Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-10 15:55:34    
Bunkasuwar maganin gargajiya na Tibet

cri
Ana samun kayayyakin da ake yin amfani da su don yin maganin gargajiya na Tibet a yankunan da tsawonsu ya fi tsawon lebur din teku da mita sama da 3800. Bisa kididdigar da aka yi an ce, a tudun Qinghai-Tibet na kasar Sin akwai tsire-tsire kala kala fiye da 2000, da dabbobi daban daban kamar 160, da kuma ma'adinai nau'o'i 80 da wani abu, wadanda ake iya yin amfani da su don yin maganin gargajiya na Tibet. Gaskiya ne wadannan sinadira suna da yawa bisa na maganin gargajiya na sauran al'umma na duniya.

A shekaru fiye da dubu da suka wuce, a kan hada maganin gargajiya na Tibet ta hanyar yin amfani da hannu, wato ana samar da magani kamar gari. Amma, da kyar ake iya shan magani kamar haka. Yanzu, kamfanin maganin gargajiya na Tibet yana amfani da fasahar zamani, don sarrafa maganin na kwayoyi, da na ruwa, da dai sauransu, ta yadda za a sanya maganin gargajiya na Tibet ya kara ba da amfani wajen kwantar ciwace-ciwace.

Kwanan baya, kamfanin maganin gargajiya na Tibet na jihar mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Tibet ya gudanar da wani aikin ba da misali na sana'ar sabbin fasahohi na zamani kan maganin gargajiya na Tibet. Shugaban kamfanin Mr. KungaNorbu ya gabatar da cewa,

"An zuba kudin da yawansu ya wuce RMB miliyan 98 kan wannan aiki, ciki kuma gwamnatin kasarmu ta bayar da kudin taimako na miliyan 10. A cikin wannan aiki, an shigar da fasahohi na zamani, haka kuma maganin gargajiya na Tibet zai kara samun karfin yin takara."

An ce, domin ingiza bunkasuwar maganin gargajiya na Tibet, a shekaru fiye da goma da suka wuce, gwamnatin jihar Tibet ta tsaida kudurin karfafa aikin sarrafa maganin gargajiya na Tibet, daga baya kuma ta mayar da wannan aiki a matsayin daya daga cikin muhimman ginshikin masana'antu na musamman na wurin. A waje daya kuma, gwamnatin jihar Tibet, da kamfanin maganin gargajiya na Tibet, da kuma kwalejin nazarin fasaha ta jihar, da dai sauransu sun kara ayyukan nazari da shuke-shuke kan kayayyakin da ake yi amfani da su wajen hada maganin gargajiya na Tibet. Tsohun shugaban hukumar kula da harkokin kimiyya da fasaha ta jihar Tibet Mr. TsedimGyaco ya bayyana cewa,

"Tun daga shekarar 2006 har zuwa shekarar 2010, gwamnatin wurin na shirya tsara ma'auni na kasa kan kayayyakin maganin gargajiya na Tibet har guda 200. A waje daya kuma, tun daga shekarar 2005, an soma ayyukan shuka maganin gargajiya na Tibet da aka jefa su cikin hadari, haka kuma an aza harsashe ga bunkasuwar sana'ar maganin gargajiya na Tibet."

Wani jami'in kwamitin kula da aikin gyare-gyare na jihar Tibet Mr Yang Qian ya ce, ko da yaushe jihar na mayar da hankali sosai kan sana'ar maganin gargajiya na Tibet.

"Ya kamata mu kai matsayin gaba a duniya kan aikin maganin gargajiya na Tibet, za mu cigaba da karfafa ra'yin kirkire-kirkire, kana kuma za mu cigaba da nuna goyon baya kan wannan aiki ta hanyar tsara manufofi."