Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-22 19:53:34    
Wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

---- Cikin takardar sunayen kamfanoni wadanda suka samu iznin tafiyar da harkokinsu a duniya a shekarar 2008 da kungiyar FLA ta bayar kwanan baya, bisa sunan kasar Sin ne kamfanin sayar da abincin Sinawa mai sunan Xiaofeiyang na jihar Mongoliya ta gida ya samu wannan babban yabo a karo na farko, kuma karo na farko ke nan da wani sanannen kaya na kasar Sin ya samu wannan babban yabo.

Kungiyar ta bayyana cewa, dalilin da ya sa kamfanin Xiaofeiyang ya samu wannan babban yabo shi ne ayyuka nagari da ya yi wajen tafiyar da harkokinsa.

An ce, Xiaofeiyang wani kamfani ne na zamani wanda yake yin hidima daga fannoni daban-daban wajen sayar da abinci na kasar Sin, wanda kuma yake da tsarin sayar da abinci ko'ina. Ya zuwa yanzu yawan kananan sassan sayar da abinci da kamfanin Xiaofeiyang ya kafa ya kai fiye da 350 wadanda suke barbaje a babban yankin kasar Sin da Hongkong da Macao da kasashen Japan da Amurka da Canada da Hadaddiyar daular Larabawa.

---- Kwanan baya a birnin Lhasa an bude taro na 5 na nuna yabo ga masu ba da misali wajen hadin kai da ci gaban kabilun jihar Tibet, da akwai hukumomi 155 da mutane 237 wadanda suka samu lambobin yabo a gun taron.

Taron ya bayyana cewa, a shekarar da muke ciki an samu nasara wajen yaki da bala'in dusar kankara da babbar girgizar kasa ta Wenchuan, kuma an daidaita rikicin "Ran 14 ga Maris" da ya faru da birnin Lhasa, ta yadda za a tabbatar da aikin mika wutar wasannin Olimpic a kolin tudun Everest wato Jumo Langma, cikin wadannan ayyukan da aka yi an bullo da tarin kungiyoyi da mutane masu ba da misali, wadanda kuma suka ba da muhimmin taimako ga kara hadin kan kabilu, da yin adawa da masu jawo baraka ga al'ummar kasar, da kiyaye dinkuwar kasa daya, da sa kaimi ga bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma.

Da akwai kabilu fiye da 10 wadanda suke zaune a Jihar Tibet, daga cikin su kuma yawan 'yan kabilar Tibet ya wuce kashi 90 bisa 100. Dangantaka mafi muhimmanci ta jihar Tibet ita ce dangantakar da ke tsakanin kabilu. A gun taron nuna yabo, Mr. Zhang Qingli, sakataren kwamitin jam'iyya na jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta JKS ya yi jinjina sosai ga dangantakar dake kasancewa tsakanin kabilun jihar cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, kuma ya yi bayani sosai kan muhimmiyar ma'ana wajen kulla dangantaka mai jituwa kuma mai dorewa tsakanin kabilu.