Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-06 18:54:06    
Bayani game da kasar Mauritius

cri

Fadin kasar Mauritius ya kai muraba'in kilomita dubu 2 da arba'in. Ita wata kasa ce dake kan tsibirai da yawa a kudu maso yammacin tekun Indiya. Muhimmin tsibiri na kasar Mauritius mai tazara kilomita dari 8 daga gabashin kasar Madagascar. Sauran tsibirai sun hada da tsibirin Rodrigues da Agalega da Cargados Carajos. Kuma tsawon gabar teku na kasar ya kai kilomita 217.

Yawan mutane na kasar Mauritius ya kai miliyan 1 da dubu 400. Yawancin mazauna na kasar mutane ne masu asalin Indiya da Pakistan da yawansu ya kai kashi 67 cikin dari. Harshen gwamnatin kasar shi ne turanci, amma yawancin mutane suna yin amfani da harshen Indiya da na Creole da na Faransanci. Mazauna kimanin kashi 51 cikin dari suna bin addinin Hindu, da kuma kashi 31.3 cikin dari na wadanda suke bin addinin Kirista, da kashi 16.6 cikin dari da suke bin addinin Islama, ban da wannan kuma, wasu mutane suna bin addinin Buddha.

Babban birnin kasar shi ne Port Louis wanda ya kafu ne a shekarar 1735. Yana arewa maso yammacin gabar teku ta tsibirin Mauritius. Ba kawai shi ne cibiyar siyasa da al'adu da tattalin arziki ta kasar ba, hatta ma shi ne tashar teku mafi girma ta kasar. Yawan kayayyakin shigi da fici da ake yin safararsu ta tashar a kowce shekara yana kaiwa ton miliyan 3 ko fiye. Kuma yawan mutane na wannan birni ya kai dubu 144 a shekarar 2004.

Shugaban kasar Mauritius shi ne Anerood Jugnauth, ya hau kan kujerar mulki a ran 7 ga watan Oktoba na shekarar 2003. Kuma firayim ministan kasar Mauritius Navin Chandra Ramgoolam ya kama aiki ne a watan Yuli na shekarar 2005.

Kasar Mauritius tana bin manufar tsaka-tsaki, da ta ba ruwanmu a fannin harkokin waje, ta bude kofa ga kasashen waje a duk fannoni. A ran 15 ga watan Afrilu na shekarar 1972, kasar Mauritius da Sin sun kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu. (Asabe)