Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-14 21:26:35    
Ya kamata a samu sabon sakamako wajen ayyukan yaki da cin hanci da rashawa a sabuwar shekara

cri
Tun daga ranar 12 zuwa ranar 14 ga wata, an shirya taron shekara-shekara na kwamitin duba dokokin biyayya na tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Taron ya nuna cewa, kara sa ido kan manyan jami'ai, da mayar da hankali kan warware matsalar cin hanci da rashawa da aka samu a fannonin ingancin abinci da magunguna, da kuma kwanciyar hankali wajen aikin samar da kayayyaki, da dai sauransu, su ne muhimman ayyuka a gaban jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wajen yaki da cin hanci da rashawa. Kwararru kan batun cin hanci da rashawa na kasar Sin na ganin cewa, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta dauki matakai a hakika kan ayyukan yaki da cin hanci da rashawa a sabuwar shekara, a waje daya kuma an jaddada da samun sabon sakamako wajen ayyukan. Lallai wadannan matakai sun bayyana babbar aniyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wajen ayyukan yaki da cin hanci da rashawa. To, masu sauraro, yanzu ga cikakken bayanin.

A gun taron, babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS, kuma shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya yi jawabi, inda ya tabbatar da sakamakon da aka samu a fannin yaki da cin hanci da rashawa a 'yan kwanakin da suka wuce, amma a sa'i daya kuma ya nuna cewa, har zuwa yanzu ana kasancewa da matsalar cin hanci da rashawa mai tsanani a wasu fannoni.

"A takaice dai, an fi samun tabbaci wajen hanyar sa ido kan ladabtar da jami'ai, da yaki da cin hanci da rashawa, an riga an samu cigaba wajen hana matsalar cin hanci da rashawa, kazalika jama'a na kara nuna gamsuwa kan wannan. Amma, a waje daya kuma, a kan samu wannan matsala cikin sauki a wasu hukumomi, har ma an haifar da sabon hali da sabbin matsaloli."

Bayan haka kuma, Mr. Hu Jintao ya jaddada cewa, dole ne a cigaba da kara sanya ido wajen ladabtar da jami'ai da yaki da cin hanci da rashawa, domin ba da tabbaci ga gyare-gyare, da bunkasuwa, da kuma dorewa.

A cikin sanarwar da aka bayar bayan taron, an tabbatar da aikin yaki da cin hanci da rashawa a shekarar 2009, ciki har da dora muhimmanci kan binciken laifufukan da jami'ai da 'yan kasuwa suka yi tare, da daidaita muhimman matsaloli dangane da ingancin abinci da tsaron ayyukan samarwa da kiyaye muhalin halittu da sa ido kan kudade da sauransu da jama'ar suka fi mai da hankula a kansu, da kara sa ido kan jami'ai, musamman ma manyan jami'ai, domin tabbatar da yin amfani da ikonsu yadda ya kamata, da dai sauransu.

Mr. He Zengke, kwararre a fannin yaki da cin hanci da rashawa na kasar Sin yana ganin cewa, ana kyautata zaton wadannan hakikanan matakai za su ingiza ayyukan cin hanci da rashawa na kasar Sin a shekarar 2009.

"Kamar misali, a cikin sanarwar, an gabatar da kara sa ido da yin bincike kan inganta bukatun gida, da sayen kayayyaki, wadannan su ne matsalolin da ke jawo hakulan jama'a sosai. Ban da wannan kuma, sanarwar ta jaddada cewa, ya kamata a samu sabbin sakamako, da samun amincewa daga wajen jama'a a lokacin da ake yaki da cin hanci da rashawa, wannan na nuna niyyar jam'iyyar kwminis ta kasar Sin, da alkawarin da ta dauka a fannin siyasa. Muna fata za mu iya samun sabon cigaba wajen wasu muhimman ayyukan gyare-gyare ta wannan dama mai kyau ta yaki da cin hanci da rashawa."

Bisa kididdigar da kwamitin duba dokokin biyayya na tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya yi an ce, tun daga watan Nuwamba na shekarar 2007 har zuwa watan Nuwamba na shekarar 2008, hukumomi na matakai daban daban masu kula da harkokin da'a sun yi hukunci kan mutane sama da dubu 150.

Mr. He Zengke ya ce, ya kamata kullum gwamnati na lura da sabon halin da ake ciki, kana kuma daidaita ayyukan cin hanci da rashawa masu dacewa.

"Yanzu, saurin bunkasuwar tattalin arziki ta duniya ya ragu, sakamakon haka, saurin bunkasuwar tattalin arziki ta kasar Sin shi ma ya ragu, saboda haka, gwamnati ta kara zuba jari don samun cigaban tattalin arziki, kila za a kara samun damar cin hanci da rashawa. Bayan haka kuma, bisa bunkasuwar fasahar zamani, an samu hanyoyi da yawa don fitar da kudi zuwa kasashen ketare, haka kuma jami'ai masu cin hanci za su samu hanyoyin tserewa zuwa waje."