Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-24 08:43:44    
Sirrin yaduwar wasan kwallon kafar mata a kasar Amurka

cri

Ran 7 ga watan Disamba na bana, an kawo karshen gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta matan da ba su kai shekaru 20 da haihuwa ba ta shekarar 2008 a kasar Chile. A yayin gasar, kungiyar 'yan wasan kwallon kafa ta matan kasar Amurka ta sake zama zakara. Bisa kididdigar da aka yi, gaba daya kungiyar 'yan wasan kwallon kafa ta matan kasar Amurka ta taba samun damar zama zakara sau biyar wato karo uku a gasar wasannin Olympic kana karo biyu a gasar cin kofin duniya. To, ina dalilin da ya sa matsayin wasan kwallon kafa na mata na kasar Amurka ya zama kolin haka? A hakika dai, sirrinsa shi ne yada wasan kwallon kafa mai sa farin ciki a cikin makarantu. A cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani kan wannan.

Masu sauraro, a cikin wannan gasar cin kofin duniya ta kwallon kafa ta mata, 'yan wasa daga kasar Amurka sun yi wake-wake kuma sun yi raye-raye, a bayyane ana iya gane cewa sun fi jin dadi saboda halin nishadin da suke ciki. A akasin haka, wasu kungiyoyin 'yan wasan da suka zo daga sauran kasashen duniya sun tsorata a gasa. Ana tsamani cewa, halin nishadin da 'yan wasan kasar Amurka ke ciki shi ne dalili mafi muhimmanci da ya sa kungiyarsu ta sake zama zakara, a waje daya kuma halinsu ya fi jawo hankulan 'yan kallo.

Kafin karawar kusan karshe tsakanin kungiyar kasar Amurka da ta kasar Jamus, 'yan wasan kasar Amurka sun rera wakoki masu farin jini bayan da suka ci abincin dare, kuma sun yi raye-raye tare da kide-kiden Latin tamkar a gun taron shaye-shaye, amma 'yan wasan kungiyar kasar Jamus wadanda ke zaune a cikin otel daya tare da su yi haka ba, sai suka yi ta aikin share fage kawai.

Game da wannan, babban malami mai horaswa na kungiyar kasar Amurka Tony Dicicco ya bayyana cewa, "Abu mafi muhimmanci shi ne kiyaye sha'awar 'yan wasa kan wasan kwallon kafa, in ba haka ba, ba za su ci gaba da wasan ba, shi ya sa kamata ya yi wasan kwallon kafa ya hada da nuna sha'awa."

Tony Dicocco ya ci gaba da cewa, a kasar Amurka, yawancin iyaye suna fatan yaransu za su shiga wasanni tare da sauran yara, haka kuma, yara za su motsa jikinsu kuma za su kara karfin tunanin hadin guiwa. Alal misali, wasan kwallon kafa da wasan kwallon kwando da wasan kwallon rugby da sauransu. Ana iya cewa, atisayen wasan kwallon kafa ya fi nuna sha'awa, musamman ga 'yan wasa mata, saboda haka, a kasar Amurka, wasan kwallon kafa ya fi jawo hankulan 'yan mata. Tony Dicicco ya yi mana bayani cewa, aikin malami mai horaswa a kasar Amurka ya sha bamban sosai da na sauran kasashe. Ya ce,  "A kasar Amurka, aiki mafi muhimmanci ga malami mai horaswa shi ne kara janyo sha'awar 'yan wasa kan wasan kwallon kafa, a sakamakon haka, 'yan wasa za su yi atisaye da kansu ba tare da sa idon malamin horaswa ba. Daga tarihin bunkasuwar wasan kwallon kafa a kasar Amurka, ana iya gane cewa, ba malamai masu horaswa ne suka horas da 'yan wasa ba, sai dai 'yan wasa sun yi atisaye da kansu, kana daga baya kuma matsayinsu ya dinga daguwa a kai a kai. Malamai masu horaswa na wasan kwallon kafa na kasar Amurka sun fi mayar da hankali kan samar da jagoranci ga 'yan wasa saboda suna yin atisaye da kansu. A waje daya kuma, bisa al'adar wasan kwallon kafa ta kasar Amurka, aikin malamai masu horaswa shi ne kafa wata kungiyar wasa da kuma tsara shirin atisayen wasa."

