarar kamar kilomita da dama da babban birnin Lhasa na jihar Tibet, akwai wani kauye mai suna "Zang Re" wanda kullum ake kiransa "Kauyen Madara". Ba Sang, wata manoma mai shekaru 40 da haihuwa da 'yan kai, uwargida mafi girma ce a kauyen Zang Re wajen kiwon shanu. Ba Sang ta ce, a halin yanzu, sha'anin kiwon shanu ya kasance ginshiki wajen kara samun kudin riba, inda ta ce: "Ina kiwon shanu da yawansu ya kai 35, yawan madarar da na kan samu a kowace rana ya zarce kilogiram dari 2. Akwai masu sayar da kindirmo gami da masu aikin kimiyya da fasaha guda 11, baya ga kudin da mu kan yi amfani da shi wajen biyan albashin ma'aikata da sayen abincin shanu, yawan kudin ribar da na kan samu a kowace shekara ya zarce Yuan dubu 70, zaman rayuwarmu yana kara kyautatuwa."

A cikin shekarun 1980 na karnin da ya gabata, kamar sauran iyalan dake zaune a yankunan noma na jihar Tibet, Ba Sang, wadda ta yi aikin gona shekara da shekaru ta iya biyan bukatun cikin gidanta na yau da kullum ta hanyar kiwon wasu shanu na wurin. A shekarar 1994, Ba Sang ta sayar da shanunsa na wurin, ta kuma bukaci samun kudin rance daga wajen gwamnati, sa'annan ta sayi kyawawan shanu guda 6 daga babban yankin kasar Sin, daga baya Ba Sang ta fara gudanar da harkokin cinikinta na sayar da man shanu da madara. Daga shekarar 2003, Ba Sang ta kafa dakin harhada kindirmo na farko a kauyen "Zang Re". A halin yanzu, Ba Sang tana zaune a cikin wani gini mai benaye biyu da fadinsa ya zarce murabba'in kilomita dari 4, ciki har da kayayyakin masarufi iri-iri, da shannu da raguna da yawa, gami da isasshen abinci.

Akasarin kudin da Ba Sang ta yi amfani da shi wajen bunkasa harkokin ciniki na sayar da man shanu da madara, rance ne da gwamnatin wurin ta bayar. A cikin kauyen "Bai Ding" na garin Cai Gong Tang na gundumar Chengguan ta birnin Lhasa, mazaunin kauyen Caidan Pingcuo ya ce, gwamnati tana daukar matakai na nuna gatanci domin taimakawa manoma da makiyaya wajen yin amfani da injunan zamani wajen gudanar da aikin huda, wato ta zuba kudin da yawansa ya kai kashi 80 bisa dari, sauran kashi 20 bisa dari manoma da makiyaya suka tattara, inda Caidan Pingcuo ya ce: "Yanzu kusan kowane iyali na kauyenmu yana amfani da injunan aikin gona na zamani, wadanda suka kawo sauki ga aikin huda da samar da karin hasti, ta yadda yawan kudin shiga da za mu samu zai iya karuwa ainun. A halin yanzu, matsakaicin kudin shiga da na kan samu a kowace shekara ya zarce Yuan dubu 30, wanda ya ninka har sau 3 idan aka kwatanta shi da na shekarun baya."

Masu saurare, a halin yanzu, injunan aikin gona na zamani suna maye gurbin hanyoyin gargajiya da aka bi wajen gudanar da aikin huda a filin noma. Mataimakin darektan ofishin hukumar kula da aikin gona da kiwon dabbobi ta jihar Tibet mai cin gashin kanta, Mista Lin Mu ya bayyana cewa, a cikin shekaru 5 da suka gabata, jihar Tibet ta yi amfani da kudaden da yawansu ya zarce Yuan biliyan guda, a wani kokarin bada tallafi wajen raya ayyukan musamman na aikin gona da kiwon dabbobi da adadinsu ya kai 173, inda Mista Lin Mu ya ce: "An fara samun yankin raya aikin gona da kiwon dabbobi a jihar Tibet. Haka kuma, mun kafa wani tsarin bunkasa aikin gona da harkokin kiwon dabbobi wanda ke dacewa da hakikanin halin da kasarmu ke ciki. A halin yanzu, yin namijin kokari wajen daukaka cigaban aikin gona mai sigar musamman, ya zama ra'ayi guda da aka cimmawa tsakanin hukumomi a matsayi daban-daban da dimbin manoma da makiyaya."

Masu saurare, bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare, tattalin arzikin jihar Tibet ya sami bunkasuwa kwarai da gaske, yawan kudin shiga da mazauna birane da garuruwan jihar suka samu ya yi ta karuwa, zaman rayuwar mutanen jihar ya kyautatu kwarai da gaske. Bisa kididdigar da hukumar kididdiga ta jihar Tibet ta bayar, an ce, a shekarar 2007, matsakaicin kudin da mazauna birane da garuruwan jihar suka samu ya kai Yuan 11131, wanda ya karu da Yuan 10566 idan aka kwatanta shi da na shekarar 1978.

Mataimakin shugaban sashen nazarin tattalin arzikin kauyuka na cibiyar nazarin ilimin zaman al'umma ta jihar Tibet, Duo Qing ya ce, harkokin da ba na aikin gona ba na jihar su ma suna bunkasa cikin sauri, ciki har da sha'anin yawon shakatawa, da zirga-zirga da dai sauransu, inda Duo Qing ya bayyana cewa: "Sakamakon manufofin da kasar Sin take aiwatarwa na bada kwarin-gwiwa ga manoma da makiyaya da su gudanar da harkokin cinikayya, ra'ayinsu na yin kasuwanci ya sami ingantuwa. Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, a shekarar 2008, yawan mutanen da suka gudanar da harkokin masana'antu da kasuwanci a wurare daban-daban na jihar Tibet ya kai dubu 170."

Duo Qing ya cigaba da cewa, al'ummar jihar Tibet wadanda suka maida hankalinsu kan samun isasshen abinci da kayan sutura a lokacin da, a halin yanzu hankalinsu ya karkata kan gyaruwar zaman rayuwarsu na yau da kullum. Yawan kudin da mutane suke kashewa ta fannin aikin jinya da kiyaye lafiyar jiki ya yi ta karuwa.

A cikin wadannan shekaru 30, sha'anin kiwon lafiya na jihar Tibet ya habaka kwarai da gaske, tsarin bada tabbaci ga samun aikin jinya ya kusan kafuwa a duk fadin jihar. Zuwa yanzu, akwai hukumomin aikin jinya guda 7127 a jihar, kamar yadda shugaban sashen kula da harkokin kiwon lafiya na kananan hukumomi da mata da yara kanana na hukumar kiwon lafiya ta jihar Tibet Mista Wang Jianpeng ya ce: "A shekarar 2007, matsakaicin kudin da mazauna yankunan noma da kiwon dabbobi na jihar Tibet suka tattara ya kai Yuan 110, ciki har da matsakaicin kudin da yawansa ya kai Yuan 85 da gwamnatin tsakiyar kasar Sin ta zuba. Zuwa yanzu, kusan dukkan manoma da makiyaya a jihar Tibet suna jin dadin tsarin bada tabbaci ga samun aikin jinya da kiwon lafiya."