Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-30 16:27:09    
Fasahar sauya kamannin fuska mai ban mamaki fasaha ce da babu kamar ta a cikin wasan kwaikwayon waka na Sichuan

cri
Yau ma bari mu kara saninmu kan wata fasahar musamman da ke cikin wasan kwaikwayon waka na Sichuan. Amma kafin mu soma shirinmu na yau, kamar yadda mu kan yi a da, ga wasu tambayoyi 2 da za mu yi muku, da farko, mece ce fasaha daya tilo da ta fi shahara a cikin wasan kwaikwayon waka na Sichuan? Ta biyu kuma, a birnin Chengdu, shin ana iya kallon wasan kwaikwayon waka na Sichuan a ko wace rana? To, masu sauraro, yanzu ku karkade kunnuwanku domin jin shirinmu na yau!

Ya zuwa yanzu tsawon shekarun kasancewar wasan kwaikwayon waka na Sichuan ya wuce dari daya. Ya shahara ne bisa murya mai dadin ji da 'yan wasa suka fito da ita a cikin wasan kwaikwayon da motsi da rawar 'yan wasan da kuma abubuwa masu ban sha'awa da 'yan wasan suka furta a cikin wasan. Lan Jiafu, wani sansannen dan wasan kwaikwayon waka na Sichuan ya yi shekaru fiye da 30 yana nuna wasan kwaikwayon waka na Sichuan. Ya yi karin bayani cewa,

"An mayar da wasan kwaikwayon waka na Sichuan da na Beijing da na Henan da dai sauransu a matsayin muhimman wasannin kwaikwayon waka na kasar Sin. Halin musamman da wasan kwaikwayon waka na Sichuan ke nunawa shi ne an fito da shi ne bisa al'adun Sichuan, a kan tanadi abubuwa masu ban sha'awa a cikinsa, kuma a kan nuna shi kamar yadda ake yi a zaman yau da kullum, shi ya sa kowa da kowa yake iya fahimta. Muryar 'yan wasa da ke cikin wasan kwaikwayon ta sha bamban da saura sosai bisa hanyar zaman rayuwa da mazauna Sichuan suka saba bi. Haka kuma, akwai wasu sassa masu ban sha'awa a cikin wasan kwaikwayon waka na Sichuan, kamar sauya kamannin fuska da boye wuka da wasan digirgire da kwano a ka da kuma yin wasa da kyandir."

A cikin fardar fasahohi da ke cikin wasan kwaikwayon waka na Sichuan, fasahar sauya kamannin fuska ita ce ta fi shahara. In an tabo magana kan wasan kwaikwayon waka na Sichuan, to, kusan kowa da kowa ya kan tuna da wannan fasaha nan da nan, ta kusan zama alamar wasan kwaikwayon waka na Sichuan. Tare da kide-kiden da aka samar da kayan kida na gong da ganga, 'yan wasan da ke kan dandamali su kan rufe fuskokinsu da hannun riga, su kada kansu, nan da nan su canza kamannin fuska, su fito da wata daban. Kwarewarsu ta nuna irin wannan fasaha ta ba mutane mamaki sosai.

Kusan ko wane dan kallon da ya kalli sauya kamannin fuska da ke cikin wasan kwaikwayon waka na Sichuan yana matukar neman gano sirrin wannan fasaha. Amma duk da haka, game da wannan sirri, ko wane dan wasan kwaikwayon waka na Sichuan bai ce kome ba. Chen Jiaxin, dan wasan nuna fasahar sauya kamannin fuska, wani saurayi ya bayyana mana cewa,

"Sauya kamannin fuska wata fasaha ce daya tilo da ke cikin wasan kwaikwayon waka na Sichuan. A kan nuna wannan fasaha ta hanyoyi 3, amma sirri ne da ba za a iya fada ba. Dan wasa mafi saurin sauya kamannin fuska ya iya sauya kamannin fuska sau 3 a dakika 1."

Domin tono sirrin fasahar sauya kamannin fuska, mun zanta da shehun malami da ke aiki a jami'ar Sichuan kuma masani mai ilmin al'adun gargajiya Mr. Mao Jianhua. Ashe! A kan sauya kamannin fuska ta hanyoyi 3, wato shafe fuska da fenti da buga garin kwalliya a kan fuska da kuma jan abubuwan rufe fuska daga fuskar dan wasa. A dandamali, 'yan wasa su kan ja abubuwan rufe fuska daga fuskokinsu. Mr. Mao ya ce,

