Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-10 15:34:32    
Shiyyar yin ciniki ba tare da shinge ba ta Lekki ta Nijeriya na fuskantar sabon masomi da kuma sabon zarafi

cri
A yayin taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka da aka yi a shekarar 2006, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi alkawarin cewa, kasar Sin za ta kafa shiyyoyi 3 zuwa 5 na yin ciniki ba tare da shinge ba a kasashen Afirka, ta haka kasashen Afirka za su iya more fasahohin da kasar Sin ta samu a fannin raya tattalin arziki. Shiyyar yin ciniki ba tare da shinge ba ta Lekki da ke tsibirin Lekki a kudu maso yammacin kasar Nijeriya ita ce daya daga cikin irin wadannan shiyyoyin ciniki. Yanzu shiyyar Lekki tana bin hanyar samun saurin bunkasuwa. To, ga wani bayanin musamman da wakilinmu ya ruwaito mana daga Nijeriya.

A kwanan baya, tawagar ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta kai rangadin aiki a shiyyar Lekki, inda Lv Jijian, shugaban tawagar kuma mataimakin daraktan ofishin yin hadin gwiwa da ketare a fannonin tattalin arziki da ciniki na ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya taba kai wa shiyyar Lekki ziyara a watan Satumba na shekarar bara. Bayan watanni 3, sanye-sauyen da wannan shiyya ta samu sun ba shi mamaki sosai. Ya ce,"A kan gudanar da ayyuka da yawa wajen kafa shiyyar yin ciniki ba tare da shinge ba. Amma a ganina, a cikin watanni kasa da 3, a shiyyar Lekki, an sami ci gaba kamar haka, a zahiri, an sami sauri sosai. Yanzu muna kafa shiyyar kawai, muna raya ababen al'umma, kamar shimfida hanyoyi da gudanar da ayyukan samar da ruwa da wutar lantarki."

Shiyyar ciniki ta Lekki ita ce daya daga cikin sabbin shiyyoyi mafi saurin ci gaba da aka kafa a biranen Nijeriya. Kamfanin CCECC na kasar Sin ya yi shekaru da dama yana yin ciniki a Nijeriya, inda kuma ya kulla aminci mai danko tare da rukunoni daban daban na wurin. Chen Xiaoxing, mataimakin babban manajan kamfanin ya ambaci manufar kamfanin na nan gaba da cewar,"Za mu yi shekaru 2 da kuma kudin Sin yuan biliyan 2 wajen raya shiyyar Lekki ta mataki na farko mai fadin murabba'in kilomita 7.5, za mu kuma zaunar da masana'antu da dama."

Bangaren Nijeriya kuwa yana fatan shiyyar Lekki za ta kasance tamkar muhimmin bangare na yankin da ke kewayen birnin Lagos. Adeyemo Thompson, mataimakin babban manajan kamfanin raya shiyyar Lekki a bangaren Nijeriya yana fatan shiyyar Lekki za ta zama babban birni kamar yadda birnin Beijing yake kasancewa. Mr. Thompson ya ce,"A shiyyarmu, akwai masana'antun kerawa da man fetur da iskar gas da manyan masana'antu. Za mu kuma kafa gidajen kwana. A matsayinta na wani bangare na yankin da ke kewayen Lagos, shiyyar Lekki tana kan muhimmin matsayi. Mun taba ziyarar shiyyoyin kasar Sin na raya tattalin arziki, shi ya sa muke ganin cewa, yin koyi da kasar Sin zabi ne mafi kyau wajen raya shiyyar ciniki ba tare da shinge ba. Muna fatan kasar Sin za ta iya taimake mu domin raya shiyyar Lekki zuwa babban birnin kamar Beijing."

Kafa shiyyar yin ciniki ba tare da shinge ba a ketare, sabon gwaji ne da masana'antun kasar Sin suka yi, musammam ma a lokacin yanzu da matsalar hada-hadar kudi ta addabar duk duniya, irin wannan shiyya ta gamu da matsalar zaunar da masana'antu.

Amma duk da haka, Mr. Lv Jijian ya nuna cewa, kasar Sin na da aniyar gudanar da raya shiyyoyin yin ciniki ba tare da shinge ba a kasahen Afirka yadda ya kamata.

Baya ga shiyyar Lekki a Nijeriya, kasar Sin tana kafa shiyyar yin ciniki ba tare da shinge ba a kasar Zambia da sauran kasashen Afirka. An labarta cewa, domin sa kaimi kan gudanar da ayyukan kafa shiyyar yin ciniki ba tare da shinge ba a kasashen Afirka, gwamnatin Sin za ta fito da jerin manufofin ba da fifiko. An yi imani cewa, a sakamakon bullowar sabbin manufofi, shiyyoyin yin ciniki ba tare da shinge ba da kasar Sin za ta kafa a kasashen Afirka za su fuskanci makoma mai kyau.(Tasallah)