Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-19 17:59:14    
Wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

---- Kwanan baya, an gama aikin gina mashigin ruwan kamun kifaye na farko cikin Hamadar kasar Sin wato mashigin ruwan kamun kifaye na Bositeng da ke tsakiyar hamadar Taklamakan ta jihar Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar.

Wakilinmu ya samu labari daga hukumar da abin ya shafa ta jihar Xinjiang ta kabilar Uigur mai ikon tafiyar da harkokin kanta cewa, jimlar fadin mashigin ruwan kamun kifaye na Bositeng ta kai murabba'in mita 7,000, yawan kudin da aka ware domin gina wannan mashin ruwa ya kai kudin Sin wato Yuan miliyan 6, kuma za a fara aiki da shi a nan gaba kadan. Bayan da aka gina wannan mashigin ruwan kamun kifaye, jiragen ruwan kamun kifeye da yawansu ya kai 150 wadanda za su iya zamewa a nan don a yi musu lodi da kuma sauke lodin kayayyakin amfani ruwa a sa'i daya.

Fadin ruwayen jihar Xinjiang ya kai kadada dubu 730, yawan nau'o'in kifaye na wananan jihar ya wuce 50, kuma yawancin samfurorinsu kifaye ne masu kyau. Nau'o'in kifaye 8 ciki har da kifi mai sunan Silver carp wadanda aka fi ba da karfi wajen fitar da su a Tafkin Bositeng inda mashigin ruwan kamun kifaye yake, wadanda kuma suka riga suka samu amincewa daga wajen babbar hukumar kiyaye muhalli ta kasar Sin, har suka zama amfanin ruwa masu shahara a jihar Xinjiang ta kasar.

---- Wakilinmu ya samu labari daga hukumar da abin ya shafa ta jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin cewa, yanzu jiragen sama suna iya tashi da sauka a filin jirgin sama na Kunga na birnin Lhasa a kowane lokaci, daga ran 12 ga watan Nuwamba an fara yin zirga-zirgar jiragen sama daga birnin Chengdu zuwa birnin Lhasa da dare, wannan ya sa aya ga tarihin rashin zirga-zirgar jiragen sama da dare cikin shekaru 43 da suka wuce a filin jirgin sama da ke faffadan tsaunin Lhasa.

Bisa labarin da aka bayar an ce, domin bude wannan hanyar zirga-zirgar jiragen sama da dare, filin jirgin sama na Kunga na birnin Lhasa ya ware kudin Sin wato Yuan miliyan 99 domin haskaka filin ta hanyar yin amfani da wutar lantarki, ta yadda aka samu tabbaci wajen ba da haske ga jiragen sama wadanda suka tashi da sauka da dare a wannan filin jirgin sama.

An labarta cewa, samfurin jiragen sama da ke zirga-zirga da dare a filin jirgin sama na Lhasa manyan jiragen saman fasinjoji ne wadanda suke dacewa da yanayin faffaden tsauni, yawan kudin tikitin jirgin saman fasinja na dare ya tashi daidai bisa na zaman yau da kullum.