Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-12 15:56:02    
Domin kirkiro kyakkyawar makoma ga Shangri-La

cri
Ko kuna sane da cewa, akwai wani kyakkyawan wuri a lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin wanda ya yi suna a duniya??Shangri-La. A cikin yaren kabilar Zang, "Shangri-La" na nufin "rana da wata a zuciya". Shangri-La, wadda kulllum ake kiranta "aljanna", tana janyo hankulan dubbun-dubatar masu yawon bude ido a duniya. A cikin 'yan shekarun nan, tare da habakar tattalin arzikinta ba tare da kakkautawa ba, Shangri-La ta riga ta kasance daya daga cikin ni'imtattun wurare a yankin kabilar Zang na kasar Sin.

A kowace rana, manomi Qilin Peichu, dan asalin Tibet, da mazauna kauyensa sukan hau dutse su shiga cikin gandun daji, nauyin dake bisa wuyansu shi ne kiyaye muhallin halittu wanda ke kunshe da aikin yin riga-kafin tashin gobara, da yaki da masu farautar dabbobi, da tsintar jakar leda da dai sauran abubuwa masu gurbata muhalli. Qilin Peichu da abokansa suna kokarin kiyaye gandun daji da suke zama, kuma yayin da suke yawo akan dutse, sukan rera waka irin ta kabilar Zang. Qilin Peichu ya ce:

"Mu kan tsinci abubuwa masu gurbata muhalli, da yin riga-kafin masu sare bishiyoyi da masu farautar dabbobi, a wani kokarin kiyaye muhallin halittu."

Qilin Peichu, mutum ne wanda ke zaune a kauyen Luorong cikin lambun shan iska na Pudacuo na gundumar Shangri-La. A wannan wuri, akwai kungurmin daji, da kwari, da tafki, da fadama, da dabbobi iri-iri da ba kasafai akan ga irinsu ba. Wurare mafi ni'ima a lambun shan iska na Pudacuo su ne Tafkin Shudu da Tafkin Bita, wadanda suke renon nagartattun 'yan asalin kabilar Zang. A kan tsibirin dake cibiyar Tafkin Bita, akwai wani wurin ibada na addinin Buddah, inda mabiya addinin Buddah na wurin sukan je domin yin ibada.

Amma, kafin shekara ta 1998, mazauna gundumar Shangri-La ba su fahimci irin muhimmanci na kiyaye muhallin hallitu ba, shi ya sa bala'u sukan afka musu lokaci-lokaci, ciki har da zabtarewar kasa, da gangarar baraguzan duwatsu tare da malalar laka, har ma mazauna Shangri-La suka yi fama da mummunan bala'in ambaliyar ruwa a shekarar 1996. Domin yaki da bala'u daga indallahi, da kiyaye muhallin halittu, gwamnatin Sin ta dauki kwararan matakai na haramta sare bishiyoyi fiye da kima, da mayar da gonaki da su zama gandun dazuzzuka, da shimfida ciyawa, da raya makamashin bola-jari da dai sauransu. Sakamakon matukar kokarin da ake yi har na tsawon shekaru 10 ko fiye, muhallin Shangri-La ya kyautatu kwarai da gaske.

Mataimakin babban manaja na kamfanin kula da harkokin lambun shan iska na Pudacuo na Shangri-La, Ding Wendong ya gabatar da cewa, domin kare muhallin halittu, gwamnatin wurin ta tsaurara matakan rushe matsugunai da gine-gine da aka gina a kewaye da Tafkin Shudu da na Bita ba bisa doka ba, ta yadda aka rage yawan abubuwan da suka gurbata muhalli da aka fitar zuwa tafkunan biyu. Haka kuma, gwamnatin wurin ta sayi manyan motoci guda 20 masu yin amfani da makamashi mai tsabta, domin kaiwa da dawowa da masu yawon shakatawa, a waje daya kuma, ta gina gidajen cin abinci masu yin amfani da makamashi daga hasken rana. Manaja Ding Wendong ya ce:

"Muna gudanar da ayyukanmu daidai bisa ka'idar kiyaye muhallin halittu. Yawan kudaden da muka zuba wajen raya muhimman ababe masu kiyaye muhalli ya kai Yuan miliyan 230."

A halin yanzu, ra'ayin kiyaye muhallin halittu ya riga ya shiga cikin zukatan mazauna gundumar Shangri-La. Mazauna Shangri-La suna ganin cewa, kiyaye muhallin wurin na iya kawata Shangri-La, ta yadda zai kara janyo hankulan masu yawon bude ido.

Wani mazaunin kauyen Nuoxi na garin Jiantang na Shangri-La mai suna Ciwang Pingcuo ya ce, a lokacin da, 'yan kabilar Zang sun yi zama a cikin ginin katako mai benaye 2. Domin gina irin wannan gini, mazauna wurin sun sare bishiyoyi masu tarin yawa.

"Da ma mu 'yan kabilar Zang mun yi amfani da katakai da yawa domin gina dakinmu mai girma kuma mai tsayi. Wannan ya kashe kudi da yawa kuma ya kawo illa ga muhallin halittu. Yanzu ra'ayinmu ya sauya, kuma gwamnati ta gina mana injuna masu yin amfani da makamashi daga hasken rana ba tare da biyan kudi ba. A hakika dai gwamnati tana kokarin yin amfani da makamashi daga hasken rana da yin tsimin makamashi."

Ciwang Pingcuo ya cigaba da cewa, gwamnatin wurin ba ma kawai ta gina injuna masu yin amfani da makamashi daga hasken rana ga duk wani iyalin kauyen ba, har ma ta bada tallafin kudi wajen gina ramukan iskar gas da akan samo daga taki. A halin yanzu, mazauna wurin suna yin amfani da makamashi maras gurbata muhalli, kamar su makamashi daga hasken rana, da iskar gas da akan samo daga taki, suna zama cikin tsabta.

Kauyen Tangdui na garin Nixi na gundumar Shangri-La ya yi suna ne wajen gasa kayayyakin yumbu. Amma za'a fitar da hayaki mai gurbata muhalli da yawa yayin da ake gasa kayayyakin yumbu. Domin rage yin amfani da katakai da yawan hayaki da ake fitarwa, masu aikin gasa kayayyakin yumbu a kauyen Tangdui suna neman makamashi na daban cikin himma da kwazo domin maye gurbin katakai, inda mataimakin manajan kamfanin gasa kayayyakin yumbu na kauyen Tangdui, Wang Dui ya furta cewa:

"A ganina, ya fi kyau a yi amfani da iskar gas da akan samo daga taki domin gasa kayan yumbu, wadda ba za ta lalace muhallin halittu ba."

A cikin 'yan shekarun nan, mazauna gundumar Shangri-La suna yin la'akari da wani batu ba tare da kakkautawa ba, wato yadda za su yi domin raya sha'anin yawon shakatawa mai dorewa, da kiyaye wuraren yawon shakatawa masu dogon tarihi. Sakataren yankin Diqing na kabilar Zang mai cin gashin kansa, Qizhala ya bayyana cewa, gwamnatin wurin na kokarin bunkasa sha'anin yawon shakatawa ba tare da bata muhalli ba, Ya ce:

"Muna son kiyaye muhallin halittu cikin dogon lokaci. A cikin 'yan shekarun nan, sha'anin yawon shakatawa na Shangri-La ya sami bunkasuwa kwarai da gaske, haka kuma za mu raya Shangri-La har ta zama wani wurin yawon shakatawa mai dorewa."