Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-06 20:52:48    
Takaitaccen bayani kan kasar Saudiyya

cri

Saudiyya tana kudu maso yammacin nahiyar Asiya a zirin Larabawa, a gabas ta yi makwabtaka da yankin Gulf, kuma a yamma ta yi makwabtaka da tekun Bahar Maliya, ta yi iyaka da kasashen Jordan da Iraqi da Kuwait da Hadaddiyar Daular Larabawa da Oman da Yemen da dai sauransu. Fadin kasar ya kai murabba'in kilomita miliyan 2.25, yawan jama'ar da take da shi ya kai kimanin miliyan 25.57, kuma kashi 30 cikin kashi 100 na jama'ar kasar, sun fito ne daga kasashen waje. Harshen Larabci harshe ne na gudanar da ayyuka a kasar, kuma ana iya yin magana da Turanci a dukkan fadin kasar. Saudiyya wata kasa ce da take bin addinin musulunci, kashi 85 daga cikin kashi 100 na jama'ar kasar 'yan Sunni ne, yayin da sauran kuma 'yan Shiah. Ma'anar Saudiyya a harshen Larabci ita ce "kwararowar hamada mai cike da alheri". Yankin hamada ya mamaye rabin fadin kasar.

Yawan mutanen da ke cikin birnin Riyadh watau hedkwatar kasar ya kai kimanin miliyan 4, matsakaicin yanayi na birnin ya kai Centigrade 25.

Sarki Abdullah bin Abdul-Aziz ya hau karagar mulki a ranar 1 ga watan Agusta na shekarar 2005.

Saudiyya ta shahara a duniya ne sabo da wadataccen man fetur da take da shi, kuma yawan adanannen man fetur da take da shi da yawan man fetur da take fitarwa na sahun gaba a duniya, a shekarar 2006. yawan man fetur da za a iya hakowa a kasar, ya kai Ton biliyan 3.63, kuma ya kai kashi 26 cikin kashi 100 na yawan man fetur da duk duniya ke da shi. Yawan iskar gas da take adanawa ya kai Cubic mita biliyan 6900, kuma yana matsayi na 4 a duniya. Haka kuma, Saudiyya na da ma'adinai kamarsu zinariya da bakin karfe da karfe da gwangwani da sanholo da kwano da dai sauransu.

Sin da Saudiyya na da dankon zumunci tsakaninsu. A karni na 7 bayan haihuwar Annabin Isa, Annabi Mohamed da magoya bayansa sun ketare teku, kuma sun yada addinin Musulunci a kasar Sin. A karni na 15, shahararren matukin jirgin ruwa Zheng He ya taba kai ziyara a kasar Saudi Arabia. A ranar 21 ga watan Yuli na shekarar 1990, Saudiyya ta kulla dangantakar diplomasiyya tare da kasar Sin, bayan da aka kafa dangantakar diplomasiyya tsakaninsu, dangantakar sada zumunci ta hada kai tsakaninsu ta karfafa daga dukkan fannoni. A watan Janairu na shekarar 2006, sarki Abdullah Bin Abdul-Aziz ya kawo rangadin aiki a kasar Sin, inda bangarorin biyu suka daddale yarjejeniyar hadin gwiwa kan makamashi tsakaninsu. A watan Afrilu na shekarar 2006, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya kai ziyara a kasar Saudiyya, inda ya bayar da muhimmin jawabin da ke da lakabi "Sa kaimi ga kawo zaman lafiya ga yankin gabas ta tsakiya da gina duniya mai jituwa" a gun shawarwari kan kasar Saudiyya. A watan Yuli na shekarar 2008, mataimakin shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara kasar a hukunce. Tun bayan kafa huldar diplomasiyya tsakaninsu, dangantakar hadin gwiwa ta sada zumunci ta kara zurfafa tsakaninsu, bangarori biyu sun kara hada kai a fannoni da dama. A shekarar 2007, yawan cinikayya ta bangarorin biyu tsakaninsu ya zarce dalar Amurka biliyan 25.3 kuma idan aka kwatanta da makamancin lokaci na shekarar 2006 ya karu da kashi 26 cikin kashi 100.(Bako)