Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-11 16:34:05    
Amfanin da Vitamin D ke bayarwa ga lafiyar jiki ya fi wanda ake tsammani yanzu

cri
Bisa sakamakon nazarin da masu ilmin kimiyya na kasar Amurka suka bayar a kwanan nan, an ce, ba kawai Vitamin D na iya sa kaimi ga girman kasusuwan dan Adam ba, har ma yana da nasaba da lafiyar duk jikin dan Adam.

Anthony Northmen, mai ilmin halitta na reshen Riverside na jami'ar California ta kasar Amurka ya bayar da wani rahoto a kan mujallar ilmin abubuwan gina jiki cikin asibitoci ta kasar Amurka, cewar amfanin da Vitamin D ke bayarwa ga lafiyar jikin dan Adam ya fi wanda ake tsammani yanzu, wato ba kawai yana iya ba da taimako wajen girman kasusuwan dan Adam da kuma shawo kan ciwon sanyin kashi ba, a'a har ma yana da nasaba da lafiyar kayayyakin jiki 36 ciki har da hanji da ciki da koda da huhu da tushen mafitsawar maniji da yanar ido da dai sauransu.

Mr. Northmen ya riga ya gudanar da nazari kan Vitamin D har na tsawon shekaru 45. Kuma ya bayyana cewa, nazarin da aka gudanar kafin wannan ya shaida cewa, karancin Vitamin D zai iya haddasa ciwon sanyin kashi na yara da ciwon sauye-sauyen halitta na duk jiki, da gaza girma, da ciwon kashi da ake kiransa Osteoporosis na baligai da dai sauransu, amma sabon nazari ya gano cewa, karancin Vitamin D yana da nasaba da barkewar wasu cututtukan sankara, kamar sankarar hanji da ta mafitsara da ta mama da dai sauransu, sabo da haka dole ne a samu isasshen Vitamin D in ana son kiyaye lafiyar jiki.

Yaya za a iya samun Vitamin D? To, masu sauraro, yanzu sai ku shakata kadan, daga baya kuma za mu ci gaba da yi muku bayani kan amfanin Vitamin D ga lafiyar jiki.

Mr. Northmen ya nuna cewa, shan hasken rana wata muhimmiyar hanya ce ga jikin dan Adam wajen samun Vitamin D. Amma sabo da yanzu dimbin mutane suna zaune a cikin biranen da aka fi samun manyan gine-gine a ciki, da kuma zaune cikin dakuna na dogon lokaci, shi ya sa ba safai su kan iya samun isasshen lokaci wajen shan hasken rana ba, ta haka dimbin mutane suna da karancin Vitamin D sosai.

Kuma Mr. Northmen ya ba da shawarar cewa, ya kamata baligai su samu Vitamin D a kalla IU2000 a ko wace rana. Amma bisa ma'aunin da cibiyar nazarin kiwon lafiya ta kasar Amurka ta bayar kan samun Vitamin D, an ce, ya kamata yawan Vitamin D da mutanen da shekarunsu ba su kai 50 da haihuwa ba su samu a ko wace rana kar ya kasa IU 200, yayin da ya kamata wannan jimla ta kai IU 400 ga mutanen da shekarunsu suke a tsakanin 51 da 70 da haihuwa, haka kuma kamata ya yi wannan jimla ta kai IU 600 ga wadanda shekarunsu suka zarce 70 da haihuwa. Ban da wannan kuma Mr. Northmen ya ce, idan ba a iya samun isasshen hasken rana ba, to jimlolin Vitamin D da aka ba da shawarar samunsu ba su isa sosai ba. Sabo da haka yana ganin cewa, wajibi ne a gyara ma'aunin samun Vitamin D.

Sabili da haka, Mr. Northmen ya kuma ba da shawarar cewa, hanyar samun Vitamin D ita ce kara cin abincin da ke kunshe da vitamin D da yawa, ciki har da shan magungunan ba da kariya ga lafiya da ke kunshe da vitamin D. Ban da wannan kuma ya nuna cewa, hanta da nono da kuma kwayayen tuntsaye suna kunshe da vitamin D da yawa, haka kuma an fi samun yawansa a cikin man kifi.