Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-17 16:02:24    
Kayan lambu da 'ya'yan itatuwa suna amfanawa lafiyar jiki

cri
Bisa labarin da jaridar Asahi Shimbun ta kasar Japan ta bayar a kwanan nan, an ce, shan taba da kuma shan giya suna iya kara hadarin kamuwa da sankarar jannai, haka kuma bisa binciken da ma'aikatar kula da jin dadin jama'a ta kasar Japan ta gudanar a 'yan kwanakin nan da suka gabata, an ce, watakila kara cin kayayyakin lambu da kuma 'ya'yan itatuwa zai iya rage hadarin.

Bayan da aka gudanar da wannan bincike ga maza dubu 39 da shekarunsu yana tsakanin 45 da 74 da haihuwa har shekaru 8 a fannin cin abinci da shan taba da kuma shan giya, a ciki mutane 116 sun kamu da sankarar jannai a tsawon wannan lokaci.

Ban da wannan kuma an bincike yawan kayayyakin lambu da 'ya'yan itatuwa da suka ci. Kuma manazarta sun kasa mutanen da aka gudanar da bincike gare su cikin kungiyoyi biyu, wato kungiyar masu cin kayayyakin lambu da 'ya'yan itatuwa kullum da kuma kungiyar wadanda da ba safai a kan ci kayayyakin kullum ba bisa nauyin kayayyakin lambu da 'ya'yan itatuwa da suka ci a ko wace rana ya kai gram 540 da na tsakanin gram 70 da 320.

Daga baya kuma an gano cewa, idan aka mayar da yiyuwar kamuwa da sankarar jannai a matsayi 1 ga mutanen da ba su shan taba kuma yawan giya da su kan sha a ko wace rana bai kai litre 0.2 ba a cikin kungiya da ba safai a kan ci kayayyakin lambu da 'ya'yan itatuwa kullum ba, to yiyuwar kamuwa da sankarar jannai ga wadanda suka sha taba da kuma shan giya fiye da litre 0.2 a cikin kungiyar ya kai 7.67. Amma a cikin kungiyar cin kayayyakin kullum, yiyuwar kamuwa da sankarar ga wadanda suka sha taba da kuma shan giya fiye da litre 0.2 ya kai 2.86 kawai.

A galibi dai, idan an kara cin kayayyakin lambu da 'ya'yan itatuwa, to za a iya rage yiyuwar kamuwa da sankarar jannai, kuma idan an kara cinsu da yawansu ya kai gram 100 a ko wace rana, to yiyuwar kamuwa da sankarar za ta iya rage kimamin kashi 10 cikin dari.

To, masu sauraro, yanzu sai ku shakata kadan, daga baya kuma za mu yi muku wani bayani kan cewa, cin apple yana iya ba da taimako wajen shawo kan sankarar hanji.

A 'yan kwanakin nan da suka gabata, manazarta na kasar Jamus sun gano cewa, cin apple yana iya ba da taimako wajen rage yiyuwar kamuwa da sankarar hanji. Ta haka an samu wata sabuwar shaida ta wani karin magana na kasashen yamma wato cin apple daya a ko wace rana, likitoci za su bar ni.

Bisa labarin da kafofin watsa labarai na kasar Jamus suka bayar, an ce, kungiyar nazari a karkashin jagorancin dakta Dieter Schrenck ta ba da rahoto a kan mujallar ilmin gina jiki ta kasar Amurka, cewar sakamakon nazari ya bayyana cewa, apple da ruwansa suna iya ba da taimako wajen kara karfin jiki wajen samar da sinadarin shawo kan sankara musamman ma a fannin shawo kan sankarar hanji.

Manazarta suna ganin cewa, pectin da ke cikin apple da kuma ruwan apple suna iya ba da taimako wajen kara sinadarin butyrate da ke cikin jikin dan Adam, wanda zai iya rigakafin barkewar sankarar hanji. (Kande Gao)