Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-19 18:00:14    
Drolma, yarinya mai farin ciki kuma mai yin jagorancin masu yawon shakatawa

cri

Idan an tabo magana kan jihar Shangri-la, kila ka iya tunawa da tsaunukan da ke rufe da dusar kankara da tafkuna masu kayatarwa da ke filin ciyayi, nan ne wuri mai tsabta da ya jawo hankulan mutane. A hakika kuwa jihar Shangri-la hedkwatar gundumar Diqing ce ta kabilar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta da ke kudu maso yammacin kasar Sin, a can da akwai tsaunukan da ke rufe da dusar kankara, da tafkunan da ke faffadan tsauni, da kungurmin daji, ban da wannan kuma da akwai al'adun gargajiya na kabilar Tibet. Jama'a masu sauraro, cikin shirinmu na yau za mu kawo muka bayani game da Drolma, kyakkyawar yarinya 'yar kabilar Tibet wadda take dukufa kan aikin jagoranci ga masu yawon shakatawa a jihar Shangli-la.

A jihar shangli-la, akwai wani lambun shan iska na kasar Sin mai sunan Pudachu inda akwai koguna da koramu da tafkuna da filayen ciyayi da wurare masu danshi da kuma dabbobi da itatuwa masu daraja. A kowace rana, Drolma, kyakkyawar yarinya 'yar kabilar Tibet takan yi jagorancin masu yawon shakatawa da suka zo daga kasashe daban-daban domin gane ma idonsu yanayin halitta mai kyaun gani da ke wurin Pudachu. "Ya abokai masu yawon shakatawa, barkanku da safe! Ina maraba da zuwan ku lambun shan iska na kasar Sin mai sunan Pudachu don yin ziyara, ni ce mai gabatarwa ta sana'ar musamman ta lambun shan iska na Pudachu na kasar Sin, sunana kuma Drolma. Ina fatan da zuciya daya cewa za ku yi ziyara a wannan karo cikin murna da farin ciki, kuma ina fatan za ku ji dadi sabo da tsaunuka da ruwaye masu kyaun gani da ke cikin lambun Pudachu." A cikin harshen kabilar Tibet, kalmar "Drolma" mace ce da ba ta mutu ba. Yarinya Drolma mai shekaru 21 da haihuwa 'yar kabilar Tibet ce gaba da baya wadda aka haife ta a jihar Shangri-la, ba kawai ta iya waka da rawa ba, hatta ma ta iya magana da harshen kabilar Han sosai, idanunta sukan yi haske lokacin da take Magana. Lokacin da yarinya Drolma take yin jagorancin masu yawon shakatawa don shan iska a jihar Shangri-la mai kayatarwa, takan rera wakokin kabilar Tibet masu ratsa zuciya domin shere wa baki.

Yau da shekaru 2 ke nan Yarinya Drolma ta kammala kataru daga Kolejin koyon sana'ar yawon shakatawa ta Shangri-la, kuma ta zama wata mai yin jagorancin masu yawon shakatawa ta sana'ar musamman da ke lambun shan iska na Pudachu na kasar Sin, takan yi wa masu yawon shakatawa bayani a kowace rana kan wannan wuri mai kyaun gani da kuma bayyana musu al'adun gargajiya masu halayen musamman na kabilar Tibet, sabo da haka tana jin dadi sosai.

Domin samar da sharuda masu amfani ga aikinta, yarinya Drolma takan yi zama cikin lambun shan iska na Pudachu wanda yake da nisan kilomita 30 zuwa 40 a tsakaninsa da garin gundumar Shangri-la. Amma a duk lokutan da ba a samu masu yawon shakatawa da yawa ba, sai ta koma gidanta mai nisan kilomita 70 zuwa 80 daga garin gundumar don taimaka wa iyayenta wajen aikin noma. Ta ce, "Yanzu gidana yana da gonaki kusan kadada daya, iyayena suna shan wahalhalu da yawa, ina fatan mahaifina da mahaifiyata za su iya samun zaman jin dadi."

Saurayi Shen Xueshu, dan kabilar Yi wanda ya shafe shekaru 2 da wani abu yana aiki tare da yarinya Drolma, lokacin da ya tabo magana kan yarinyar, ya yi mata yabo cewa, "Drolma ta mai da hankali sosai kan aikinta, tana aiki cikin farin ciki a kowace rana, kuma ta jawo farin cikinta ga kowane bakin da suka zo nan domin yawon shakatawa."

Yarinya Drolma tana da wani kyakkyawan buri, wato tana fatan ganin mutane sai kara yawa suke za su kai ziyara jihar Shangri-la, kuma su yi yawo ciki lambun shan iska na Pudachu na kasar, da kuma ganin yadda jama'a suke zaman jin dadi a nan, daga baya kuma za su kai karimci da so da aminci da jama'ar jihar Shangri-la ke nuna musu zuwa wurare daban-daban na duniya.