Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-03 16:43:05    
Masanin batun Afirka na kasar Sin ya hangi makomar kungiyar AU

cri

Daga ranar 1 ga watan Faburairu zuwa ranar 3, shugabanni da wakilai na membobi kasashe 53 na kungiyar gamayyar Afirka ta AU, sun hallarci taron kolin kungiyar, mai taken 'gina kayan more rayuwa a Afirka', wanda aka yi a Addis Ababa, hediwatar kasar Habasha, inda suka tattauna kan yadda za a raya aikin gina kayan more rayuwa da ya shafi sufuri, da makamashi, da kuma aikin zuba jari, haka kuma, sun yi bitar tasirin rikicin hada-hadar kudi kan Afirka, da hanyar da za a bi don tinkarar matsalar.

Dangane da taron, wakilinmu ya yi hira da Xu Weizhong, darektan sashen Afirka na cibiyar nazarin dangantakar kasa da kasa ta kasar Sin, inda Mista Xu ya yi tsokaci ga kuduri niyyar dakatar da kafa hadaddiyar gwamnati ta Afirka da membobi kasashen kungiyar AU suka yi, ya ce, kafa wata hadaddiyar gwamnati ta nahiyar buri ne na shugabannin kasashen Afirka na zuriyoyi. Yana kuma da wajibci, ta la'akari da aikin raya nahiyar Afirka na yanzu da na nan gaba, amma ba cikin kwanaki daya ko biyu za a cimma burin ba.

"Da farko dai, tun lokacin da mazan jiya na nahiyar Afirka suke kokarin neman 'yancin kan al'ummominsu, sun riga sun mai da aikin kafa hadaddiyar gwamnati ta nahiya ya zama babban burinsu. Na biyu, kawo yanzu bayan da aka samu rikicin hada-hadar kudi, musamman ma, cikin shekarun baya da ake kokarin ganin dinkuwar kasashen duniya a waje daya a fannin tattalin arziki, shugabannin Afirka sun fara ganin bukatar hada karfin kasashen nahiyar don raya kansu. Shi ya sa aka riga aka kafa majalisar dokoki ta nahiyar Afirka, kuma tuni har an fara la'akari kan kafa hadaddiyar gwamnati. Na uku, ana kara samun hadin gwiwa a tsakanin shiyyoyi da kasashen da ke nahiyar Afirka, shi ya sa ana bukatar wata hukuma kamar hadaddiyar gwamnati da za ta iya daidaita aikin. Duk da cewa ya kasance da butaka, amma ba za a samu cimma burin cikin sauri ba, sai dai a bi matakin sannu a hankali."

Game da rikicin hada-hadar kudi da ke addabar duniya, Mista Xu ya nuna cewa,

'Ba nan take ne za a iya ganin tasirin rikicin hada-hadar kudi kan nahiyar Afirka ba, amma a nan gaba ka iya samun mummunan tasiri a wasu fannoni. Da farko, faduwar farashin dayun kayayyaki za ta haifar da faduwa kan tattalin arzikin kasashen Afirka. Na biyu, jin radadin rikicin hada-hadar kudi, zai sa kasashe masu arzikin masana'antu su yi rangwame kan tallafin kudin da suka alkawarta baiwa kasashen Afirka, yadda zai haifar da tasiri mai muni kan wasu kasashen Afirka marasa cigaba, wadanda ke dogaro kan tallafin kudin.'

Duk da cewa, za a samu raguwar tallafin kudi, amma Mista Xu Weizhong na ganin cewa, kasahen Afirka za su iya yin amfani da wannan dama don kawar da dogaron da ake yi kan kasashen da suka cigaba a fannin masana'antu, ta yadda za a samu 'yancin kai a fannin tattalin arziki.

'Kalubale ka iya kawo sauyin yanayi. Tare da bunkasuwar tattalin arzikinsu, kasashen Afirka na kara samun kwarewar raya kansu. Sabo da famar da ake yi da rikicin hada-hadar kudi, kasashe masu cigaban masana'antu na shan aiki sosai, watakila ba za su samu damar tsoma baki cikin sha'anin kasashen Afirka, ko kuma yi musu katsalanda ba. Wannan zai ba kasashen Afirka damar zabar hanyoyin kansu don raya tattalin arziki. Wasunsu ka iya samun hanyoyin da suka dace da halayensu.'

An ce, cikin shekaru 10 masu zuwa, kasashen Afirka za su kasa kudin da yawansa ya kai dalar Amurka biliyan 250 don gina kayan more rayuwa, haka kuma, za a fi mai da hankali kan wasu fannoni kamarsu sufuri, da wutar lantarki, da ruwa, da sadarwa, da dai sauransu. Xu ya ce, wadannan manyan ayyukan da kasashen Afirka ke da shirin aiwatarwa, za su ba da taimako wajen tinkarar rikicin hada-hadar kudi da raya kasashen a nan gaba. (Bello Wang)