Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-28 15:36:55    
Fadar gargajiya ta kasar Sin

cri
A wannan mako, za mu amsa tambayar malam Salisu Muhammed Dawanau, daga Abuja, tarayyar Nijeriya. A cikin wasikar da ya aiko mana a kwanan baya, ya kawo mana wata tambaya, wato "Forbidden city, shin mene ne labarin wannan wuri?" Watakila da ma masu sauraronmu kun taba jin sunan "Forbidden City", amma ba ku san shi sosai ba, sabo da haka, a cikin shirinmu na yau, bari mu kawo muku labarinsa.

"Forbidden City", ko kuma "fadar gargajiya" da ake kira a yanzu, daidai take a cibiyar birnin Beijing. Ita fada ce ga sarakunan gargajiya na daulolin Ming da Qing a zamanin gargajiyar kasar Sin. Gaba daya sarakuna 24 ne suka taba zama a fadar da kuma tafiyar da harkokin mulki.

An kammala gina Fadar a shekarar 1420. Kasancewarta fada mai girma sosai, wadda fadinta ya kai muraba'in kilomita dubu 720, har ma ana daukarta a matsayin daya daga cikin fada masu girma guda biyar na duniya, wato sauran hudu su ne fadar Versailles ta Faransa da Buckingham ta Birtaniya da White House ta Amurka da kuma Kremlin ta kasar Rasha. A cikin fadar, da akwai dakuna sama da 9000, kuma ita ta kasance fadar gargajiya mafi girma da ake iya samu yanzu a kasar Sin, har ma a duniya baki daya. Fadar ta kasu kashi biyu, wato gaban fadar da kuma bayanta. Gaban fadar wuri ne da sarakuna ke gudanar da kasaitattun bukukuwa, a yayin da bayanta ya kasance wuri da sarakuna da matansu ke zama da kuma kulawa da harkokin mulki. Ban da wannan, akwai katangu wadanda tsayinsu ya kai mita goma kuma tsawonsu mita 3,400 ne a kewayen wannan babbar fada. A waje da wadannan katangu kuma, da akwai wani kogi mai fadin mita 52.

Gine-ginen fadar gargajiya ta kasar Sin sun zama abin al'ajabi a duniya, ban da wannan, kayayyakin da ke cikinta ma sun zama masu daraja wadanda ba safai a kan ga irinsu ba. A cikin fadar, akwai kayayyakin tarihi masu dimbin yawa, wadanda yawansu ya kai sama da miliyan 1, ciki har da kayayyakin zinari da na azurfa da na tagulla da zane-zane da dai sauran kayayyakin fasaha na tarihi. A ran 10 ga watan Oktoba na shekarar 1925, fadar ta zama gidan nune-nunen kayayyakin tarihi, wanda ya kasance mafi girma a kasar Sin. A halin yanzu dai, an kafa dakunan nune-nunen zane-zane da fadi-ka-mutu da kayayyakin tagulla da kayayyakin fasaha da kayayyaki masu daraja da agoguna da dai sauran kayayyakin tarihi a cikin fadar.

A shekarar 1987, kwamitin kula da kayayyakin tarihi na duniya a karkashin kungiyar UNESCO, wato kungiyar ilmi da kimiyya da al'adu ta MDD ta saka fadar gargajiya ta kasar Sin cikin jerin wuraren tarihi na duniya. (Lubabatu)