Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-15 16:31:57    
'Yan kabilar Korea dake yankin Yanbian na kasar Sin suna gudanar da harkokinsu a duniya

cri
Daga shekarun gomiya ta 8 na karnin da ya wuce, da akwai 'yan kabilar Korea fiye da dubu 100 da ke yankin Yanbian na kasar Sin sun fita daga kasar don yin aikin kwadago a kasashen waje, Mr. Jin Xinlie dake zaune a kauyen Xinhua na garin Zhixin na birnin Longjing na yankin Yanbian yana daya daga cikinsu. Kwanan baya ya dawo daga kasar Libya, diyarsa madinkiya ce wadda take aiki a kasar Amurka, matarsa da dansa kuma suna aiki cikin wani hotel na kasar Korea ta kudu.

Yanzu a garin Zhixin na yankin Yanbian na kabilar Korea mai ikon tafiyar da harkokin kansa na kasar Sin, yawan gidajen manoma fiye da kashi 50 cikin 100 wadanda ke da iyalinsu da suke aikin kwadago a kasashen waje, sabo da yawan mutane sai kara karuwa suke suna ta kara samun kudin shiga ta hanyar aikin kwadago, shi ya sa wannan garin kabilar Korea wanda a da akan tafiyar da zama ta hanyar noman shinkafa da dasa itatuwa masu bada 'ya'yan tuffa da faya ya samu kyakkyawan yanayin bunkasuwa. Mr. Zhao Jinzhe, mutumin wannan kauye ya ce,

"An samu manyan sauye sauye a kauyenmu, da akwai gidaje da dama wadanda kowanensu yake da kudin ajiya na Yuan miliyan daya, wasu kuma suna da Yuan dubu 500, dukkan gidajensu sababbi ne kuma da kyaun gani."

Cikin wadannan shekarun da suka wuce, yawan mutanen yankin Yanbian na kabilar Korea da suka je aikin kwadago a sauran wurare sai kara karuwa suke, yawan kasashen waje da suka sa kafa ya kai fiye da 20 ciki har da Korea ta kudu da Amurka da Japan da Canada da Australia da New Zealand da Faransa, jimlar kudin da suka samu a shekarar 2006 daga aikin kwadago ya kai dalar Amurka biliyan daya da miliyan 60, wato ya nika sau 2 bisa na dukkan kudin shiga da aka samu a wannan shekara a yankin. Mr. Zhao, dan asalin wannan kauye ya gaya wa wakilanmu cewa,

"Wannan gidan da kuke gani yanzu sabon gida ne da aka gina bayan da mai gidan ya dawo a karo na farko daga kasashen waje. A karo na 2 na dawowarsa kuma ya yi fasalin gina wani sabo gida mai hawa 2. Shi ne mutum na farko daga cikin 'yan kabilar Korea na kauyenmu da yake shirin gina sabon gida mai hawa 2. Kafin wannan kuma ya gina wani dakin sayar da abinci, ga shi yanzu ya ware kudin Sin Yuan dubu 600 domin gina sabon gida."

Madam Wu Xilan ta bada misali ga wadannan mutane kuma ta ci zaben zama "mace mai gwada misalin koyo wajen kirkire-kirkire bayan da ta dawo daga wurin aikin kwadago" ta shekarar 2007 ta yankin Yanbian, kantin sayar da taliyar da aka yi da hannu mai sunan Xiaobanzhi da ta kafa yana da kananan rassa fiye da 10 wadanda suke barbaje a birnin Yanbian, hedkwatar yankin Yanbian na kabilar Korea mai ikon tafiyar da harkokin kansa, da birnin Changchun, hedkwatar lardin Jilin, da birnin Harbin, hedkwatar lardin Heilongjiang, da birnin Dalian, hedkwatar lardin Liaoning. Madam Wu Xilan ta koyi fasahar yin taliya da hannu ne daga kasar Korea ta kudu lokacin da take aikin kwadago a can. Da ta tabo magana kan tarihin aikin kwadago da ta yi a waccan shekara, ta fadi abin da take ji a zuciyarta cewa,

"Tun da sassafe uwargida mai kanti ta tashi daga barci ta fara dafa ruwa da shirya garin alkama domin yin taliya, sabo da haka ni ma na tashi kafin gari ya waye domin koyon fasahar yin taliya da hannu daga gare ta, kuma na kudufa kan aikin kwadago, shi ya sa uwargida ta amincewa da ni, ta koya mini da fasahar. Bayan da na dawo gida kuma na yi gwaje-gwaje har sau 50 ko 60 wajen yin taliyar da kaina".

Bayan da madam Wu Xilan ta dawo gida daga kasar Korea ta kudu, ta shafe shekaru 3 tana bincike har ta kago nau'o'in taliya masu dadi kusan 20 da ta yi da hannu, yawan kudin shiga da ta samu kuma ya kai kusan Yuan miliyan daya.