Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-06 17:12:12    
Abinci na Sichuan na yaduwa a duk duniya

cri

A cikin shirinmu na karshe na gasar kacici-kacicin, za mu dandana abinci mai dadi irin na Sichuan. Amma kafin mu soma shirinmu na yau, kamar yadda mu kan yi a da, zan gabatar muku da tambayoyi 2 na karshe, da farko, mene ne dandanon da mazauna Sichuan suke fi so? Ta biyu kuma, mene ne sunan wani irin cincin din na Sichuan da ake zuba ruwan bakin sukari kan kwallayen shimkafa mai danko 3? To, masu sauraro, bari mu more bakinmu da cincin din na Sichuan mai dadin ci!

Lardin Sichuan aljanna ce ta cin abinci mai dadi a idon dukkan Sinawa. A matsayinsa na daya daga cikin manyan tsare-tsaren abinci 4 na kasar Sin, abinci irin na Sichuan ya shahara a gida da kuma waje bisa hanyar dafa abinci da ta sha bamban da saura da kuma dandanon musamman na wurin. Kuku-kuku su kan yi amfani da abubuwa iri daban daban wajen dafa abinci irin na Sichuan, kuma akwai mabambanta dandano ta fuskar abinci na Sichuan, amma mazauna Sichuan suna fi son kayan abinci mai yaji. Har ma in an ambaci abinci iri na Sichuan, to, nan da nan an tuna da kayan abinci mai yaji. Amma donme mazauna Sichuan suke son kayan abinci mai yaji? Mao Jianhua, shehun malami da ke aiki a jami'ar Sichuan kuma masani mai ilmin al'adun gargajiya ya yi bayani cewa,"Sichuan na kasancewa cikin wani kwari, kuma akwai danshi sosai a wurin, shi ya sa mazauna wurin su kan kamu da ciwon amosanin kashi. Barkono da kuma yaji suna amfanawa wajen kiyaye mutane daga danshi. Shi ya sa aka iya dauka cewa, dalilin da ya sa mazauna Sichuan suke son kayan abinci mai yaji shi ne domin wurin da suke zama da kuma yanayin wurin. Sa'an nan kuma, ba 'yan kabilar Han kawai suna son kayan abinci mai yaji ba, haka kuma, sauran 'yan kananan kabilu kamar na Qiang da na Yi su ma suna son kayan abinci mai yaji sosai a Sichuan."

Daga wani bangare an kiyasta cewa, abinci na Sichuan ya hada da sassa fiye da dubu 4. Mapo Tofu shi ne daya daga cikin kayayyakin abinci na Sichuan na gargajiya da suka fi shahara. An yi wa farin Tofu ado da jajayen daddagen naman sa da koren kayan lambu, haka kuma, jan man girki na kewayen Tofu. Wannan kayan abinci na da yaji da kuma dadi sosai. Wang Bing, wani mai dakin cin abinci na samar da kayan abinci na Sichuan a Chengdu ya yi karin bayani cewa, tsawon shekarun kasancewar Mapo Tofu ya wuce dari daya. Akwai wata almara kan asalinsa. Mr. Wang ya fada mana cewa, "Asalin wannan kayan abinci shi ne wani karamin dakin cin abinci a Wanfuqiao da ke arewacin Chengdu. Sunan mijin shugabar shi ne Chen, akwai zanzana wato Mazi a bakin Sinawa a kan fuskar shugabar, shi ya sa akea kiranta Chen Mapo, wato matar Chen da ke da zanzana a fuskarta. Chen Mapo tana son dafa Tofu da daddagen nama da aka yi saura, kayan abinci da ta dafa na da dadin ci sosai, sannu a hankali, kayan abincin yana kasancewa ya zuwa yanzu."

Yanzu Mapo Tofu ya sami karbuwa sosai a duk duniya, amma a Chengdu kawai ake iya dandana tsantsar wannan kayan abinci. Baya ga Mapo Tofu, dafa yankakken nama da ganyaye a tukunya wato Huoguo shi ne ya shahara kwarai. Mazauna Sichuan su kan kewaye wata tukunya, su dafa yankakken nama da ganyaye a cikin miyar da aka yi da abubuwan kamshi iri daban daban, daga baya, su ci dafaffun naman da ganyayen tare da abubuwan kamshin da aka yi da yaji da barkono da gishiri da man ridi. Zuo Yanmei tana aiki a cikin wani shahararren dakin dafa yankakken nama da ganyaye a tukunya a Chengdu, ta yi mana karin bayani kan hanyar da a kan bi wajen cin wannan kayan abinci. Ta ce, "Halin musamman na wannan shahararren kayan abinci wato dafa yankakken nama da ganyaye a tukunya shi ne cin danyun abubuwa masu dadi da kamshi tare da kiwon lafiya. A kan dafa yankakken nama da ganyaye a cikin miyar da aka yi da yaji da kuma ba tare da yaji ba. Miyar da aka yi ba tare da yaji ba ta iya kiwon lafiyar mutane. Sa'an nan kuma, wasu ire-iren nama kamar naman sa da na kaji za su kara dadin ci in an dafa su cikin dogon lokaci. Haka kuma, dukkan masu son wannan kayan abinci sun san cewa, cikin sa da hancin dinya da kuma hanyoyin numfashi na sa su ne abubuwa 3 da ba a raba su da dafa yankakken nama da ganyaye a tukunya ba. Dadin dadawa kuma, a kan dafa laiman kwadi a cikin tukunya."

