Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-13 20:36:52    
Tarihin Jackie Chan

cri
Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun Ishaq Abdullahi Dan Rimi Bena, wanda a cikin wasikarsa ya ce, "Don Allah, ku ba ni tarihin Jackie Chan, ina sunansa na yanka?" To, a gaskiya, ban da Ishaq Abdullahi, sauran masu sauraronmu sun taba aiko mana wasiku, don neman bayani a kan Jackie Chan, shahararren tauraron fim na kasar Sin, wanda kuma ya shaida cewa, Jackie Chan na samun farin jini daga masu sha'awar fina-finansa a kasashe daban daban, ciki kuwa har da kasashen Afirka.

An haifi Jackie Chan a Hongkong a ran 7 ga watan Afril na shekarar 1954. Iyayensa, Charles Chan da Lee-lee Chan sun rada masa sunan Chan Kong-sang, wato sunansa na yanka, wanda ke da ma'anar "an haife shi a Hongkong". Lokacin da aka haife shi, Jackie na da nauyin pound 12, shi ya sa ba yadda za a yi sai a yi wa mahaifiyarsa tiyata.

A lokacin da yake karami, mahaifinsa ya kan tashe shi da sassafe, kuma tare za su yi wasan Kung fu. Sabo da a ganin mahaifinsa, wasan Kungfu na iya taimakawa wajen raya halayensa da kuma koya masa hakuri da karfi da kuma bajimta.

A lokacin da yake da shekaru 7 da haihuwa, mahaifinsa, Charles Chan ya kama aikin kuku da ofishin jakadancin Amurka a Australia, amma yana ganin cewa, ya fi kyau Jackie ya koyi wani abu a Hongkong, shi ya sa ya bar shi a Hongkong, don ya shiga kwalejin koyon wasan kwaikwayon kasar Sin, inda Jackie ya yi shekaru 10 yana koyon wasan Kungfu da kundumbala da waka da kuma wasan kwaikwayo.

A lokacin da yake da shekaru 17 da haihuwa, Jackie ya gama karatu a kwalejin koyon wasan kwaikwayo ta kasar Sin. Amma a lokacin, wasannin kwaikwayo na kasar Sin ba su samu karbuwa sosai ba, shi ya sa Jackie da abokan karatunsa sun sha wahalar samun aikin yi, sai dai kawai suka kama ayyukan kwadago da kasada. A lokacin, Hongkong na fitar da dimbin fina-finai a kowace shekara, kuma kullum ana bukatar samari masu aikin kasada, ga shi kuma Jackie ya kasance mutum mai kuzari da karfi da kuma hikima, shi ya sa ba da jimawa ba sai ya yi suna sabo da rashin tsoronsa a wajen ayyukan kasada.

Daga bisani, Jackie ya yi shekaru da dama yana aikin kasada. Amma ayyukan fina-finai sun fara tabarbarewa a Hongkong, shi ya sa ba yadda zai yi sai ya kaura zuwa Australia domin zama tare da iyayensa. A lokacin da yake Australia, Jackie ya taba aiki cikin wani dakin cin abinci da kuma wurin gine-gine, kuma a can wurin ne ya sami sunan "Jackie". Wani ma'aikacin wurin ya sa masa wannan suna sabo da bai iya fada ainihin sunansa, wato "Kong-sang" sosai ba, kuma ya fara kiransa da "little Jack", wanda daga baya ya zama "Jackie".

Amma Jackie bai yi farin ciki ba a Australia. Ayyukan gine-gine na da wahala, kuma halin bai kyautata ba sai bayan da wani mutum mai suna Willie Chan ya buga masa waya. Willie Chan yana ayyukan fina-finai a Hongkong, kuma a lokacin, yana neman wani da ya taka rawa cikin wani fim da wani shahararren darektan fim na Hongkong ke yi. Ayyukan kasada da Jackie ya taba yi sun burge Willie sosai. Ba da jimawa ba, Jackie ya kama hanyar komawa Hongkong. Amma duk da haka, fina-finan da Jackie ya yi ba su sami nasara sosai ba, kuma dalili shi ne Jackie bai yi amfani da basirar da Allah ya ba shi yadda ya kamata ba. Har zuwa lokacin da ya nuna ra'ayoyinsa cikin fina-finai, wato hada abubuwa masu ban dariya a cikin fina-finai na Kungfu, sai ya zama wani babban tauraron fim. Fim mai taken "Snake in Eagle's Shadow" ya zama babbar nasara ta farko da ya samu, daga baya, akwai "Drunken Master" da "Fearless Hyena", wadanda dukansu suka sami farin jini sosai, wadanda kuma suka sa Jackie ya samu karbuwa sosai a nahiyar Asiya. Amma duk da nasarorin da ya samu a Asiya, Jackie bai yi fice sosai ba a farkon zuwansa a Hollywood. Shi ya sa ya bar Amurka, kuma ya mai da hankalinsa a kan yin fina-finai a Hongkong. Bayan kimanin shekaru 10, Jackie ya sake zuwa Hollywood, inda ya fitar da fim mai suna "Rumble in the Bronx", wanda ya tabbatar da matsayinsa a zukatan masu kallon fim na Amurka. Daga baya, Rush Hour da Shanghai Noon dukansu sun saka Jackie cikin jerin sunayen taurari na Hollywood.

Ban da fina-finai, a cikin 'yan shekarun baya, Jackie yana ta kara mai da hankali a kan harkokin jin dadin al'umma. Ya kasance jakadan UNICEF da kuma UNAIDS, kuma ya yi lokuta da yawa yana tare da yara da kuma wadanda ke bukatar taimakon sauran jama'a.

Jackie ya auri Lin Feng Jiao a shekarar 1982, kuma suna da da namiji, wato Jaycee Chan, wanda ya kasance dan wasan kwaikwayo kuma mawaki.(Lubabatu)