A gun wannan gasa, iyayen 'yan wasan kungiyar kasar Amurka da yawan gaske sun je kasar Chile domin sa kaimi ga yaransu, iyayen Ellie Reed su ma haka, sun gaya mana cewa, tun diyarsu tana karamar yarinya mai shekaru shida, sai suka aike da ita zuwa wani kulob na wasan motsa jiki domin yin atisaye a can. A wurin, diyarsu ta taba koyon wasan kwallon kwando da wasan tsalle-tsalle da lankwashe-lankwashe da wasan kwallon kafa da wasan iyo. Daga baya kuma ta girma har ta kai shekaru 12, a wannan lokaci kuma Ellie ta tsai da cewa, za ta ci gaba da yin atisayen wasan kwallon kafa kadai, dalilin da ya sa haka shi ne domin ta fi jin farin ciki kwarai yayin da take yin wasan. Ellie ta yi karatu, a sa'i daya kuma tana yin atisayen wasan kwallon kafa. Kodayake wasan kwallon kafa ya dauki lokacinta da yawa, amma bai kawo mugun tasiri ga karatunta ba. Kan wannan batu, mahaifiyar Ellie ta ce: "ana iya cewa, wasan kwallon kafa ya taimaka mata wajen yin amfani da lokaci, saboda ta gane sosai, dole ne ta kashe lokaci kan fannoni biyu wato wasan kwallon kafa da kuma karatu." Mahaifinta ya ce: "ma'aunin Ellie kan wasan kwallon kafa da karatu daya ne, wato shi ne matsayin koli guda, shi ya sa babu sabani tsakaninsu."

A kasar Amurka, 'yan mata wadanda ke sha'awar wasan kwallon kafa suna da yawan gaske. Wannan harsashi ne na yaduwar wasan a kasar. Ban da wannan kuma, abu mafi muhimmanci shi ne bunkasa wasan a cikin makarantu. Tony Dicicco ya yi mana bayani cewa, a kasar Amurka, yawancin yara masu shekaru 6 suna fara atisayen wasan kwallon kafa a cikin kulob din motsa jikin da aka kafa musamman domin yara da samari, bayan da suka shiga makarantar midil, sai su shiga hadaddiyar gasa tsakanin kungiyoyin wakilan daliban makarantun midil. Daga baya kuma, bayan da suka shiga jami'a, to, za su shiga hadaddiyar gasa tsakanin jami'o'in duk kasar Amurka. Tony Dicicco ya bayyana cewa, hadaddiyar gasar wasan kwallon kafa tsakanin jami'o'in kasar Amurka ta sa kaimi ga bunkasuwar wasan na mata a kasar sosai. Ya ce,  "A kasar Amurka, hadaddiyar gasar wasan kwallon kafa ta mata tsakanin jami'o'i tana da mihimmanci kwarai da gaske, dukkan 'yan wasan kungiyata sun zo ne daga kungiyar jami'a, sun sami babban ci gaba a cikin jami'a. A ganina, bunkasa wasan a cikin makarantu hanya ce mafi kyau ta bunkasuwarsa. Ba ma kawai kana iya yin karartu a cikin makaranta ba, har ma kana iya kara karfin lafiyar jikinka."

A cikin wadannan 'yan wasa na kungiyar Amurka, yawancinsu sun je kasar Chile tare da littafi saboda dole ne su rubuta jarrabawa bayan da suka koma kasarsu. Amma haka ba zai kawo mugun tasiri ga gasa ba. A kasar Amurka, yawancin dalibai ba za su zama 'yan wasa na sana'a ba, sai dai, wasan kwallon kafa nishadi ne kawai gare su.

Yanzu, Malia Obama, diyar shugaban kasar Amurka mai jiran gado Barack Obama ta fi jawo hankulan mutane, tana yin atisaye a cikin kulob din motsa jiki na Chicago, Tony Dicicco ya dauka cewa, wannan zai kara ingiza yalwatuwar wasan a Amurka. Ya ce,  "A hakika dai, ina fatan 'yaya biyu na Obama za su shiga wasan kwallon kafa tare, haka kuma zai sa wasan ya kara samun karbuwa a kasar, idan shugaban kasa ya zo kallon gasa, to, zai kara kyau."(Jamila Zhou)