Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-15 19:55:24    
Kasar Sin za ta yi kokari domin raya dangantakar zumunci da hadin gwiwa a tsakaninta da Tanzania zuwa sabon mataki

cri

Ran 15 ga wata, shugaba Hu Jintao na kasar Sin da ke yin ziyara a kasar Tanzania ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Jakaya Kikwete.

A yayin shawarwarin, shugaba Hu ya nuna cewa, kasar Sin tana son inganta tuntubar juna da taimakawa juna a tsakaninta da kasashen Afirka da suka hada da Tanzania, za ta yi iyakacin kokari domin sassauta illar da matsalar hada-hadar kudi ta duniya take kawo wa bangarorin 2 wajen samun ci gaba. Sa'an nan kuma, kasar Sin za ta cika alkawarinta, ko kadan ba za ta rage taimakon da take bai wa Afirka ba. Ban da wannan kuma, za ta kalubalanci kasashen duniya da su cika alkawarin da suka yi wajen taimakawa kasashen Afirka yadda ya kamata.

A nasa bangaren kuma, Mr. Kikwete ya ce, Tanzania ta mayar da kasar Sin tamkar abokiya ce mai girma kuma mafi kyau a gare ta. Kasarsa za ta ci gaba da kyautata zumunci a tsakaninta da kasar Sin. Nasarar da kasar Sin ta samu ya karfafa aniyar kasashen Afirka ta bin hanyarsu ta fitar da kansu daga talauci da kuma samun bunkasuwa. Ya kuma jaddada cewa, har kullum Tanzania tana bin manufar 'kasar Sin daya tak a duniya'.(Tasallah)