Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-06 18:36:58    
Takaitaccen bayani kan hukumar hadin kan kasashen Larabawa dake kewayen mashigin tekun Pasha

cri

Hukumar hadin kan kasashen Larabawa da ke kewayen mashigin tekun Pasha ta GCC, wadda ke da hedikwatar a birnin Riyad, na Saudiyya, an kafa ta ne a watan Mayu na shekarar 1981. Membobi kasashen hukumar sun hada da kasar Saudiyya, da hadaddiyar daular Larabawa, da Oman, da Bahrein, da Qatar, da kuma Kuwait. Fadin kasashen hukumar a gaba daya ya kai kilomita miliyan 2.67, kuma yawan jama'a ya kai kimanin miliyan 35, shi ya sa hukumar ta kasance wata kungiyar shiyya-shiyya mai muhimmanci a yankin gabas ta tsakiya.

Duk wadannan membobi kasashe 6 na hukumar GCC na da tsarin siyasa da na tattalin arziki kusan iri daya, sa'an nan suna da moriya daya a fannonin siyasa, da tattalin arziki, da harkokin waje, da aikin soja, da dai makamantansu. Makasudin kafa hukumar GCC shi ne, daidaita hadin gwiwa a tsakanin membobi kasashe, da kara hada su a waje daya, da inganta mu'amala a tsakanin jama'ar kasashen, da raya masana'antu, da aikin gona, da kimiyya da fasaha, da kafa cibiyoyin binciken kimiyya, da kuma karfafa hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da cinikayya tsakanin kamfanoni masu zaman kansu.

Hukumar hadin kan kasashen Larabawa da ke kewayen mashigin tekun Pasha ta GCC ta kunshi majalisar koli, da majalisar monistoci, da babbar sakateriya. Majalisar koli ta kunshi shugabannin membobi kasashen hukumar, ta kuma kasance majalisa mai ikon koli ta hukumar. Shugabannin kasashen 6 na daukar nauyin shugabantar majalisar a matakin karba karba, kuma a zagayen kowa ne wa'adi ana yin shekara daya. Majalisar ministoci ta kunshi ministocin harkokin waje na kasashen 6, yayin da babbar sakateriya take da babban sakatare daya, da sauran mataimakansa 3 masu kula da ayyukan siyasa, da kudi, da kuma soja. Babban sakataren hukumar, majalisar koli ita ce ke nada shi, kuma yana da wa'adin aiki na shekaru 3. Babban sakataren hukumar na yanzu shi ne Abdurrahman al-Attiyah.

Ko wane watan Nuwamba ko na Disamba, hukumar GCC ta kan yi taron koli a daya daga cikin hedikwatocin membobi kasashen 6. Taron karon da ya wuce da aka yi shi a watan Disamba na shekarar 2008, an yi ne a Muscat, hedikwatar kasar Oman. Ministocin membobi kasashen hukumar GCC masu kula da harkokin waje, da aikin tsaron kasa, da harkokin gida, da aikin hakar mai, da kudi, da dai sauransu, su ma su kan kira taro bisa agenda ko kuma bisa bukatun da ake da su, inda su kan yi kokarin neman samun ra'ayi daya kan wasu manyan ayyukan da suka shafi siyasa, da tattalin arziki, da soja, da harkokin waje, ta yadda za a iya aiwatar da aiki bisa hadin kai.

Membobi kasashe 6 na hukumar GCC na da albarkatun danyun mai masu dambin yawa, inda yawan ajiyayyun man da aka gano ya kai kimanin kashi 45 % na dukkan albarkatun mai da Allah ya hore wa dan Adam. Cikin shekarun baya, kasashen 6 sun yi amfani da albarkatun mai da suke da shi don raya tattalin arziki, sun kuma dauki jerin matakai don neman dinke kasahen a waje daya, musamman a fannin tattalin arziki. A ranar 1 ga watan Janairu na shekarar 2003, membobi kasashen hukumar GCC sun kafa wani kawancen tara haraji, inda aka kayyade cewa, za a tara haraji daya na kashi 5% kan dukkan kayayyakin da aka shigar da su daga kasashen da ke wajen hukumar GCC, yayin da a tsakanin membobi kasashen hukumar za a yi kokarin kawar da kariyar haraji. Ran 1 ga watan Janairu na shekarar 2008, kasashen 6 sun sanar da kafuwar kasuwar gama-gari ta mashigin tekun Pasha. A watan Disamba na shekarar 2008, a wajen taron koli na hukumar GCC na karon 29 da aka yi shi a Muscat, Oman, an zartar da yarjejeniyar kawancen kudi, da kundin catar kwamitin kudi. Wadannan takardun sun share fage ga kafa baitulmalin mashigin tekun Pasha a nan gaba. Haka kuma, hukumar GCC na kokarin neman samun takardun kudi na kanta a shekarar 2010.

Dangantakar da ke tsakanin hukumar GCC da kasar Sin na samun bunkasuwa lami lafiya. A watan Yuli na shekarar 2004, Abdurrahman al-Attiyah, babban sakataren hukumar GCC ya shugabanci wata tawagar da ke kunshi da ministocin kudi na membobi kasashen hukumar don kawo ziyara zuwa kasar Sin, inda gwamnatin kasar Sin da hukumar GCC suka cimma yarjejeniyoyin hadin gwiwa kan tattalin arziki, da cinikayya, da aikin zuba jari, da kuma yin musanyar fasahohi, haka kuma sun fara shawarwai kan kafa wani yankin cinikayya mara shinge. Bisa yarjejeniyoyin, kasar Sin da hukumar GCC sun kafa hadadden kwamiti mai kula da hadin kai a fannin tattalin arziki da cinikayya, inda bangarorin 2 suka gabatar da wani tsari na musayar ra'ayi kan aikin raya tattalin arziki. Har ila yau kuma, yarjejeniyoyin sun karfafa wa bangarorin 2 kwarin gwiwa kan hada karfi a fannonin tattalin arziki, da cinikayya, da zuba jari, da binciken fasaha, da tantance hanyar da za a bi don habaka cinikayya, da kara zuba wa juna jari, da kara kai wa juna ziyara, da dai sauransu. (Bello Wang)