"Galibi dai, 'yan wasa su kan sauya kamannin fuska ta hanyar jan abubuwan rufe fuska daga fuskokinsu a kan dandamali. Ja abubuwan rufe fuska daga fuskar dan wasa shi ne an yi zanen fuskoki kan siliki tukuna, an hada wadannan siliki da wata igiya siririyakan fuskar dan wasa daya bayan daya, dan wasan ya daura wannan igiya siririya a kan wani sashen da ke rigarsa, inda ya iya kama igiyar a saukakke ba tare da janyo hankalin saura ba. A lokacin nuna wasan kwaikwayon, tare da rawar da yake yi, dan wasan ya ja abubuwan rufe fuska daga fuskarsa daya bayan daya. Amma abin da ya fi wuya shi ne in an hada abubuwan rufe fuska da gulu da yawa fiye da kima, to, ba zai iya ja abubuwan rufe fuska ba, ko kuma zai ja su gaba daya. Sa'an nan kuma, tilas ne dan wasan ya ja abubuwan rufe fuska cikin sauri, kuma tare da rawar da yake yi yadda ya kamata, ta haka 'yan kallo ba za su iya tonon sirrin fasaharsu ba."

Ko da yake haka ne, amma mutane su kan tambayi yadda 'yan wasa su kan ja abubuwan rufe fuska, a ina ne suka boye su. Game da wadannan sirri, watakila mu 'yan kallo ba za mu iya tonowa ba. Kamar yadda Lan Jiafu ya fada, su ne abubuwa masu ban mamaki da ke jawo hankalin mutane. Ya ce,

"Masu fasahar sauya kamannin fuska suna kiyaye sirrin wannan fasaha. In mun tona wannan sirri kamar yadda aka tono sirrin dabo, to, mutane ba za su ci gaba da mamaki ba."

A matsayin wata fasaha ta daban da ke cikin wasan kwaikwayon waka na Sichuan kamar yadda fasahar sauya kamannin fuska ke kasancewa, an iya dauka cewa, tofa wuta daga bakin dan wasa ya fi tsorata mutane. 'Yan wasa sun iya tofa wuta daga bakinsu. An ce, 'yan wasa su kan kunshe kananzir a bakinsu, su tofa hazon kananzir din tare da kunna shi. Abu mafi muhimmanci shi ne kafin wutar ta kare, kada dan wasan ya yi numfashi, in ba haka ba, zai kunna wa kansa wuta. A dandamali, 'yan wasa su kan sauya kamannin fuska tare da tofa wuta daga bakinsu, ta haka su kan bai wa 'yan kallo mamaki sosai.

A birnin Chengdu, hedkwatar lardin Sichuan, har zuwa yanzu mutane suna iya jin dadin kallon wasan kwaikwayon waka na Sichuan na gargajiya. Shan shayi da cin cincin tare da kallon wannan wasan kwaikwayon waka ita ce hanyar zaman rayuwa da mazauna Sichuan suka saba bi. Li Xian, shugaban wani wurin shan shayi ya gaya mana cewa, ko ana ruwa ko ana yin iska mai karfi, a ko wace rana, ana nuna wasan kwaikwayon waka na Sichuan. Ya ce,

"A ko wace rana, muna fara nuna wasan kwaikwayon waka na Sichuan da karfe 8 na dare. Muna ci gaba da nuna wasan kwaikwayon, ko da yake akwai dan kallo daya tilo. Muna himmantuwa kan wasan kwaikwayon waka na Sichuan kamar yadda ake bin addini. Ko mun iya samun kudi, ko kuma an bata kudinmu sosai, za mu ci gaba da nuna wasan kwaikwayon waka na Sichuan. A lokacin da kasuwa ke ci sosai, mu kan nuna wasan kwaikwayon sau 2 a ko wace rana, 'yan kallo 800 su kan iya kallon wasan kwaikwayon a ko wane karo. Mun sami karbuwa sosai a gida da kuma waje."

Wasan kwaikwayon waka na Sichuan ya jawo hankulan 'yan kallo daga sassa daban daban na duniya, suna Allah-Allah don kallon sauya kamannin fuska mai ban mamaki da ke cikin wasan kwaikwayon waka na Sichuan. Bayan da ya kalli wasan kwaikwayon, Asaad Addin da ya zo daga kasar Yemen ya gaya mana cewa,

"Wannan shi ne karo na farko da na zo nan Chengdu. Wasan kwaikwayon waka na Sichuan na da ban sha'awa ainun, shi ne kuma wasan kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin, da ya iya wakiltar al'adun kasar Sin, Ina sha'awar wasan sauya kamannin fuska sosai, yana da dadi sosai."

To, madalla, masu sauraro, lokaci ya yi da za mu sa aya ga shirinmu na yau, amma kafin mu yi ban kwana da ku, bari mu maimaita tambayoyi 2 da muka kawo muku, da farko, mece ce fasaha da ta fi shahara da ke cikin wasan kwaikwayon waka na Sichuan? Ta biyu kuma, a birnin Chengdu, shin ana iya kallon wasan kwaikwayon waka na Sichuan a ko wace rana?