Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-26 17:20:37    
Sin na kokarin taimakawa ma'aikata da kamfanoni wajen haye wahalhalu

cri
Bayan da zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya gudanar da bincike kan yadda ake aiwatar da dokar da ta shafi daukar ma'aikata , an gano cewa, ko da yake matsalar hada-hadar kudi ta duniya ta kawo illa ga habakar tattalin arzikin kasar Sin da masana'antunta, amma wurare da sassa daban-daban suna daukar kwararan matakai, a wani kokarin kare hakki da moriyar 'yan kwadago, da taimakawa kamfanoni wajen haye wahalhalu. Haka kuma, zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya nuna cewa, duk tsananin wahalar da muke sha tattare da rikicin hada-hadar kudi na duniya, kamata ya yi mu kara mayar da hankali kan zaman rayuwar jama'a, da kara nuna hazaka domin kiyaye moriyar ma'aikata.

Dokar da ta shafi daukar ma'aikata, tana daya daga cikin muhimman dokokin da gwamnatin kasar Sin ke aiwatarwa ta fannin kwadago, wadda ke maida hankalinta kan kare hakki da moriyar ma'aikata, da bukatar kamfanoni da su rattaba hannu kan rabutattun kwangiloli. Shekara mai karewa wato shekarar 2008, shekara ce ta farko da aka fara aiwatar da wannan doka a hukunce. Daga watan Satumba na bana, zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya soma gudanar da bincike kan yadda ake aiwatar da wannan doka a kamfanoni daban-daban da yawansu ya zarce 30 a birane 18 na kasar Sin. Sakamakon binciken ya shaida cewa, bayan da aka aiwatar da dokar da ta shafi daukar ma'aikata, yawan mutanen da suka daddale kwantaragi tare da kamfanoni ya karu ainun, hakki da moriyar ma'aikata, musamman ma moriyar manoma 'yan ci rani ta sami ingantuwa kwarai da gaske.

Amma tun da watan Oktoba na wannan shekara, rikicin hada-hadar kudi da ya dabaibaye duniya ya rika kawo illa ga habakar tattalin arzikin kasar Sin, tare da matsa lamba ga kamfanonin kasar, aiwatar da dokar da ta shafi daukar ma'aikata yana fuskantar wasu sabbin matsaloli. A halin yanzu, hukumomi daban-daban na wurare daban-daban na kasar Sin suna kokari ba tare da kasala ba wajen lalubo bakin zaren daidaita wadannan matsaloli, kamar yadda mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Mista Hua Jianmin ya ce:

"Sakamakon binciken ya nuna cewa, kwalliya ta biya kudin sabulu wajen aiwatar da dokar da ta shafi daukar ma'aikata. Yanzu sassa daban-daban, da wurare daban-daban suna daukar matakai cikin himma da kwazao wajen shawo kan matsalar hada-hadar kudi."

A waje daya kuma, zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya bayyana cewa, a halin yanzu, ya kamata a mayar da hankali kan kare hakki da moriyar ma'aikata, da taimakawa kamfanoni wajen haye wahalhalu a cikin lokaci guda, inda Hua Jianmin ya cigaba da cewa:

"Duk tsananin wahalar da muke sha tattare da rikicin kudi, ya kamata mu kara maida hankalinmu kan kyautata zaman rayuwar jama'a, da aiwatar da dokar da ta shafi daukar ma'aikata yadda ya kamata, da kara tabbatar da kwanciyar hankali a zaman al'umma."

Dadin dadawa kuma, dangane da zaman rayuwar manoma 'yan ci rani masu karamin karfi, zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya bukaci a kara kiyaye hakkinsu, da kara samar musu da guraben aikin yi, inda Mista Hua ya ce:

"Ya kamata a dauki kwararan matakai domin bada tabbaci ga bayar da isasshen albashi ga manoma 'yan ci rani, da daidaita takaddama tsakanin manoma 'yan ci rani da kamfanoninsu. Kazalika kuma, kamata ya yi a kara samar musu da guraben aikin yi, da horas da su, gami da inganta kwarewarsu".(Murtala)