Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-15 16:53:44    
An kara saurin gina tashar ruwa ta Shanhaiguan a birnin Qinhuangdao na kasar Sin

cri

Mr. Yu Shaotong yana ganin cewa, wurin da tashar ruwa ta Shanhaiguan take, tare da sharadin sufurin kayayyaki na kasa da na ruwa sun zama sharadi mai kyau ga kamfaninsa wanda ke sufurin manyan injuna da kayayyaki. Sabo da haka, a cikin shekaru 10 masu zuwa, kamfaninsa zai iya samun kyakkyawar damar neman cigaba.

Ya zuwa yanzu, dimbin masana'antu da kamfanonin da suke kera da yin sufurin injunan samar da wutar lantarki da na'urori da kayayyakin gyara na mota sun riga sun kafa sassansu a unguwar raya tattalin arziki da fasahohin zamani ta Qinhuangdao. Sabo da haka, wannan unguwa tana zama wani sansanin kera injuna a kai a kai.

A waje daya kuma, aikin gina tashar ruwa ta Shanhaiguan yana kuma sa kaimi ga cigaban kamfanonin sarrafa amfanin gona da man girki cikin saurin da ba safai ake ganinsa ba. Yawan kudaden sufurin amfanin gona da man girki da irin wadannan kamfanoni suke kashe ya yi yawa a gare su. Irin wadannan kamfanoni suna mai da hankali sosai kan yadda unguwar raya tattalin arziki da fasahohin zamani take samar da ayyukan sufurin kayayyaki a kasa da a ruwa. Ba ma kawai tashar ruwa ta Shanhaiguan tana bakin teku ba, hatta ma ita wuri ne da ke hade da hanyoyin dogo da dama. Idan kamfanoni sun kafa masana'antunsu a wannan wuri, za su iya tsimin kudade da lokaci na sufurin kayayyakinsu. Lokacin da ake gina tashar ruwa ta Shanhaiguan, gwamnatin wurin ta mai da hankali sosai wajen kyautata zirga-zirga domin kara yawan kayayyakin da za a iya sufurinsu ta hanyoyin dogo. Sabo da haka, kamfanoni za su iya samun sauki wajen sufurin kayayyakinsu a tashar.


1 2 3