Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-27 19:55:48    
Kirkire-kirkire da kuma damar kasuwnci da aka samu daga bikin baje-koli na sadarwa na birnin Suzhou

cri
Ba kawai yankin kogin Yantse delta na kasar Sin da ya hada da birnin Shanghai da jihohin Jiangsu da Zhejiang yana daya daga cikin yankunan da aka fi samun ci gaban tattalin arziki a kasar Sin ba, har ma shi ne muhimmin sansani na sana'ar sadarwa ta kasar Sin. Domin ba da hidima ga bunkasuwar sana'ar fasahar samar da bayanai ta IT ta yankin, birnin Suzhou mai shekaru dubu daya da ke cibiyar yankin koyin Yantse delta ya fara shirya bikin baje-koli na sadarwa na Suzhou na kasar Sin a shekara ta 2002. Kuma bayan da aka raya shi har shekaru 6, ya zuwa yanzu bikin ya riga ya zama daya daga cikin bukukuwan sana'ar sadarwa da suka fi taka muhimmiyar rawa a kasar Sin. Bikin baje-koli na sadarwa na shekarar bana ya jawo hankalin masana'antun fasahar samar da bayanai ta IT da hukumomin da abin ya shafa fiye da 630 na gida da na waje, ta haka ya zama biki mafi girma bisa na lokacin da.

Dimbin sakamako masu kyau da aka samu daga wajen fasaha da kuma boyayyen karfin kasuwanci, bikin ya jawo hankalin 'yan kasuwa na kasa da kasa. Kuma Mr. Odd Lindahl da ya zo daga kasar Sweden wani dan kallo ne kuma wani dan kasuwa da ya nuna kayayyakin sadarwa a gun biki, kuma ya gaya wa wakilinmu cewa,

"bikin na da girma kwarai, wanda ya shiga cikin zuciyata sosai. Kuma ana iya samun dimbin sabbin ra'ayoyin kirkire-kirkire da kayayyaki a wurin, shi ya sa ina so in ci gaba da kallon kayayyakin da aka nuna a gun bikin."

Yayin da duniya ke fama da karancin makamashi da albarkatun kasa da kuma kara gurbatawa muhalli sakamakon kayayyakin sadarwa, ana mayar da "kimiyya da fasaha mai kiyaye muhalli" a matsayin babban taken wannan bikin baje-koli. A gaban dakalin nuna kayayyaki na wani kamfanin Beijing, na'urorin kwamfuta biyu da ke iya tsimin makamashi da kiyaye muhalli sun jawo hankalin mutane. An rage nauyin jikinsu sosai, har ma daya daga cikin wadannan na'urorin kwamfuta biyu ya yi kamar wani littafi. Zhao Gang, manaja mai kula da ayyukan sayarwa na kamfanin ya bayyana cewa, irin wannan kwamfuta da kamfaninsu ya kirkiro yana aiki da kwakwalwar kwamfuta a zamani a duniyar yau, wadda ba kawai an iya rage nauyin jikinta ba, a'a har ma an iya rage yawan makamashi da ake konewa. Kuma ya ce,

"na'urar sarrafa bayanai da irin wannan kwamfuta ke amfani da ita na'ura ce ta farko da ta fi karama wajen kiyaye muhalli a duniya, an daina yin amfani da sinadarin lead wajen kera muhimman kayayyakinta. Ban da wannan kuma, yawan makamashin da take konewa ya ragu da kashi 70 cikin dari in an kwatanta da sauran na'urorin sarrafa bayanai da ke cikin kwamfuta bisa mataki daya."

A cikin dakunan nuna kayayyaki, sabbin fasahohi iri daban daban sun kashe wa 'yan kallo kwarkwatar ido sosai. Amma a gun dandalin tattaunawa da abin ya shafa, an kara bayyana labaru kan bunkasuwar sana'ar IT. Kuma ta bikin baje-koli na sadarwa, mutane sun gano sauye-sauyen salon tattalin arziki na shiyya-shiyya da kuma girman sana'ar sadarwa ta kasar Sin. Kuma an labarta cewa, dalilin da ya sa aka shirya bikin a birnin Suzhou shi ne sabo da an gano babbar makomar bunkasuwar sana'ar sadarwa ta yankin kogin Yantse delta. Wang Rong, sakataren kwamitin Suzhou na JKS ya bayyana cewa,

"ya zuwa yanzu, sana'ar sabbin fasahohin zamani da aka mayar da sana'ar sadarwa a matsayin kashi mafi muhimmanci ta riga ta zama sabuwar sana'a mafi girma a Suzhou. Daga watan Janairu zuwa watan Satumba na shekarar bana, yawan kudaden da Suzhou ya samu daga sana'ar IT ya riga ya kai kimanin Yuan biliyan 521, wanda ya kai kashi 37.5 cikin dari bisa na dukkan yawan kudaden da birnin ya samu daga masana'antu."(Kande Gao)