Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-16 16:01:01    
Zirga-zirgar kumbon kirar "Shenzhou-7"

cri
A ran 25 ga watan jiya da misalin karfe 9 da minti 10 na dare, an harba kumbon kirar "Shenzhou-7" mai dauke da mutane na kasar Sin cikin nasara, ta haka an kaddamar da zirga-zirgar kumbo mai dauke da mutane a karo na uku na kasar Sin. Idan an kwatanta da kumbon kirar "Shenzhou-5" da "Shenzhou-6", to za a iya gano cewa, ba kawai yawan 'yan sama-jannati da kumbon kirar "Shenzhou-7" ya dauka ya karu daga 1 zuwa 3 ba, har ma an yi gwajin fitowa daga kumbon a karon farko na kasar Sin. To, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku wani bayani ne kan zirga-zirgar kumbon kirar "Shenzhou-7".

Zhang Bonan, babban mai zayyane-zayyane kan kumbo kirar "Shenzhou-7" ya yi mana bayani kan ayyukan fasaha na zirga-zirgar kumbon, cewa

"An yi gyare-gyare kan fasahohin kumbon kirar 'Shenzhou-7' daga fannoni uku. Na farko shi ne yin fasali da kuma gwaji kan harkokin yin tafiya a sararin samaniya, na biyu shi ne shigad da 'yan sama-jannati uku cikin kumbon, wadanda yawansu ya kai matsayin koli ga kumbon, na uku shi ne yin gwaji kan wasu fasahohin zirga-zirgar sararin samaniya da kasar Sin ta yi nazari da kirkire-kirkire cikin gashin kai."

A cikin wannan aikin zirga-zirgar kumbon "Shenzhou-7", abin da ya fi jawo hankalin Sinawa shi ne yin tafiya a sararin samaniya wanda ya zama karo na farko ga 'yan sama-jannati na kasar Sin, to yanzu bari mu saurari gaisuwar da Zhai Zhigang, dan sama-jannati na farko na kasar Sin wajen yin tafiya a sararin samaniya ke yi wa duk duniya lokacin da yake fitowa daga kumbon.

"Na riga na fito daga kumbo, ina cikin koshin lafiya, kumbon kirar 'Shenzhou-7' yana nuna gaisuwa ga jama'ar Sin da kuma jama'ar duk duniya. Don Allah kasarmu ta kwantar da hankalinta, muna tsayawa tsayin daka kan kammala aikinmu."

Zhou Jianping, babban mai zayyane-zayyane na aikin zirga-zirgar sararin samaniya tare da daukar mutane na kasar Sin ya bayyana cewa, nasarar da dan sama-jannti na kasar Sin ya samu wajen fitowa daga kumbo za ta ba da taimako ga kasar Sin wajen samun fasahohin da ke da nasaba da fitowa daga kumbo, wanda ya shaida cewa, kasar Sin ta samu babban ci gaba a kan hanyar kafa dakin gwaje-gwaje a sararin samaiya da kuma tashar sararin samaniya. kuma Mr. Zhou ya kara da cewa,

"Dan Adam yana iya yin amfani da inji bai iya ba a sararin samaniya. Bayan da aka samu fasahohin fitowa daga kumbo, to za a iya gudanar da aikin sanya injuna da gyara su da dai sauran ayyukan gwaje-gwaje na ilmin kimiyya a wajen kumbo, shi ya sa fitowa daga kumbo yana daya daga cikin muhimman fasahohin zirga-zirgar sararin sama tare da daukar mutane. Daga baya kuma za mu gudanar da aikin hada kumbuna biyu tare. Idan mun samu dukkan fasahohin harba kumbo cikin hanyar da aka tsara, da dawowa cikin lumana, da gudanar da aiki a kan hanyar da aka tsara, da fitowa daga kumbo, da kuma hada da kumbuna biyu tare, to za mu iya gudanar da manyan harkokin zirga-zirgar sararin samaniya a nan gaba."

To, masu sauraro, shirnmu na yau na "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin" ke nan. Muna fatan kun ji dadinsa, da haka Kande ta shirya muku wannan shiri kuma ke cewa sai makon gobe war haka idan Allah ta kai mu kuma ku huta lafiya.(Kande Gao)