Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-19 16:00:17    
Kwamitin sulhu na MDD

cri
Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malama A'isha Hamza, wadda ta zo daga birnin Yola, jihar Adamawa, tarayyar Nijeriya. A cikin wasikar da malamar ta aiko mana, ta ce, ina so ku yi cikakken bayani a kan kwamitin sulhu na MDD, kuma shin yaya ake zabar mambobinsa?

To, malama A'isha da dai sauran masu sauraronmu, yanzu sai ku gyara zama ku saurari bayaninmu a kan kwamitin sulhu na MDD.

kwamitin sulhu na daya daga cikin muhimman hukumomi shida na MDD, kuma yana daukar nauyin kiyaye zaman lafiya da tsaro a duniya. Kwamitin sulhu na da ikon gudanar da bincike a kan duk wani abin da ya haddasa rikici ko gardama a tsakanin kasa da kasa, kuma yana iya gabatar da hanyoyin da za a bi wajen daidaita su. Kwamitin sulhu na iya yanke shawara a kan ko ya kasance da ayyuka na lalata zaman lafiya, kuma zai iya gabatar da shawarwari da tsai da kuduri na daukar matakai domin kiyaye ko maido da zaman lafiya a duniya. Ban da wannan, kwamitin sulhu yana kuma daukar nauyin gabatar da rahoton shekara shekara da rahoton musamman ga babban taron MDD.

Sa'an nan, a game da mambobinsa, kasashe biyar na da kujerun dindindin a cikin kwamitin sulhu, wato su ne Sin da Faransa da Rasha da Birtaniya da Amurka. Sa'an nan, a gun babban taron MDD, a kan zabi wasu kasashe a kan kujerun da ba na dindindin ba cikin kwamitin sulhu, wadanda yawansu ya kai shida tun farkon fari, daga baya aka kara su zuwa 10. Daga cikin kasashen 10 kuma, biyu kasashe ne na Asiya, sa'an nan akwai kasashe uku na Afirka da biyu na Latin Amurka da kuma daya na gabashin Turai, a yayin da kasashen yammacin Turai da sauran kasashe suka sami kujeru biyu. Wa'adin aikinsu ya kai shekaru biyu, kuma a kan yi zabe a kowace shekara domin canza biyar daga cikinsu. Bisa ka'ida, sabbin mambobi biyar da aka zaba a kowace shekara ya kamata su kunshi kasashe uku na Asiya da Afirka da wata kasar gabashin Turai tare kuma da kasa guda ta Latin Amurka ko yankin Caribbean. Mambobin kwamitin sulhu na yanzu sun hada da Belgium da Italiya da Afirka ta kudu da Indonesia da Panama, wadanda suka fara aiki tun ran 1 ga watan Janairu na shekarar 2007, da kuma Libya da Burkina Faso da Vietnam da Croatia da Costa Rica, wadanda suka fara aiki tun ran 1 ga watan Janairu na shekarar 2008 da muke ciki.

Kowace mambar kwamitin sulhu na da ikon kada kuri'a, amma ba su iya kada kuri'ar nuna rashin amincewa, a yayin da kasashen da ke da kujerun dindindin cikin kwamitin sulhu suna da ikon kada kuri'ar nuna rashin amincewa a kan muhimman batutuwa, wato idan wata kasa ta kada kuri'ar nuna rashin amincewa, to, ba za a iya zartas da abin ba.

Mukamin shugaban kwamitin sulhu na MDD yana rika zagayawa a tsakanin mambobin dindindin da kuma wadanda ba na dindindin ba na kwamitin, wato bisa tsarin harufa na sunayensu.

Kwamitin sulhu ya kan kira taro sau biyu a kowace shekara, amma idan shugaban kwamitin yana ganin ya dace, ko kuma idan babban taron MDD ko babban sakatare ko kuma kowace mambar kwamitin ya shawarta, to, zai iya kira taro nan da nan. (Lubabatu)