Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-13 17:04:41    
Yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofa ga waje sun kawo wa kasar Sin gasannin duniya

cri
A shekarun baya, an shirya gasar wasannin Olympic da gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa da gasar fid da gwani ta tseren motoci ta F1 da gasar wasan kwallon kwando ta NBA da sauran gasanni mafiya ban sha'awa a nan kasar Sin daya bayan daya. Matsayin gasanni a fannonin shiryawa da kuma yin takara a tsakanin 'yan wasa sun sami babban yabo sosai. A cikin shekaru 30 da suka wuce, 'yan wasan kasar Sin sun sake shiga gasannin duniya, birnin Beijing ya sami nasarar shirya gasar wasannin Olympic a shekarar 2008, sa'an nan kuma, kasar Sin ta sami bakuncin dimbin gasannin da suke da babban tasiri a duk duniya. Don me kasar Sin ta sami saurin bunkasuwar wasannin motsa jiki haka? Kuma ina dalilin da ya sa kasar Sin ta sami damar shirya gasannin duniya da yawa? A cikin shirinmu na yau, za mu tono dalilin da ya sa hakan.

A shekarar bara, an yi gasar wasannin Olympic ta karo na 29 a nan Beijing, hedkwatar kasar Sin, inda 'yan wasa da masu horas da wasanni da jami'ai na sassa daban daban na duniya suka yi kwanaki 16 masu ban sha'awa suna haduwa a nan. Karfin Beijing na shirya gasa ya sami amincewa daga bangarori daban daban. Jacques Rogge, shugaban kwamitin wasan Olympic na duniya ya yaba wa ayyukan shirya gasar da Beijing ta yi, inda ya ce,"Kasashen duniya sun kara saninsu kan kasar Sin ta hanyar gasar wasannin Olympic a wannan karo, haka kuma, kasar Sin ta kara samun fahimta kan kasashen duniya. Wannan ita ce ainihin gasar wasannin Olympic mai kayatarwa da ba za a iya kwatanta saura da ita ba."

Shekarar 2008 shekara ce ta cikon shekaru 30 da kasar Sin ta fara yi gyare-gyare a gida da kuma bude kofarta ga waje. Shi ya sa shirya gasar wasanni mafi koli ta duniya a nan kasar Sin a daidai shekarar 2008 bai yi tamkar a ce "kai ya zo gora ta zo" ba. A lokacin da yake takaita gasar wasannin Olympic ta Beijing, shugaba Hu Jintao na kasar Sin yana ganin cewa,"Ingantaccen karfin wata kasa ya sa kaimi kan bunkasuwar wasanni. A sakamakon yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofa ga waje da ci gaba da raya kasar Sin ta zamani mai gurguzu, kasarmu ta sami babban ci gaba, ta shiga jerin manyan kasashen da suka nuna fifiko a wasanni."

A halin yanzu, a kan yi gasannin duniya masu matsayin koli a kasar Sin. Biranen Beijing da Shanghai da kuma Guangzhou da sauran biranen da ke nuna karfi da ci gaba sun ba da karin tasiri a dandalin wasannin motsa jiki na duniya a kwana a tashi. A zahiri, wadannan kungiyoyin wasannin duniya masu yawa haka suna son shirya gasanninsu mafiya shahara a kasar Sin ne a sakamakon babban ci gaban da kasar Sin ta samu bisa manufar yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofarta ga waje.

Da farko, dalilin da ya sa kasar Sin ta samu bakuncin muhimman gasannin duniya sau da yawa shi ne domin saurin bunkasuwar tattalin arzikinta. Tun daga shekarar 2006 zuwa shekarar 2008, hadaddiyar kungiyar wasan karta ta duniya wato WBF ta yi gasanni 3 na wasan karta masu matsayin koli na duniya a kasar Sin. Don me aka yi irin wannan gasa sau da dama a wata kasa? Richard Grenside, mashawarci a harkokin fasaha na kungiyar WBF ya yarda da cewa, muhimmin dalilin da ya sa kungiyar WBF ta tsai da wannan kuduri shi ne domin babban karfin kasar Sin a harkokin tattalin arziki. Ya ce,"Kasar Sin na daya daga cikin kasashe kadan da suka iya shirya manyan gasannin duniya. Alal misali, ana bukatar zuba makudan kudade kan shirya gasar wasannin kwakwalwa ta duniya da gasar fid da gwani ta wasan karta ta duniya. Wannan shi ne dalilin da ya sa muka shirya gasar fid da gwani ta wasan karta ta duniya a Shanghai sau 2, kuma a nan Beijing a shekarar bara. An cimma daidaito a wannan fanni cikin sauki."

Yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofa ga waje har na tsawon shekaru 30 sun kuma raya ababen wasanni sosai, filaye da dakunan wasa da yawa da kasar Sin ta gina sun kasance kan gaba a duk duniya. Wannan ya taimakawa kasar Sin wajen samun bakuncin gasannin duniya masu matsayin koli.

Kafin shekarar 1978, kasar Sin ba ta da filaye da dakunan wasa masu inganci. Xia Song, wani shahararren mai gudanar da harkokin wasanni ya waiwaya da cewa,"Akwai babban bambanci a wancan lokaci bisa na yanzu. A wancan lokaci, a kan mayar da babban dakin da ke da kujeru a ciki a matsayin dakin wasanni, inda ba a ba da kyakkyawan hidima ba, kuma ababen nishadi ba su da inganci. Amma yanzu mun sami babban ci gaba a fannin."

Filaye da dakunan wasa na "Shekar tsuntsu" da "Water Cube" da aka yi amfani da su a wajen gasar wasannin Olympic ta Beijing sun bawa kasashen duniya mamaki kwarai, suna matsayin kan gaba a tsakanin gine-ginen duniya a zamanin yanzu.

Yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofarta ga waje da kasar Sin take yi a cikin shekaru 30 da suka wuce sun kara wa jama'ar Sin kaifin hangen nesa. Mutanen Sin suna alla-alla wajen shirya gasannin duniya masu matsayin koli a yanzu bisa na da. Kafin kasar Sin ta yi gyare-gyare a gida da kuma bude kofarta ga waje, mutanen Sin ba su san gasannin da aka yi a sauran sassan duniya sosai ba. Amma bayan shekarar 1978, mutanen Sin sun kara saninsu kan kasashen waje. A shekaru 1980, gidan telibijin na kasar Sin wato CCTV ya fara watsa shirye-shirye kai tsaye kan gasar wasannin Olympic da gasar wasan kwallon kwando ta kasar Amurka wato NBA da kuma gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa da hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta duniya wato FIFA ta shirya a duk fadin kasar Sin. Nan take dimbin mutanen Sin suka fara kishin wadannan wasanni da gasanni. Kazalika kuma, shirya wadannan gasanni ya zama buri ne na jama'ar Sin, wadanda suke zura ido kan shirya wadannan gasanni. A shekarar 2004, gasar wasan kwallon kwando ta NBA ta shirya gasar share fage a nan kasar Sin a karo na farko. Dan wasan kwallon kwando Yao Ming na kasar Sin ya yi matukar farin ciki a wancan lokaci. Ya bayyana cewa,"Ina fatan a sakamakon shirya gasar share fage ta NBA a nan kasar Sin, kowa da kowa zai iya kasancewa cikin yanayin gasar wasan kwallon kwando, zai iya kara saninsa kan wasan kwallon kwando, ta yadda karin mutane za su iya shiga wannan wasa."

A cikin shekaru 30 da suka wuce, kasar Sin ta sami manyan nasarori a cikin wasannin cin gasa. A sakamakon kasancewa kan gaba da 'yan wasan kasar Sin ke kasancewa a gasanni da yawa, shi ya sa kungiyoyin wasanni na duniya masu yawa suka zabi kasar Sin domin shirya gasanninsu. Wang Dazhao, wani dan jarida kuma dattijo na kasar Sin ya gaya gama cewa,"Kasar Sin na ba da babban tasiri a wasanni da yawa a duk duniya, tana taka muhimmiyar rawa sosai a dandalin wasanni na duniya. Ta haka, in ba a shirya wasu gasanni a kasar Sin ba, to, za a kawo illa wajen yayata gasannin, shi ya sa kungiyoyin wasanni na duniya suka yi kokarin mamaye kasuwar kasar Sin da kuma neman samun karin 'yan kallo na kasar Sin, sa'an nan kuma, sun kawo wa kasar Sin damar ci gaban kasuwanci."

A lokacin da yake zantawa da wakilinmu, He Zhenliang, shugaba mai daraja na kwamitin wasan Olympic na kasar Sin kuma mamban kwamitin wasan Olympic na duniya ya bayyana cewa, ainihin dalilin da ya sa aka sami nasarar shirya jerin gasannin duniya masu matsayin koli a kasar Sin shi ne domin kasar Sin ta sami babban ci gaba a sakamakon yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofarta ga waje. Mr He ya ce,"Ainihin dalilin shi ne samun nasarar yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofar Sin ga waje. Inda babu wannan muhimmiyar manufa, to, ba mu iya samun bakuncin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing, balle ma babban yabo da kasashen duniya ke nuna mana kan gasar wasannin Olympic mai kayatarwa."(Tasallah)