Mazauna Sichuan masu hikima sun raya kayan abinci na dafa yankakken nama da ganyaye a tukunya, sun fito da wani kayan abinci daban, wato Chuan Chuan Xiang. Ba kamar yadda ake dafa yankakken nama da ganyaye a tukunya ba, an dauri abubuwan abinci a kan wata sandar gora siririya, an ajiye ta a cikin miyar kayayyakin kamshi tukuna, daga baya, an dafa ta a tukunya kamar yadda aka dafa yankakken nama da ganyaye a tukunya. Feng Qingshu, darektan dakin samar da Chuan Chuan Xiang da ya fi shahara a Chengdu ya yi karin bayani cewa, "Chuan Chuan Xiang tana dacewa da kowa da kowa, tsaffi da yara dukkansu suna iya ci. Tana da dadin ci sosai amma ba tare da kudi da yawa ba. A kan dauri nama da kuma kayayyakin lambu a kan sandunan gora sirara. Babban halin musammanta shi ne dandana abubuwan abinci da yawa amma ba tare da kudi da yawa ba. "

Cincin irin na Sichuan shi ma yana matsayin daya daga cikin alamun abinci na Sichuan. Masu son cin abinci suna Allah-Allah don dandana cincin din iri daban daban na Sichuan.

Cincin na Sichuan ba ma kawai yana da dogon tarihi, kuma dandanonsa ya sha bamban sosai ba, har ma akwai labaru masu ban sha'awa kan sunayen cincin da yawa. Akwai wani irin cincin mai suna 'San Da Pao', da wuya ne aka gano danyun abubuwa da aka yi amfani da su domin samar da 'San Da Pao' bisa sunansa kawai. Mr. Mao ya yi mana karin bayani cewa, 'San Da Pao' shi ne zuba ruwan bakin sukari kan kwallayen shimkafa mai danko 3. Ya kuma bayyana mana dalilin da ya sa ake kiran wannan cincin 'San Da Pao'. Ya ce, "Hanyar da aka samar da 'San Da Pao' ta nuna halin musamman sosai. An fito da kwallayen shimkafa mai danko da girmansu bai kai na kosai ba. Daga baya, an yi wani abu ta hanyar fasaha domin samar da babban amo guda 3 kawai, ba domin kyautata dandanon abincin ba. Wato an jefa wadannan kwallaye 3 kan farantai 3 da karfi, kwallayen su fada a cikin wata rariya, inda akwai garin ridi da na wake a ciki, a dauka wadannan kwallaye 3, a ajiye su a cikin wani kwano, a zuba ruwan bakin sukari a kansu. Ma'anar San Da Pao ita ce babban amo guda 3 da suke yi kamar yadda aka harba bindiga."

Sinawa su kan ce, an fi samun abinci mai dadi a lardin Sichuan. A lokacin da masu yawon shakatawa da suka zo daga sassa daban daban na duniya suke yin ziyara a Sichuan, suna more idannunsu da ni'imtattun wurare na Sichuan, su ma suna more bakinsu da abinci mai dadi na Sichuan. Choi Kwang Sek ya kawo wa Sichuan ziyara a lokacin hutu daga kasar Korea ta Kudu, ya nuna babban yabo ga abinci mai dandano na Sichuan. Ya ce, "Abin da ya jawo hankalina a Sichuan shi ne ni'imtattun wurare., amma na kara jin farin ciki saboda cin tsantsar abinci na Sichuan. Abinci na Sichuan ya shahara ne a fannin yaji, ya dace ni kwarai, musamman ma abokaina da ni mun ci tsantsar Mapo Tofu tare. Mun ji matukar murna. Ina fatan abokan da suka zo daga sauran sassan duniya za su zo nan Sichuan domin kallon wurare masu ni'ima da kuma dandana abinci mai kyau. Ina kece rani a nan."