Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-30 18:25:39    
Sin na maraba da karin manema labarai na waje da su zo kasar Sin don ba da rahotanninta

cri
A gun taron manema labarai da aka shirya yau 30 ga wata a nan birnin Beijing, shugaban ofishin samar da bayanai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, Mr.Wang Chen ya bayyana cewa, a shekarar da muke ciki, gwamnatin kasar Sin ta sami babban cigaba ta fuskar tafiyar da mulki a fili da kuma samar da bayanai ga al'umma. Sin na maraba da karin manema labarai na kasashen waje da su zo kasar Sin don ba da rahotanninta, kuma tana son kara bude kofarta, don bunkasa mu'amala da hadin gwiwa a tsakaninta da kasashen duniya.

A shekarar 2008, bala'u masu tsanani daga indallahi da suka hada da dusar kankara da girgizar kasa sun galabaitar da kasar Sin, a sa'i daya kuma, Sin ta gudanar da wasannin Olympic cikin nasara, haka kuma ta harba kumbo mai dauke da mutane zuwa sararin samaniya. Sabo da haka, a shekarar, Sin ta jawo hankulan duniya kwarai da gaske, har ma yawan manema labarai da suka zo kasar Sin ya kai matsayin koli a tarihi.

Mr.Wang Chen, shugaban ofishin samar da bayanai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, ya ce, a shekarar 2008, sassan da abin ya shafa na gwamnatin kasar Sin sun yi kokarin tafiyar da harkokin mulki a fili, kuma sun kara samar da bayanai ga al'umma, sun yi kokarin bayyana wa duniya gaskiyar kasar Sin da kuma sauye-sauyen da ke faruwa a kasar. Ya ce,"Gaba daya ofishin samar da bayanai na majalisar gudanarwa ta Sin da sassan gwamnatin tsakiya da kuma kananan hukumomi suka gudanar da tarurrukan manema labarai da yawansu ya kai 1587, wanda ya zarce na shekarun da suka gabata. Wani abin da ya kamata mu jaddada shi ne, an kafa tsarin watsa labarai da kirkiro da mukamin kakaki a ma'aikatar tsaro ta kasar Sin. A sa'i daya, ofishinmu ya kuma bayar da takardun bayanai dangane da manyan al'amuran da ke daukar hankulan duniya."

Ta fannin kulawa da yanar gizo ta internet, Mr.Wang Chen ya ce, yanar gizo ta internet a bude take daga dukan fannoni. Yawan masu amfani da yanar gizo ta internet a kasar Sin ya zo na farko a duniya, wanda kuma ya shaida mana gaskiyar al'amarin. Amma duk da haka, kamar yadda sauran kasashen duniya ke yi, Sin ita ma tana kulawa da yanar gizo ta internet bisa doka. Ya ce,"Mun koyi yadda sauran kasashe ke yi, kuma mun yi nazari a kan yadda za a daidaita matsaloli iri iri da ake fuskanta wajen bunkasa yanar gizo ta internet, tare da cimma nasara. A hakika, abin da muke yi a kullum shi ne tafiyar da internet a bude daga dukan fannoni tare da kulawa da su bisa doka."

Mr.Wang Chen ya ce, tun daga shekarar 2007, Sin ta bayar da "ka'idar ayyukan manema labarai na waje a lokacin wasannin Olympic na Beijing" da sauran ka'idoji, wadanda suka tabbatar da ayyukan manema labarai na kasashen waje a kasar Sin. Sin na maraba da karin 'yan jarida na waje da su zo kasar Sin domin ba da rahotanni. Ya ce,"Ko a yanzu ko kuma a nan gaba, Sin za ta tsaya tsayin daka a kan manufar bude kofa ga kasashen waje, kuma da sahihin zuci ne take maraba da manema labarai na kasashen waje da su zo kasar Sin don ba da rahotanninta, haka kuma za ta samar da sauki gare su." (Lubabatu)