Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-05 21:35:25    
Labari game da kungiyar likitanci mai ba da taimako ga jihar Tibet

cri

A watan Mayu na wannan shekara, Mr. Du Jiming, jami'in gwamnatin birnin Qi Taihe na lardin Heilongjiang da ke arewa maso gabashin kasar Sin ya sami wata wasikar da Mr. Norbu Tsering, dan kabilar Tibet da ke zaune a gundmar Renbu ta jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ya rubuta don nuna masa godiya.

Gundumar Renbu wata karamar gunduma ce ta jihar Tibet, yawan mutanenta ya wuce dubu 30. Gundumar nan kuma tana kan faffadan tsauni wanda nisansa daga matsayin teku ya wuce mita 4000, sabo da haka akan gamu da mummuan yanayin halitta, kuma akan yi ambaliyar ruwa da girgizar kasa da sauran bala'un indallahi. A watan Fabrairu na wannan shekara, birnin Qi Taihe na lardin Heilongjiang ya aika da wata kungiyar likitanci mai ba da taimako ga jihar Tibet.

Sabo da karancin masu fasahar musamman, shi ya sa har tsawon shekaru 5 ba a taba yin aikin fida cikin asibitin gundumar Renbu ba kafin zuwan kungiyar likitanci a wannan gundumar, a dakin kwantar da marasa lafiya akan yi musu karin ruwa kawai. Mamban kungiyar kuma likita Si Congmin ya tuna da cewa, "Da na ga haka, sai na yi tunani cewa, ya kamata mu shiga cikin gidajen manoma da makiyaya da sauri don yada kimiyya, kuma ya kamata mu nuna kwarewa a fannonin aikin jiyya domin warkar da 'yanuwa marasa lafiya na kabilar Tibet da cece su daga bakin mutuwa."

A da an yi karancin likitoci da magungunan a jihar Tibet, bayan zuwan kungiyar likitanci mai ba da taimako a gundumar Renbu ta jihar an samu sauki wajen ganin likita. Amma sabo da likitoci sun yi ta shan aiki ba dare ba rana, shi ya sa suka gaji tikis, wata rana bayan da babban likita Si Congmin ya yi aikin fida ga wasu marasa lafiya, ya gaji kwarai kuma ga wahalar da aka jawo masa sabo da mummunan yanayin faffadan tsauni, shi ya sa ya suma har ya fadu cikin dakin yin fida. Yayin da ya waiwayi halin da ake ciki a lokacin ya ce, "Na gaji kwarai a wancan lokaci, kuma ina jin ciwon kai, kuma ina jin kumallo, ba na iya hangen nesa, kuma ina shan wahalar jan numfashi, ina jin kamar zuciyata ta fito, har na fadu kuma ban san kome ba."

Mambobin kungiyar likitanci mai ba da taimako ga jihar Tibet sun samu amincewa daga wajen 'yan kabilar Tibet sabo da irin cikakkiyar gwaninta da kyakkyawan aikin likitanci da suka yi. A da wasu mutane wadanda suka gwammace kuna turaren wuta don yin addu'a, ba su son ganin likita, amma yanzu sun je asibiti don neman a yi musu fida. Medok, wata 'yar addinin budda ce da ke cikin wani dakin ibadan birnin Lhasa, wadda kuma take fama da ciwon madaciya har tsawon shekaru da yawa, bayan da ta gani mutane marasa lafiya na kabilar Tibet sun warke bisa taimakon da 'yan kungiyar likitanci suka ba su, sai ta shafe awoyi 5 da wani abu tana tafiya cikin mota daga birnin Lhasa zuwa gundumar Runbu musamman domin ganin likita Si Congmin, dan kungiyar likitanci don neme shi da zai yi mata fida.

Cikin rabin shekarar da wannan kungiyar take ba da taimako ga jihar Tibet wajen likitanci, yawan marasa lafiya da ta yi musu aikin fida ya kai 38, daga cikinsu har da wasu ayyukan fida kamar yanke madaciya da haihuwa ta hanyar yin fida wadanda a da ba a taba yin su ba cikin asibitin jama'a na gundumar Renbu ta jihar Tibet. Mr. Dawa Tering, shugaban gundumar Renbu ya ce, "Likitocin da ke cikin kungiyar likitanci mai ba da taimako ga jihar Tibet sun kware a fannonin aikin jiyya, kuma su mutane ne masu kirki sosai, bayan da suka zo nan, an samu manyan sauye- sauye a gundumarmu, tunaninmu kuma ya canja. Lokacin da muke kamuwa da ciwo, sai nan da nan muka je asibiti don ganin likita. Bisa matsayina na wani ma'aikacin hukuma na gundumar, ina nuna musu godiya sosai sabo da wahalhalun da suka sha lokacin da suke aiki a nan don ba mu taimako wajen likitanci."

Gundumar Renbu tana kudu maso yammacin kasar Sin, gundumar Qitaihe kuma tana arewa maso gabashin kasar, amma aikin ba da taimako ga Tibet ya hada wadannan wurare 2 sosai.