Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-18 15:44:38    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin

cri
Dansa ya bace yayin da ya daure kekensa na hawa a kan titi. Bisa labarin da aka buga a cikin jaridar Yanzhao evening news ta lardin Hobei dake arewancin kasar Sin a makon jiya, an ce a ranar litinin da ta shige, wani uba ya dauke da dansa ya tafi babbar kasuwa domin saye abubuwa na zaman yau da kullum. Yayin da ya isa wurin yana so ya ajiye kekensa na hawa sabon ful a wani wuri daban, ya kuma daure shi da makulli guda biyu, amma hankalinsa bai sauka kan dansa ba a lokacin, a wannan lokaci wata mata ta tafi da dansa. Bayan da uban yaro ya ajiye kekensa, ba ya ga dansa, sai hankalinsa ya tashi, ya fashe da kuka, yana gayyar kokarin neman dansa. Duk da haka ya samu dansa daga baya, dalili kuwa shi ne yayin da wannan mata ta tafi da dansa, wani mutum mai kirki yana bin sawunta, ba da dadewa ba ya sanar da 'yan sanda, 'yan sandan sun kama matar,sun ba uban dansa, uban ya yi farin ciki ya gode wa 'yan sanda.

Wata mace ta yi sa'a ta wadata saboda ta sayar da tuffafi na musamman. Bisa labarin da aka buga a cikin jaridar Shenyang evening news ta lardin Liaoning dake arewa maso gabacin kasar Sin a makon da ya gabata, an ce wata mace mai suna Zhao ta yi sa'a ta wadata sabo da ta sayar da tuffafi na musamman. Macen nan tana da kiba sosai, nauyinta ya kai kilo 120, ba safai a irinta ba yawancin wurare na kasar Sin. Duk da haka tana da kantuna da dama na sayar da tuffafi domin mata masu kiba kamar ta, daga baya ta yi sa'a ta samu kudi. Kudin da ta samu a ko wane wata ya kai kudin Sin Yuan dubu talatin wato dalar Amurka dubu hudu da dari hudu, matsakacin albashi na yawancin ma'aikatan gwamnati kimanin dalar Amurka dari hudu kawai a wata.